Sashe 52
Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Umm-Rumana kam haka kawai yau bayan tashinsu barcin safe ta tashi da ƙulafucin son cin alala, wakenta ta gyara ta bama Ahmad ya kai mata markaɗe nan makwaftansu, dayake fa'iza sun wuce gida tun ɗazun, yanzu akwai wajen koyan saƙa da suke zuwa sai lokacin islamiyya suke tasowa su biyoma Rumana, duk da yanzu wataranma ita da kanta take cewa bazata jeba batajin daɗi.
Sai da ta kammala ƙulla alalan ta ɗora a wuta sannan ta share ɗakin ta wuce wanka, shigarta babu jimawa Ahmad ya shigo gidan.
Kawai muryarsa ta jiyo yana amsawa maman Ama dake masa sannu da zuwa, cikin mamaki a zuciyarta take faɗin, “Da gaske yaya Ahmad ko dai kunne nane baiji da ƙyau ba?�.
Sake jiyo muryarsa tai yana ma yaran da suka shigo masa da kaya godiya.
Mamaki ya kuma kamata da wannan bazata tashi, kofa daren jiya sunyi waya, ita kuma sam bataji alamun tafiyar motaba.
Haka dai ta kammala wankanta ta fito tana tunane-tunane da mamakinsa. Da takalmansa ruwan makuba dake ajiye ƙofar ɗakin ta fara cin karo, maman Ama ta fito daga kicin tana faɗin, “Ohni amarya an iya sema ƙunshe dai? To barka ƴan tafiya an sauka lafiya�.
Murmushi kawai nai mata ina amsawa da ngd, dan nasan ko bayanin bansan da zuwansaba nima nai mata ba fahimtata zataiba, alwala na É—aura sannan na shiga É—akin da sallama.
Yah Ahmad dake kwance bisa gado yayi filo da hannayensa ƙafafunsa duka a ƙasa ya ɗan ɗago ido yana kallonta.
Canji ya sake gani a jikin ƙanwar tasa na musamman fiye da waccan dawowar da yayi.
Rumana dake ɗan sisinne kan kuwa tace, “Sannu da zuwa Yayanmu�.
Yunƙurawa yay ya tashi zaune sosai idonsa a kanta ko ƙyaftawa bayayi, saurin riƙe hijjab ɗin da take ƙoƙarin sakawa yayi saboda daga ita sai ɗaurin ƙirjine da ƙaramin gyale data yafo, bata yarda ta fita tsakar gidansu daga ita sai zani, dan tasan ko yaushe wani zai iya shigowa daga sauran mazan gidan.
Manyan idanunta da suka ƙara wani haske na musamman ta ɗago tana masa kallon mamaki.
Yanda shima ya kafeta da nashi sai ta kasa jurewa tai ƙasa da nata tana murmushi.
Tsaye ya miƙe kawai ya jawota jikinsa ya rungume, a tare suka sauke nannauyar ajiyar zuciya kowanne na sake mannema ɗan uwansa.
Ahmad da idanunsa ke a lumshe yace, “I miss you so much Babie R�.
Murmushi Umm-Rumana tayi har yanajin hucinsa a ƙirjinsa, ta ɗago kanta a hankali ta manna masa sumba a ƙirjinsa.
Ƙankameta ya sakeyi yana sauke numfashi da kyar, dan ba ƙaramin isa saƙon Rumana yayiba a dukkan sassan jikinsa da magudanar jininsa.
Itako dauriya kawai tai wajen aikata hakan, shiyyasa tana yi ta kuma cusa kanta a jikin nasa.
Da ƙyar ta yarda ya ɗago kanta da hannayensa duka biyu, idanunsa ya fara bazawa akan fuskarta yana binta da kallon ƙurulla tamkar yaune ya fara ganinta, itako sam taƙi yarda ta kallesa.
Iska ya hura mata a fuska yay ƙasa da muryarsa tamkar mai raɗa yace, “Lallai Babie R ɗina ta girma da gaske�.
Da sauri tace “Ni dai ban girmaba�.
Yanda tai maganar da shagwaɓa ne ya sakashi yin murmushi, ya matsar da bakinsa saitin kunnenta, a hankaki ya furta, “Tunda kika iya ɗaukar nauyin Amadin Ayyah ai kin gama girma�.
Saurin ƙanƙamesa tai saboda girman maganar tasa da sanin inda ta dosa.
Aiko Ahmad ya ƙyalƙyale da dariya shima yana rungumetan da ƙyau.
Itama dai murmushi taketa zubawa tana jin ƙaunarsa mai zafi na ƙara tasiri a ranta.......
Daga waje maman Ama ta katsesu da fadin, “Amarya abincinki fa na ƙauri�.
Da ƙyar suka iya rabuwa da jikin juna, ta ɗauki hijjab ɗin daya hanata sakawa ta saka ta fice domin duba abincin.
Babuma wani ƙaurin kirki da yakeyi, tsabar kutsugune irin na maman Ama, dan ruwan data tsumbula ledojin alalarne yake kumfa yana tasowa da ɗiga a rishoɗin, shinefa yake ɗan hayaƙi, hayakin kuma na ƙauri.
BuÉ—e murfin tai ta duba, ganinma alalar tayi sai kawai ta sauke ta É—ora man da zata soya, É—akin ta koma ta kaima Ahmad ruwan sha sannan ta dawo ta tsame alalar ta kashe risho É—in.
Ba tare da ta shiga ɗakinba ta ɗaga labulen ta ɗan leƙa kanta, “Yaya azuba ruwan wanka?�.
Ahmad ya ajiye ruwan da yasha yana É—aga mata kai alamar eh.
Sai da takai masa har bayi sannan ta dawo ta sake leƙawa danta sanar masa ta kai ruwan, hannunta kawai yaja ta faɗa ɗakin sosai.
“Wannan dojewar ai nasan inda ta dosa, oya maza cire min kaya, infa ba'a tarairayata kamar ƙwai a cokali kayana zan ƙulle na koma....�
“Da gaske?� Rumana ta faɗa cikin waro masa idanu waje.
Hancinta yaja kaɗan yana murmushi da faɗin, “Mizai hana ƴar ƙyaƙyƙyawa ta�.
Umm-Ruman tai murmushi tana ƙoƙarin cire masa maɓallin shirt din jikinsa, duk yanda yaso haka tai masa, da taimakonta ya cire komai, ta barsa da kayan ciki kawai ta koma ƙoƙarin ɗakko masa jallabiyya a drawer.
Ta juyo zata bashi ya wani tsareta jikin drawer ɗin yana bata fuska, “Kai gidan hayama bai yiba, a yanda na gajinnan wankanma buƙatar aimun nakeyi�.
Rumana ta É—ora hannunta kan baki tana murmushi.
“Oh dariya ma kikemin ko? Aiko zan manta da kowa kuwa muje dole kiyim ɗin�.
Sosai ta kwalalo idanu tana faɗin, “Yaya rufamin asiri, aiko to har gidanmu sai matan gidannan sun kai gulma�.
Ƙaramin tsaki yayi yana amsar rigar da cewa, “Sun daɗe basu kaiba masu kawunan talo-talo�.
Ita dai Umm-Ruman dariya tayi, shikuma ya fita domin yin wankan.
Dole taje ta sake yo alwala ta dawo ɗaki, aiko sake alwalar nan ba ƙaramin tsone idon maman Ama tayi ba, harda jan tsakinta tana faɗin, “Iya nan kukafi afana daga ke har lusarin mijin naki da baya amfana miki komai�.
Nace, “Oh su maman Ama problem😹🌚�.
Koda Umm-Ruman da batasan maman Ama nayiba ta koma É—aki sai tai azamar fiddo kaya ta saka kafin ya fito, ta shafa mai ta É—an murza fauda da kwalli harda janbaki kaÉ—an sannan ta saka turare ta tada salla.
Tana cikin sallar ne Ahmad ya fito, shima botikin ya ajiye ya É—auka butar data ajiye masa yay alwalar sannan ya shigo.
An riga an idar da salla a massallaci, dan haka yay ƙokarin gabatarwa a ɗakin, lokacin Rumana ta idar sai ta bashi abin sallar ita kuma ta miƙe domin shirya masa abinci.
Yana idar da sallar mai yaɗan shafa ya saka wando iyakar gwiwa da t-shirt mara nauyi mai guntun hannu, zama yay inda ta shirya abincin, da mamaki yake kallon Alalar da keta tashin ƙamshi, yanda yakeson alala yasan duk wanda yay tarraya dashi zaisan haka balle ita da suka tashi a gida ɗaya.
Kallonta yay, “Babie anya bakisan zan dawoba kuwa?�.
Murmushi Rumana tayi da faɗin, “Yaya baka sanarmin ba yaya zan sani? Amma miyasa kamin wannan tambayar?�.
Ba tare da yayi magana ba ya nuna mata alalar.
“Nayine kawai saboda na tashi da sha'awar cinta ALLAH�.
Idanu ya lumshe ya buɗe a kanta, yace, “Hakan ya sake tabbatar min zuciyoyinmu suna fahimtar yaren juna koda basa a ƙarƙashin inuwa ɗaya Ruman�.
Sosai kalamansa sukai mata daɗi, ta duƙar dakai tana murmushi, shiko ya fara cin abincinsa dake masa tsagwaron daɗi.
Sai da yay lauma kusan biyar sannan ya kai ta shidan bakinta, ta kallesa shi kuma ya É—aga mata gira alamar ta amsa.
Babu musu ta buɗe bakin ya saka mata, a haka suka cigaba dacin alalar yanaci yana bata har saida sukayi nak sannan, ita tama rigasa ƙoshi.
Taji daɗin yanda yaci sosai kuwa, ya fita ya kuskuro bakinsa yazo ya haye gado yana fadin, “Bara naɗan rage barci kafin la'asar�.
“A tashi lafiya yayanmu�.
Harya rufe idanunsa ya buÉ—e yana kallonta, â€Bazaki tayaniba?â€?.
Kanta ta girgiza alamar a'a.
Yaɗan ɗage gira sama kaɗan yana fadin, “Shikenan zan rama�.
Ita dai Rumana Murmushi kawai tayi batace dashi komaiba, ta tattare kayan da suka gama cin abincin ta fita tsakar gida danta wanke, shiko babu jimawa barcin ya kwashesa dan dama shine fal idonsa.
Daga ita saisu Ahmad a tsakar gidan, mamansu ta fice tun ɗazun, Kausar kuwa tana ɗaki saboda yanzu tayi nauyi, gashi bata da isashiyar lafiya tunda cikin yakai watanni bakwai, yanzu ma inba sune suka lekata ba baka taɓa ganinta tsakar gidan sai alwala ko wanka ko fitsari ya fiddota dole.
Tana ciki. wanke-wanken ne Maman Ama ta shigo, tasan dai daga gidan maman Aysha take gulma, batabi takanta ba taci gaba da aikinta.
Koda ta kammala sai ta koma ɗaki abunta ta zauna tana ƙarema Ahmad dake barci cikin nutsuwa kallo, sosai ya kara canjawa, daka gansa kaga nutsatstsen matashi mai sassanyar ƙwalisa, ya kumayin haske ga ƙibar da yayi jikinsa ya kuma murjewa sosai, hakan saiya ƙara masa kwarjini sosai, ga ƙasunbar daya ajiye tun wancan zuwan ta kuma fidda sirrin kyawunsa kai kace irin ɗan yankin utopia ɗin nanne.
Ajiyar zuciya Rumana ta sauke a hankali, ta ɗauka wayarta ta cire hasken camara ɗin ta lallaɓa ta gabansa tai masa hoto, sosai kuwa hoton yayi ƙyau tamkar ba barci yakeba.
Tana nan zaune har aka kira sallar la'asar, a kiran farko da aka ƙwala Ahmad ya buɗe idanunsa.
Barcin dai ba isarsa yayi ba, amma yaji nauyin jikinsa ya ragu Alhmdllh.
Kallon Rumana data fara gƴangƴaɗi yayi yana murmushi, daga gani bata san barcin ya figeta ba, bai tadata ba ya sauka a gadon ya fita yo alwala, sai da ya dawone ya taɓata ta tashi shikuma ya saka jallabiya ya fita masallaci.