← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 94

Sashe 13

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Falalu ƙanin Samina da suke uba ɗaya, wato ɗan ɗakin su Umm-Rumana ne ya shiga gidansu da zancen ɗaurin auren.
Babu shiri Samina dake ban ɗaki tana wanka tajawo zani ba tare data ɗauraye kumfar jikinta ba ta fito kamar wata taɓaɓɓiya tana faɗin, “Kai Falalu ubanmi naji kake cewa?�.
Yaron yaɗansha jinin jikinsa, hakanne ya sakashi haɗiye murnar da yakeyi yana komawa bayan Amminsu ya ɓuya, Samina ta daka masa tsawa tana sake tambayarsa abinda ya faɗa.
A dai-dai lokaccinne Mama gaje tayo waje itama daga ɗaki, dan da salla takeyi, saboda sauri har tuntuɓe tayi, kaɗan ya ragema ta faɗi ta dai samu ta riƙe ƙarfen barandarsu.
Falalu dake a laɓe bayan Ammi da tai tsayuwar sojan badakkare yace, “Ai dai malam ne ya ɗaura miki aure da Yah Ahmad yanzu a massalac.......�
Wani ihu Samina ta kurma tana buga tsalle ta dire ƙasa, sai gata wanwar a sume zani a gefe.
Jikin Umm-Rumana na rawa taja Zanin gadon Ammi dake a kan igiyar shanya ta yafama Samina saboda tsirara take.
A lokacinne kuma iyayensu maza duk suka shigo, harma dasu Ayyah da matan Baba Iliyasu, dan casuke wani abunne ya faru da Saminar.
Ahmad ma da Mudanseer sai gasu sun shigo, nanfa kowa ya rufu akan Samina, yayinda Mama Gaje keta kuka akan bazata yardaba idan Æ´arta ta mutu, tunda tace batason auren miyyasa zasuyi?.
Kalaman mama gaje sun fahimtar da kowa daga ina matsalar take, hakan yasa Gwaggo zare jikinta tabar sashen ganin an zubama Samina ruwa ta kawo numfashi.
Samina dake hawaye ta fara sakin sambatu, “Wlhy kozaku haɗa wuta ku sakani bazan zauna da Ahmad ba, nace bana sonshi, na rantse da ALLAH sai ya sakeni, inba hakaba kasheshi zanyi, wlhy saina yankashi da wuƙa idan kuka matsa saina zauna dashi, randa aka kaini a ranar zan kashesa, garama na ƙare rayuwata a prison da na zauna zaman aure dashi�.
Da sauri Baba Yusha'u ya buge bakin Samina, ya kuma kai hannu zai doketa Baba Hamza ya riƙe hannun yana girgiza masa kai.
Daga ƙarshema sai yaja hannunsa suka fice, baba Iliyasu na biye dasu.
Mudanseer da zuciya tazo masa kusa ya nuna Samina yana zagi, “Banza kawai mara tunani, to dan uwarki saiki tashi ki kashesa ga shinan, butulu kawai mai manta alkairi, kwaɗayayya mara tarbiyya, idan kika kuma zagin Yah Ahmad a wajennan wlhy kafin ki kasheshin ni saina kasheki dan uwark.......�
Jan Hannun Mudanseer Ayyah tayi tana share hawaye, “Kaga ya isa haka Mudanseer, idan ita bata da hankali kaima baka da shine? Kunga ku wuce muje� tai maganar tana jan Hannun Ahmad dake tsaye kawai yana kallon kowa kamar ya samu TV.

Koda suka koma sashensu ma zama kawai yay ya dukar da kansa ƙasa yana kallon sumintin ƙofar ɗakin iyayen nasa, yayinda Mudanseer da Abu keta zage-zage Fa'iza da Zainab na tayasu, Sadiya ko tanada sanyin hali tamkar su Ahmad, sai tayi shiru kawai tana share hawaye.
Gwaggo kuwa ai saikama rantse batasan mi ake yi a gidanba, sai aikinta take kamar komai bai dameta ba, nanko jin zuciyarta kawai take tana tsitstsinkewa kamar zata faɗo ƙasa dan damuwa.

Cikin lokaci ƙanƙani gidan ya harziƙe, dan bakin Samina bai mutuba sai da baba Iliyasu ya lakaɗa mata dukan kawo wuƙa, tai tiɓis ɗin da ko yatsa bata iya ɗagawa.
Mama gaje kuwa ta fasa kuka da kururuwar za'a kashe mata Æ´a.
Kafin kace kwabo labari ya fara fitowa a anguwa, dan duk maƙwafta najin abinda ke faruwa.

________________________________

Yanda Samina ke ambaton ƙiyyar Ahmad a bakinta abun na bama kowa mamaki, duk da dai an fahimci harda ruɗin ƙyale-ƙyalen duniya ke kwasarta, amma tabbas akwai zuga dake aiki akanta, bakuma kowa bane ke zugata sai mahaifiyarta Mama gaje, saiko Inna mari kakarta da itama tai ɗare-ɗare a zancen, gefe kuma gasu Nafy sunayi ta waya da zahiri idan sunzo gidan da ƙaryar dubata.
Dan dukan da baba Iliyasu yay mata ciwo sosai ya sakata, ko magana mai ƙarfi ta kasa yi.
Kuma Ahmad ɗin dai da bakinta bai gajiya da munanawane ya samo likita ya dubata, ƴan kuɗin dake aljihunsa na ɗinki da aka biyasa ya cire ya biya kudin magani dama duk abinda aka buƙata.
Tun anama Samina mazurai har iyayenta maza da Amma suka koma lallashinta dukdan ta kwantar da hankalinta ta fahimci halin da ake ciki.
Sai dai sam taƙi fahimta ɗin.

★★★★�

Tsahon kwana huɗu abu yaƙi ci yaƙi cinyewa, saima neman ɗakin da zasu zauna haya akeyi.
Ahmad kuwa yaƙi cewa kowa komai, sai bushewa yake a tsaye saboda damuwa, harya fara duhun baƙi, gashi abun na neman taɓa masa aikinsa na ɗinki, dan yanzu ya daina yin komai sai tunani.
Wanka wannan sai Ayyah ta sakashi a gaba yakeyi, hakama abinci sam bayason ci sai an masa faÉ—a.
Yana ƙaunar Samina sosai, duk wannan haukar cin mutuncinsa da takeyi bama yajin haushinta, a ganinsa canja masa ita akai kawai, dan Saminar sa ba haka takeba da can.
Gashi duk yanda yaso su haɗu taƙi bada ƙofar hakan, duk sanda ya aika a kirata zagi ma take maido masa, idonta ya rufe gaba ɗaya, burinta kawai Ahmad yay zuciya ya saketa.

Yau data kasance duk yaran gidan na ma'auri sunzo gidan akan wannan maganar aure data bama kowa mamaki, masoya sun zama maƙiya, wanene a anguwar baisan soyayyar Samina da Ahmad ba, sai dai baƙon da bai wuce sati ɗaya ba.
Binta yayar Samina ta kalli Saminar dake kwance a saman gadon Mama Gaje tana sharɓar hawaye, ga zazzaɓi daya rufeta saboda ƙuntata kanta da takeyi a kwanakinnan.
“Humm anya Samina kina ganin kuwa kinma kanki adalci a wannan gaɓar? Anya kuwa kece Samina ƙanwata dana sani mai tsantsar ƙaunar Yah Ahmad. Mike ruɗaki hakane kike son tafka babban kuskuren da anan gaba baki da hanyar gyarashi? Miya shiga kankine? Samina kibar biyema mama wlhy, dan daga ita har Inna mari babu mai faɗa miki gaskiya akan batunnan, kwaɗayi ya rufe muku ido ku duka, kun manta UBANGIJI dake bayarwa bai manta da shi yah Ahmad ɗinba, sannan kuma aiba ALLAH ne ya sanar muku shima bazai taɓa yin arziƙinba ko? Duk gwamna da kika gani ko ɗan majalissa, ko minista, ko kwamishina, ko shugaban ƙasa, ko babban ɗan kasuwa, ko babban ma'aikacin gwamnati to shima a baya talakane, kije ki bibiyi tarihinsa kiji, talakannan da zaki aura wataran shine zaki buɗa ido ki ganshi a wancan matsayin da ayanzu ya maida ganinki duhu Samina, wlhy dana auri mai arziƙi gara na auri talaka musha wahala tare wajen tara arziƙin, koba komai zai mutuntani ya girmamani, sannan ko mata dubu yayi a bayana sai yafi nuna kulawarsa gareni fiye dasu, a wannan zamanin kuma Samina yanda maza suka lalace da wulaƙanta mace a gidan aure, wlhy kasamu mai maka soyayya irinta Yah Ahmad ka gama morewa, kwanciyar hankali a gidan aure ita mace ya kamata tayi fata a wannan zamanin ba dukiya ba, dan daga lokacin da mai dukiyar ya kaiki cikin gidansa to fa ina gaya miki komai zai canja, dan kinbar ganin farin cikinsa da lokacinsa kuma, ki zauna kiyi tunani, karki bari damarki ta wuceki, dan daga lokacin da kika kai haƙurin Yah Ahmad bango yaji ya dace ya sakeki tun a sannan zaki fara nadama har ƙarshen numfashinki wlhy.......�
“Aniyarki ta koma miki, kujimin Yaya Bintar nan da mugun baki, ai dawwama a auren Ahmad ne zaisa nayi nadama har ƙarshen numfashina, rashin auren Ma'aruff kuwa shine sakaci da damata, idanma tunani kike maganganunki zasuyi tasiri a kaina to basu shigaba, dan jinsu nake busar sarewa ma ta fisu daraja, idan kuma shine ya aikoki kije ki sanar masa ba'a daceba, nace bana sonsa a yanzu, ko dolene saina zauna dashi, ana so dolene? So kuke nima na ƙare cikin talauci da fatara a gidan miji kamar ku, a cikinku kaf babu wata mai abin nunawa a gidan miji inba talauci ba, jibeki, shekarunki gaba ɗaya basu wuce talatinba, amma saikace tsohuwar data ƙulla hamsin, a dalilinmi zan zauna na ƙare a talauci kamar ku, aini bama ƙaramin sona ubangiji yakeyi ba da ya kaini matsayin ƙara karatunnan, da haka nima za'a cutamin, a bankani ɗakinsa na ƙare rayuwata a wahale, wataranma har surfau ɗin masara da wankau sai an sameni inayi saboda fatara da rashin abincin arziƙi mai ɗan maiƙo-maiƙo�.
Binta da tai shatata da baki tana kallon ikon ALLAH daga Samina, taɓe baki, lallai ƴar uwar tata tayi nisan da sam bazataji kiraba.
“To ALLAH ya ƙyauta miki Samina, ai duk wanda yace zai iya haɗiye gatari sai a sakar masa ƙota, ALLAH yasa kar Yah Ahmad ɗin ya sakeki muga tsiya�.
Baƙin ciki sosai maganar Binta ta ƙarshe taima Samina, a masife tace, “Bakinki ya sari ɗanyen kashi, muguwa kawai azzaluma�.
Dariya Binta ta fita tanayi, inda tun fitowarta mama Gaje ke zuba mata harara tamkar idonta zai faÉ—o, É—anwake take jefawa a tukunya, shiyyasa koda take jiyosu bata shiga É—akinba.

A ɓangaren su Ahmad ma ƴan uwansa ne zagaye dashi, shawara suketa bashi akan yayi haƙuri yabar Samina tunda tace bata yinsa yanzu, da adawo ana dana sani nan gaba barin auren tun yanzu kamar shine yafi alkairi.
Murmushi mai cike da damuwa Ahmad yayi, murya a sarƙe yace, “Yaya Maryam ina sonta, nasan duk abinda take faɗa shirmene kawai, nan gaba kaɗan zata bari muyi zaman lafiya, ana kaitane zakuga wannan shirmen dukta bari, yanzunma zugata akeyi shiyyasa�.
Gaba É—ayansu zuba masa ido kawai sukayi da mamaki, sunsan É—an uwan nasu akan Samina babu abinda zasu faÉ—a masa ya fahimcesu, sai kawai duk sukaja bakinsu sukai shiru.

Haka Samina taci gaba dayin bore tsawon lokacin satin nan uku da suka shuɗe, a kuma na huɗun da aka shigane tarewar nasu, dan an samu ɗakin da zasu zauna anan ƙasan layin nasu kaɗan, harma an masa fenti, yayinda iyayensu maza suka haɗa kuɗinsu kamar yanda sukeyi aduk ƴaƴansu da zasu aurar aka siyama samina kayan gadon gwargwadon ƙarfinsu.
Kasancewar bikin yazo babu shiri sai baba Rabi'u yace ƴan shema ba sai kowa yazoba, su zaɓi wasu a ciki su ɗanzo a raka Saminar ɗakinta shikenan, dan ta jama kanta baza'ai wani taron bikiba...........✍�

*_Bilyn Abdull ce_*
Chapter 13 · 0% Book details