Sashe 22
Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
.............Shuru ɗakin yayi bayan tafiyar su Ayyah, babu wani sabo a tsakaninsu na shaƙuwa tun can baya, sai dai girmamawa irin ta yaya da ƙanwa da kowa ya sani, yayanma irin wanda ake shakka sosai ɗinnan.
Umm-Ruman tana zaune da ga kan tabarma inda ta idar da salla ta zabga tagumi, gaba É—aya kewar gidace ke addabarta, musamman ma yau da duk Æ´an uwanta suka kasance a gidan tare dasu.
Ahmad kam yana daga can ɗayan gefen kwance saman sallayar da shima ya idar da salla, dan rashin ƙwarin jiki ya hanashi tashi yaje massalaci.
Yanayinsa zaka kalla kawai shima kasan tunanin yakeyi, dan ya ƙurama silin ɗin ɗakin idone ko ƙyaftawa bayayi, gashi sai taunar lip ɗinsa na ƙasa yakeyi da haƙori.
Kiran sallar isha'i da aka ƙwalane a masallacin kusa da su ya saka Ruman miƙewa ta fita, Ahmad kam ko motsi bai yiba.
Koda ta dawo tayi kamar zata masa magana amma sai ta fasa ta kabbara sallarta, harta idar bai dawo hayyacinsa ba, ta sauke numfashi a hankali, cike da tausayinsa ta matsa gabansa,
“Yah Ahmad!�
Shiru nanma bai motsaba, ta sake kiran sunansa kusan sau uku shiru, dole ta miƙa hannunta zata ɗan bugi filon daya jingina jikin Wadrobe ya saka kusan rabin bayansa da kansa, amm sai a mistake hannunta ya gogi kafaɗarsa.
Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, yayinda Rumana kuma taja hannunta da sauri tana cusashi cikin hijjabi, jikinta sai tsuma yakeyi, sai kace wadda ta taɓa wani mugun abu.
Kallonta yayi da idanunsa da suka canja kala, ga ramar da yayi ta fito sosai saman fuskarsa, “Lafiya dai?�
Ya faÉ—a a hankali kamar mai raÉ—a.
Rumana dake ƙoƙarin matsawa baya cikin in ina tace, “Dama salla har an idar wasu masallacin�.
Yunƙurawa yay ya tashi zaune sosai, bai ce mata komaiba ya fita ya sake ɗauro alwala.
Koda ya idar ɗinma zaman shurun suka koma, a haka mijin maman Ama.. Yay sallama a ƙofar ɗakin, tashi Ahmad yay yafito suka gaisa yana sake tambayarsa yaya jikinsa?.
Cikin mutuntawa ya amsa masa akan da sauƙi, kowa ya koma wajen iyalinsa...
Yau ɗinma dai cayay ta hau gado ta kwanta, shi kuma ya kwana a ƙasa saman tabarma.
________________________
Haka zaman nasu ya cigaba babu tsangwama babu sakin jiki wa juna, har dai jikin Ahmad ya ƙara sauƙi, yanzu kam alhmdllh ya wartsake, sai dai ciwo irin na zuciya da ya ƙi barinsa, wannan kam kowa yasan abune mai wahala ace ya barshi da wuri, musamman idan aka ƙiyarsata da irin son da yakema Samina.
Tunda yaji ƙarfin jikinsa ma ba zaman gidan yakeba, barcine kawai ke kawosa, zuwa goma sunyi karin kumallo ya fice shago, bata sake ganinsa sai uku na rana, yay wanka yaci abinci ya sake ficewa, daga nan kuma sai sha ɗaya na dare ko goma da rabi zai shigo.
Wajen barci kuwa tana saman gado shiko yana ƙasa a tabarma, babu wani abu na muzgumawa da yake mata, sannan babu najin daɗi, itako tsakaninta da shi sai girmamawa kamar yanda ta saba tun can da suna gida.
Duk da ta lura hankalinsa baya gareta hakan bai damunta, ba itaba ai dama kowa dai yasan Samina yake so, to miyasa zata ɗaɗara kanta da ƙasa akan sai ya sota.
Kuma dama bawani saurayine da ita ba data ƙwallafa ma rai balle yanzu sonshi ya damu zuciyarta.
Yana fita zata dawo tsakar gida suyita hirarsu ita da Maman Ama, kokuma ta É—akko Ama taita mata wasa ita da Ahmad da take kira yayanta..
Yauma tunda ya fita gidan nasu ya zarce, sai da ya shiga suka gaisa da malam da iya sannan ya shiga sashensu, Ayyah kaÉ—ai ya iske a gidan Gwaggo ta fita, ya gaidata cike da girmamawa yana zama a gefenta.
Gwaggo ta kallesa da kulawa, “Ɗan albarka yaya dai? Naganka wani iri�.
Murmushin yaƙe yayi kaɗan yana duƙar da kansa, kamar bazai ce komaiba daboda nauyin maganar a harshensa sai kuma yaja numfashi, a ɗarare yace, “Ayyah! Sonake nabar garinnan, inaga hakan zai bani ƙyaƙyƙyawan nutsuwa, har yanzu nakanji zuciyata sam babu daɗi a cikinta, komai baya burgeni, komai baya sakani nishaɗi, koma bai sakani farin ciki wlhy Ayyah�.
A yanda ya ƙarasa maganar sai tausayinsa ya kama Ayyah, ta dafa kafaɗarsa tana faɗin, “Ɗan albarka na sani, nasan kana cikin damuwa har yanzun, musamman ma da rayuwar gidannan take neman juyewa zuwa wani abu daban, banƙi kabar garinnan ba, sai dai ka tuna yanzu bakai kaɗai bane, gashi yarinyarnan gaba ɗaya bata wuce sati biyu ba, anya tafiya ka barta a wannan yanayin bazaisa mutane su fassara abun da butulci ba?�.
“Hakane Ayyah, nima nayi wannan tunani, amma a ganina tafiyar shine mafita, ita kanta yarinyar maybe a yanda nake kallonta zai canja�.
Shiru Ayyah tayi tana nazarin maganarsa, bawai bata yarda dashi bane, ta gamsu da duk bayaninsa É—ari bisa É—ari, amma Umm-Rumana take tausayi, bai kamata a haÉ—a mata zafi uku ba a ganinta.
Ta sauke nannauyan numfashi tana mai kallon Ahmad ɗin kamar baƙonta, “ALLAH ya zaɓa mana abinda yafi alkairi to, mu miƙa lamarin hannun UBANGIJI, idan tafiyar tafi alkairi ALLAH ya tabbatar, idan ba ita bace ALLAH ya canja maka da mafi alkairi�.
“To amin ya rabbi Ayyah, sai ki tuntuɓi baba da zancen shima muji mizaice�.
“Babu damuwa, insha ALLAHU zan masa maganar, itama Gwaggo zan sanar mata ta tayamu da addu'a�.
Kansa kawai ya iya jinjina mata, daga nan suka ɗora da wata hirar, duk dama Gwaggo ce ƙarfin maganar, Ahmad kam sai ihhm da a'a.
Shigowar su Fa'iza daga makarantar allo ya sakashi miƙewa ya fice, shago ya shiga domin ya samu ya rage ɗinki, dan babu laifi sun ɗan tara da yawa.
Yana tsaka da yanka wata atanfa fallatsetsiyar mota tazo gaban shagon ta faka, kallo É—aya yay ma motar ya É—auke kai saboda hango Ma'aruff da yay a ciki.
Sai dai kuma ya kasa daurewa, dan yasan dai dole Samina yake jira, ilai kuwa sai gata ta fito cikin kwalliyar duguwar rigar Material datai mata masifar ƙyau, rabonsa da ganinta tun washe garin aurensu, ta ƙara fari da alama man bilicin ɗin ta cigaba da shafa a binta, bai iya daina kallonta ba har ta shige motar Ma'aruff yaja suka bar anguwar, yanda ya bulo ƙasa zaka tabbatar da biyu yayi hakan saboda Ahmad.
Ahmad yaja dogon tsaki yana É—auke kansa, hakan yasa Mudan dake É—inki É—agowa ya kallesa, danshi tunda yayma motar kallo É—aya bai sakeba saboda takaici.
Kamar Mudan zaiyi magana sai kuma yay shiru ya cigaba da É—inkinsa, shima Ahmad É—in dai yankansa ya cigaba da yi dukda zuciyarsa babu daÉ—i sam.
★★★★★★
Ma'aruff kam yana barin wajen dariya suka kwashe da ita shi da Samina, cikin dariyar yake faɗin, “Mutuminki fa ya shaƙa, kinga harar da yake wulloma motarnan, na tabbata ji yake kamar zuciyarsa zata faɗo dan baƙin ciki�.
“Manta da shi luv ɗina, ni ko kalloma bai isheniba wlhy, yanzu ina zamuje?�.
Gefen titi ya samu ya gangara yay fakin, hakan ya saka Samina kallonsa da faɗin “yaya haka kuma? Miyasa muka tsaya anan?�.
Juyowa yay sosai yana kallonta da wani murmushi a kan fuskarsa, ya ɗan matsota idanu a narke, cikin raɗar magana yace, “Babyna bazaki ganeba, ina cikin wani haline�.
A ɗan ruɗe Samina ke faɗin, “Miya sameka?� tana maganarne tana dube-duben jikinsa�.
Hannu ya ɗora a kafaɗarta yana kuma narke murya, “Bafa ciwo najiba, damuwar a nan ne� ya kamo hannunta ya ɗora saitin zuciyarsa.
Ƙoƙarin janye hannun tayi amma sai ya riƙe sosai yanda bazata ƙwaceba, ya fara murzashi kaɗan-kaɗan cikin nasa hannun mai taushi, “Haba babyna ki gane mana, wai sai yaushene zaki ban dama koɗan rage zafi munayi, kinfa san kece zan aura, aurenma nan da kwana kaɗan, kinaso ace yau ga mijinki a gidan karuwai ko yana huɗɗa da karuwa?�.
Da sauri ta girgiza masa kai, ya lumshe ido yana hura mata iska kaɗan-kaɗan akan fuska, ganin ta lumshe nata ya sake kai fuskarsa dab da tata har suna shaƙar numfashin juna.
“Baby karki hanani kanki, namiki alƙawarin babu abinda zai shiga tsakaninmu inba ɗan kiss hakaba, shima dan na samu nutsuwa ne kawai kar wata ta lalata miki ni, dan harga ALLAH a matse nake, shiyyasa banson aurenmu ya gaza wata ɗaya, amma gashi kekuma kince muyi haƙuri ki ƙarasa karatunki nanda watanni shida, niko yamun nisa Samin ɗina�.
A hankali ta buɗe idanunta da suka shige cikin nasa, tsigar jikinta sai tashi take saboda dama itama a bukacen take, duk yanda taso ta hanashi hakan sai ya gagareta, saboda wani tsantsar sonta take hange cikin ƙwayoyin idanunsa, itama idan son samun tane suyi aurensu nanda wata ɗayan kamar yanda ya buƙata, amma sai mama gaje tace tajashi harta gama makaranta dansu ƙara tatsar kuɗaɗen da zasuyi mata hidimar biki na garari da sai ya tsayama ƴan gidansu a rai da Ahmad, wannan shawarar ce ta saka Samina cemasa ya bari ta gama makaranta kawa......
Saukar laɓɓansa kan natane ya sakata ƙanƙame jikinta, dan wannan shine karo na farko a rayuwarta.
Duk hanyar da Ma'aruff ya ƙware akai sai da yabi Samina ta sakar masa jiki yay kissing ɗinta sosai, sai da ya gaji dan kansa sannan ya barta.
Koda suka dai-daita kunya hanata kallonsa tayi, yaje da ita wani wajen motsa baki, duk yanda yaso taƙi fita su shiga tare, dan gani take kowa zai gane abinda sukayi, Ice-cream da gasashshiyar kaza da kayan ciye-ciye ya lodo mata ya dawo, daga nan gida ya maidota, inda ya hanata fita suka cigaba da hirarsu a mota.
Koda Ahmad ya fito da ga shago zaije masallaci sallar magriba kallo ɗaya yayma motar yay gaba abinsa, zuciyarsa na wani irin ƙuna tamkar zata fito waje.
Har suka dawo sallah Ma'aruff da Samina na'a motar, hakanne ya saka Ahmad shiga cikin gida ya amsar musu tuwo shi da Rumana ya fito domin tafiya gidan.
Har abokansa na tsokanarsa akan yau da wuri haka zai wuce?.
Murmushin yaƙe kawai ya iya musu ya wuce abinsa yana tsaida mai napep.
_________________________