← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 94

Sashe 2

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƴaƴan Baba Hamza mata daya aurar Dukansu iyakarsu sakandire aji uku yake musu auren, dan haka Ahmad ne ya fara wuce aji uku na sakandire a gidansu.
Ahmad ƙyaƙyƙyawan yaro mai cikar halittar asalin rumawan katsinawa, komai nasa mahaifinsane, yanada ƙwazo a makaranta ga rashin hayaniya, dan sam da wahala kaji ance ga abokin faɗansa, inhar kaga yayi faɗa to ankaisa maƙurane, dan yanada zafin zuciya idan aka kaishi ƙarshe, sannan idan yay fushi da abu Ayyah ce kawai ke iya lankwasashi cikin sauƙi.
Dan Ahmad ɗan gatan Ayyah ne sosai, duk abinda kaga Ahmad ya nema ya rasa sai dai idan Ayyah bata da ƙarfin siyensa, shima kuma saitayi ƙokarin saya masa makamancinsa, harya fara zama saurayi komai nashi yana ɗakinta, tsakaninsa da mahaifiyarsa kuwa gaisuwace kawai, dan kallonsa ma bata iyayi saboda kunyar ɗan fari.
Ya daɗe baisan ba Ayyah ce ta haifesa ba, da yasani kuman ma bai damuba, abinda kawai ke bashi mamaki kawaicin mahaifiyarsu, dan sam bata sakewa dashi, tun abun bai damunsa harya ɗan fara damunsa, amma daya ƙara hankali sai ya fuskanci ba sonshi bane batayi kawai al'adace irinta hausawa, tunda itama Ayyah ai bata kula yayarsu Maryam, komai sai gwaggo.

Tun Ahmad na sakandire aji É—aya suka haÉ—u da Samina, an tashi makaranta sun nufo gida shi da su maryam sai suka iske yara na damben faÉ—a a wani lungu.
Maryam tayi ƙoƙarin rabasu amma ta gaza, hakan yasa Ahmad ɗaukar ƴar bulala ya tsutstsula musu a ɗuwawu, dole suka rabu kowa na shafa wajen yana kuka.
Yarinya É—aya a cikinsu sai ta maido faÉ—an akan Ahmad daya dokesu, tsayawa yay kawai yana kallonta da mamaki, dan alokacin shekarun nata bazasu gaza bakwai ba, inma sun wuce sai dai Æ´an wattani.
Kuka take kashirɓan akan saita rama dukan da yay musu, ta kama ƙasan rigarsa ta riƙe tana kai masa duka da ɗan hannunta.
Shi dariyama ta bashi, dan haka ya tsaya yana kallonta yanayi, ganin da gaske take sai Rahama ta kamata ta janye tana dungure mata kai, nanko yarinya takuma daddagewa ta fasa musu kuka harda zagi.
Sunyi mamakin rashin kunyarta, suka wuce suka barta tana cigaba da zaginsu.
Washe gari sun taho makaranta suka gamu da yarinyar jiya da ko sunanta basu saniba, tana ƙyalla ido taga Ahmad saita samu dutse ta jefa masa, aiko sai akan goshinsa, kafin kace kwabo sai jini.
Dole aka kaisa ƙyamiz daga nan makaranta, yarinyar kuwa ta tsere gida basu sake ganintaba.
Bayan kwana huɗu Ahmad ya samu sauƙi ya koma zuwa makaranta, a randa ya koma yakuma yin gamo da yarinyar nan a hanya ana faɗa da ita.
Tsayawa kawai yay yana kallonta, ya kula batajin magana sam, tana ganinsa ta kwasa da gudu zata tsere, amma saiya cafkota, kuka ta saka masa da magiyar yayi haƙuri.
Shiko ya zare mata idanu yana faÉ—in, saiya rama zubar masa da jini da tayi.
Sosai take kuka tana tsalle da bashi haƙuri, shiko ya tsaya kawai yana kallonta.
Ganin bazata nutsuba yasashi fadin, “Kinga nutsu na fasa ramawar�.
Tsayawa tai tana share hawayenta, tace, “Da gaske ka haƙura?�.
Kansa ya É—aga mata alamar eh.
Hakan ne yasa ta nutsu, sai kuma takai hannu tana taɓa masa ciwonsa inda aka saka bandejin, dukta marairaice alamar jin tausayinsa.
Hannun nata ya janye yana murmushi, yace, “Kinga ai ya warke, yaya sunanki?�.
“Samina� ta faɗa har yanzu hankalinta nakan goshin nasa data fasa.
“Suna mai daɗi� ya faɗa yana miƙewa riƙe da hannunta, cikin makaranta suka karasa yana tambayarta ajinsu, sashen ƴan firamari ya kaita, saida ya kaita har cikin aji, ya ɗauki naira ɗaya ta ƙwandala ya bata a cikin kuɗin taransa naira uku da Ayyah ta bashi.

Tun daga wannan ranar sai yazam kullum Samina saita zo wajen Ahmad, tun su Rahama na mangareta har suka bari, dan shaƙuwace ta fara shiga tsakaninsu a hankali, harma takai ga Ahmad yasan gidansu Samina, dan anguwarsu ɗaya, sai dai ba layinsu ɗayaba, tsakanin makarantar su Ahmad da gidansu Samina babu nisa, shiko Ahmad gidansu da akwai ɗan nisa da makarantar.
Haka suka kasance a tare, idan Samina ta taho makaranta bata shiga sai ta jira Ahmad yazo, dayake makarantar firamare din kusa take da sakandire ɗin, shikuma shine zai kama hannunta ya rakata har ajinsu yakuma cire ƙwandala ya bata a kuɗinsa na tara.
Shaƙuwar dake tsakaninsuce tasa har Ahmad yasan gidansu Samina, wadda ashe bai saniba ƴar uwarsace ta jini.
Dan kuwa Samina ɗiyar Mama Gaje ce tsohuwar matar Yusha'u ƙanin Hamza daya saki da ciki.
Ashe bayan fitowarta ta haifi Samina sai tai aure a can garin Bauci, kuma da Samina ta tafi sannan tana jinjira, haihuwarta biyu acan zaman yaƙi daɗi ta kashe auren ta dawo kano da Samina, dan wancan mijin ya kwace ƴaƴansa.
Tunda kowa ya fahimci hakan a gidan sai ya fara jan Samina jikinsa, yayinda Ahmad yaytama Kawunsa Yusha'u naci akan ya dawo da mama gaje mahaifiyar Samina gidan dan ALLAH.
Da taimakon Ahmad daya kama kafa dasu Iya Ladi Mama Gaje ta sake dawowa gidansu, inda Samina da Ahmad suka kasance ƙarƙashin inuwa ɗaya.
A wannan karon Mama gaje da shirinta ta dawo gidansu Ahmad, dan kuwa sai da ta gama mallake zuciyar kowa musamman Malam Rabi'u da Iya Ladi.
Dawowarta kuma gidan ya sake É—aukar sabon salon zama, sai dai kowa na dannewa da kawaici saboda yanzu akwai Æ´aÆ´a a tsakani.
Da taimakon Ahmad dukan yaran gidansu suka samu shiga makaranta a yanzu, musamman ganin ita Samina tanayi tunda ba'a gidan ta tashiba.

A haka har Samina itama ta shigo sakandire ɗin dayake maza da matane a haɗe, hakan ya saka shaƙuwarsu ta sake ƙarfi mai ban mamaki, tana aji ɗaya yana aji biyar, amma ko yaushe suna tare, hakan yasaka abokansa suka fara kiransa da suna Sharukhan baban soyayya😂............✍�

_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_

_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_

Mucigaba da shakatawa da wannan kafin a fara kafta WASAN😁👉🏻📻

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏ðŸ
*_Typing📲_*

*_🏃🏻‍♂️GUDU DA WAIWAYE.....!!_*
_(Shi ya kawo mugun zato)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*(2)*

.............Yakanyi dariya kawai, dan a sannan ba soyayyar bace a tsakaninsu, duk da dai ta musu kamu basu saniba.
Tun ana yaya da kawa har abin ya fara rikiɗa yana zama soyayya, soyayyarma mai ƙarfi da shaƙuwa, kowa ya san da hakan a cikin iyayensu kuma duk da iyayen Ahmad mata basuso hakaba saboda mugun halin Mama Gaje.
To Amma ya zasuyi da hukuncin UBANGIJI? Dole suka É—auke idanunsu suka koma musu addu'a da fatan ALLAH yasa kar Samina tayo gadon halin Uwarta.
Bayan Ahmad ya kammala sakandire saiya fara bin mahaifinsa kasuwa wajen sana'arsa ta saida yadikan maza da huluna, amma sai baban yace da hakan ai gara ya koya koda sana'ar É—inkice ko wani abun.
Ahmad ya aminta da hakan É—ari bisa É—ari, dan haka yashiga wani shagon koyan É—inki anan bayan layinsu kusa da makarantar su samina.
kusancin da suka samune ya kara sake ƙullesu sosai, dan kullum daga gida Ahmad da Samina tare suke tahowa, saiya rakata makaranta zai dawo shago wajen aikinsa.
Sannan da an tasosu daga makaranta komi yake a shago sai ya ajiye ya rakata har gida, wataranma sake biyoshi shagon ta keyi, data shiga gida babu daÉ—ewa zata fito wajensa su koma tare..
Ƴan shagon kan musu dariya, musamman da suke ganin sunyi ƙanana, badai za'ace za'ai musu aure a wannan shekarunba.
Lokacin da Baba ya fahimci wannan shashancin nasu sai yaytai ma Ahmad É—in faÉ—a, yakuma ce karya sake ganin Samina ta bishi shago bayan ta dawo makaranta.
Yaji faɗan baba ya dakatar da Samina, amma dukda hakan wataran saita ɗan zagaya a ɓoye taje, musamman ranar weekend da babu karatu.
Shekararsa ɗaya a shagon aka yayesa, zuwa lokacin kuma ya kware a aikinsa sosai dan ya nuna ƙwazo matuƙa.
Ayyah ta fasa ɗan asusunta da takeyi da ribar kayan sana'arta ta siya masa keken ɗinki, yayi murna sosai, hakama yan uwansa sunyi farin ciki, wani ɗakin dake cikin gidan aka fasama kofa ta baya aka saka masa keken ɗinkin, sai yazama shike ɗinkama baba yadika ana kaiwa kasuwa a siyar ɗinkakku, sai kuma masu kawowa da yakemawa, harma na mata yana dan jagulawa dukda bai wani ƙwareba saboda dinkin maza ya koya.
A hankali hannunsa ya fara faɗawa akan dinkin matan ma, kafin kace mi komai ya zama Alhmdllh, harma yana taimakawa gidansu da abinda ALLAH ya hore masa, gefe kuma yanama Samina hidima sosai dasu ta karatu da buƙatun yau da kullum.
Ganin yasamu madogara kuma yana samu Alhmdllh sai yay aniyar komawa karatu.
Kowa ya bashi goyon baya, dan haka ya shiga kokarin neman gurbi a jami'ar b.u.k.
Ya samu shiga jami'ar B.U.K, dayake takardunsa sunyi ƙyau sosai, kuma a lokacin tsadar rayuwa batakai hakaba sosai.
Komawarsa makaranta yasakashi sake zama busy, ko ɗinkima sai yayi da gaske yake samu yaɗanyi, ga kuma aikin yana samu, ganin zai iya korar customers ta wannan hanyar sai ya fara koyama ƙaninsa Mudanseer shima, aiko Alhmdllh Mudanseer ma sai ya maida hankalinsa sosai, sai ya zam yana taimakawa Ahmad ɗin da wasu ayyukan.
Chapter 2 · 0% Book details