← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 94

Sashe 82

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali al'amura suka cigaba da lafawa, dukda dai zukata sun gaza mantawa dasu sam, baba yusha'u yanata samun sauƙi, hakama mama gaje ta samu sauƙi, sai dai ta rame matuƙa, damuwa ta maidata tamkar wata zararriya, haka zaka sameta zaune jigum tayi tagumi saboda tunani.
Ranar da akai addu'ar arba'in ɗin malam akai zaman mitin a gidan, wanda Baba Yusha'u ya roƙa akan ayisa.
Yana hawaye yake neman gafarar Æ´an uwansa akan dukkan abinda ya faru ta sanadin iyalinsa, hakama mahaifiyarsu iya ya nema gafararta itama, kowa yace ya yafe masa, tunda ai ba shine ya aikataba, suma da suka aikata É—in ALLAH ya shiryesu ya ganar dasu gaskiya harma da Æ´an baya masu kalar tunaninsu.
Bayan gama tattaunawa da neman gafarar juna baba Yusha'u ya maida kallonsa ga mama gaje da tai jigum tun zamansu mitin É—in, uffan bata iya furtawaba sai kallonsu kawai take kamar doluwa.
Yace, “Gaje bazan iya cigaba da zama dakeba duk yanda naso jurewa, wlhy ganinki kaɗai sakani takaici yake da tashin hankali, kece sanadin komai, kece kika rusa mana zuri'a, tun daga aurenki har zuwa yanzu ban tsinci wani abun alkairi bayan na haihuwaba tattare dake, to acikin haihuwarma saida kika haddasa komai na baƙinciki wa rayuwata da ahalina, alhakin yaronnan Ahmad kawai ya isa hana rayuwarki samun salama, Samina ta tsinci kanta a halin da yafi wannan ma, yaron nan yashiga ƙuncin rayuwa a dalilin butulci, hakama iyayensa, amma suka danne zukatansu basu raba zuminci damuba, sanadin Ahmad kika dawo gidannan Gaje, a wannan gaɓar kuma dolene ki barshi, bari na har abada, dan haka kije gida na sakeki, na katse sauran igiyar data rage a tsakaninmu dama ƙwara ɗayace.........�
Cikin hanzari baba Hamza ya katse baba Yusha'u da faɗin, “Haba Yusha'u, wannan wane irin maganace? Miyasa zaka saketa? Koma dai miye ya rigada ya faru, ya kamata kuma mu ɗaukesa matsayin jarabawar da babu hannun da ya isa gogeta a duniya, sam banji daɗin wannan hukuncin nakaba, bankuma yi zato ko tsammanin zaka yankesa ba........�
Baba Iliyasu yace, “Yaya wannan hukunci yayi dai-dai wlhy, lokaci yayi da zamu dawo cikin hankalinmu, kaine babban yayanmu, wanda muke kallo tamkar uba, tayaya zamu cigaba da kallo a koda yaushe ana cuta maka kaida zuri'arka?, tun daga zamanin ƙuruciya har wannan ranar da muke yau iyalanka haƙuri kawai suke a gidannan, babu kalar haɗin masifa da ba'ai musuba, shikenan kuma dan ALLAH yasa kun kasance masu kawaici sai a maidaku juji? Wlhy bama gaje ba, kowacce ƴar iskar mata yanzu a gidanan inhar bata dai-daita sahuntaba mu zamu daidaita matashi, dan munsan gaje tanada mabiya masu koyi da munanan halayenta a gidannan.......�
Nanma dai babane ya sake katse baba iliyasu, dan (Kowa yasan baba iliyasu da matarsa yake shima).
A mamakin kowa sai akaga mama gaje ta miƙe bata cema kowa uffanba ta shiga ɗaki, mintuna baifi gomaba ta fito sanye da hijjab ta fice daga gidan nanma bata tankama kowaba.
Da kallo duk suka bita, dan zukatansu sun fara basu ƙwaƙwalwarta kamar ta fara samun matsala.
Babane yace Mudan ya bita yaga wane hali take ciki, koda Mudan ya biyota sai yaga ta tari napep tana faÉ—a masa ya kaita anguwar su inna mari.
Gida Mudan ya koma ya sanar musu, hakan ya saka baba Yusha'u faɗin, “Dama kune kuke ɗaukarta mai matsala, amma ni nasan wacece gaje, tajecan ta ƙarata, nidai na yanda ƙwallon mangwaro na kuma huta da ƙuda�.
Shiru kowa yayi, sai iyace tai gyaran murya, dan haka kowa ya maida hankalinsa gareta.
Nasiha ta shiga musu, tare da nuna musu muhimmancin zumunci da sakamakon mai wargazashi, takuma sakasu suka ƙara neman gafarar juna, taima su Ayyah nasiha akan su ƙara haƙuri da kowa su cigaba da ɗaukar girman da ALLAH ya ɗora musu, insha ALLAHU zasu cigaba da zama masu ribane har abadan.

_________________________

A saudiyya ma dai abubuwa sunyi sauƙi, sai dai abinda zuciya ta gaza mantawa, dan a tsakaninnan ba ƙaramar tsanar Samina Ahmad ke ƙara jiba a ransa sosai.
Ko gida ya tuna sai kaga ɓacin rai ya mamaye fuskarsa, abu kaɗan zai kama faɗa a kansa, ranar tsautsayi na bin Haysam Rumana ta ajiyema Ahmad ɗin tea zaisha da daddare wajen tsalle-tsallen yara na wasa ya ɓarar dashi, aiko Ahmad ya kama faɗa hardasu zane Haysam yayi.
Agaban Rumana komai ya faru, amma sai ta ɗauke kanta tankarma batasan sunaiba, sai Zainab ce keta kuka tana roƙon Ahmad yayi haƙuri, daga ƙarshema Rumana sai tabar masu falon kawai.

Ranar Haysam yaci kuka yaronan abin tausayi, daga ƙarshe yay barcin dole.
Tun daga lokacin ya koma tsoron Ahmad ɗin, ko sallamarsa yaji zakiga ya gudu ya ɓuya koda a bayan Rumana ne ko Zainab.
Sai kuma abun ya fara damun Ahmad ɗin, ranar ya dawo daga makaranta da wuri ya iske Rumana kwance bata da lafiya, duk da dai taƙi sanar masa, dan takai sati uku tana fama amma ganin yanayin da yake ciki na saurin fushi a wannan tsakanin saita danne tai gum da bakinta.
Yau É—inma koda ya fahimci bata da lafiyar sai ta fuske abinta.
Shine ya kasa haƙuri ya tambayeta da cewar, “Ruman lafiya kuwa?�.
Kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta tana cewa, “Babu komai�.
Duk yanda yaso jin damuwarta taƙi faɗa masa, tama haɗe fuska taƙi sake masa kamar yanda ta saba.
Numfashi ya sauke kawai ya shiga bayi yayi wanka, harya fito bata motsa daga kwancen da takeba a gado, ya zira jallabiya fara yana mai satar kallonta, “Bara na ɗakko Sadauki a makaranta�.
“Uhum� kawai tace masa ta ɗauke kanta.
Ya kalleta da ƙyau yanajin mamaki a ransa, amma ganin taƙi kallonsa sai ya fita kawai.

Koda Ahmad yaje makarantar su Haysam ɗaukarsa Haysam sai yaƙi yarda dashi, anyi lallashin duniya yaronnan yace shi sai dai Ummien sa ya keso.
Badan malaman sun san Ahmad ba, kuma ga tsananin kamar da Haysam keyi da shi da sai suce kodai dama ba mahaifinsa bane?.
Lallashi da wayo irin wanda akema yara babu wanda ba'aima Haysam ba amma yaƙi kallon ko Ahmad ɗin.
Wannan abu yay masifar sosama Ahmad rai, har ya gano kuskuren daya tafka ga iyalan nasa da basu da laifin komai akan damuwarsa.
Daga ƙarshe dole sai ɗaukar Haysam Ahmad yayi yaron na kuka tamkar za'a yankashi, sauƙinsama makarantar kusa da gida take, bawani uban nisa bane mai yawa tsakaninsu.
Har sukaje gida Haysam na turje-turje da kuka.
Umm-Ruman na bayi tana amai suka shigo, ta kuskure bakinta ta fito jikinta duk babu ƙwari, ga fuskartama ta nuna alamun a wahale take.
Ahmad ya sauke Haysam yana kallonta, itako ta É—auke kanta ta haye gado ta sake kwanciya tana jan bargo.
Haysam kuwa da Ahmad ya sauke da gudu yaje ya maƙalƙaleta yana ɓoyewa cikin bargon data lulluɓa.
Jikin Ahmad sai ya sake yin sanyi, ya zauna a bakin gadon yana mai zuba musu ido ranshi na ƙuna.

Har washe gari Ahmad na tare da wannan damuwa, dan da safenma Haysam ƙin yarda yay ya kaisa makaranta, gashi Rumana na kwance babu lafiya sosai, ko breakfast ma sai Zainab ce ta haɗa musu saboda tana ƙoƙarin koyama yarinyar duk abinda ya dace.
Dole sai Zainab ce ta ɗauki Haysam ɗin, Ahmad na biye dasu a baya har majarantar, daga can itama ta wuce shikuma ya dawo gida..............✍�

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
8/

...............Zama yay a bakin gadon yana mai kai hannu ya yaye bargon da Rumana ke ciki, duk tana jinsa, amma rashin ƙwarin jiki da take fama dashi saboda yawan amai ya hanata koda kallonsa.
Hawowa yay gadon ya kwanta bayanta tare da mannata a jikinsa, ya sauke ajiyar zuciya yana lumshe ido saboda zafin da jikinta ya É—auka.
Itama ajiyar zuciyar ta sauke amma ko motsawa batayi ba.
Murya ƙasa-ƙasa yace, “Haba Gwal ɗina, yanzu wannan rayuwar da kika zaɓa mana kina ganin ta dace kenan? Ace kina fama da ciwo amma kinƙi yarda muje asibiti?�.
Murmushi ƙaɗan Rumana tayi jin furucin yayan nata, batace dashi komaiba itadai.
Shima tashi yay zaune ya yaye bargon gaba ɗaya, sannan ya ɗagota jikinsa yana faɗin, “Please muje namiki wanka, kuma banason musu�.
Bata musa masanba kuwa, dan tana buƙatar wankan, rashin jin ƙwarin jikine ya hanata tashi, da taimakonsa tai wanka da ruwa mai ɗumi sosai dataji ƙwarin jikinta kaɗan, koda suka fitoma shine ya taimaka mata ta shafa mai ta saka doguwar riga.
Shima shiryawar yayi ya ɗakko kayan karin da Zainab ta haɗa musu ya kawo ɗakin, amma sai Rumana tace bazata iya ciba ta ƙoshi, da ƙyar ya takura mata tasha shayi babu madara, aiko tana gamawa sai amai.
Da gudu ta tashi zuwa bayi shima ya bita, ta bashi matuƙar tausayi, sai kuma ya fara zargi a ransa kodai cikine da Gwal ɗin tashi?.
Wani irin É—oki ya ziyarci zuciyarsa, dan haka suna fitowa cayay mata asibiti zasuje, duk yanda take masa magiyar ya barta, bai sauraretaba ya saka mata gyalen jallabiyar dake jikinta, dole ta yarda suka tafi kuwa.

_______________________________

Rayuwar jail da Samina ta tsinci kanta a ciki rayuwace da sam bata da daÉ—i, dan ALLAH ya haÉ—ata zamane da wasu mugaye dake azabtar da rayuwarta.
Cikin ƙanƙanin lokaci komanta ya canja, tai wani irin baƙi saboda man bilicin da fuskarta bata samu, gashi tayi gida-gida tamkar ta ƙone, ga ƙuraje.
Yayinda zuciya take azabtuwa ta tarin ƙaunar Ahmad da baisan tanayiba, tunda take a rayuwarta bata taɓa jin son Ahmad mai masifar zafi irin a wannan tsakaninba, ji take idan bata rayu da shiba tamkar zata iya rasa ranta, kullum cikin tunaninsa take da roƙon ya dawo gareta dan ALLAH.

Samina Ahmad baya jin wannan kirayen naki sam, sai dai haƙuri kinji😢🤒.

Tana ambaton kalmar data sani gameda Sanin Ma'aruff fiye da sau dubu a rana, tare da ɗunbin jin zafin mahaifiyarta da kakarta da tafi tsana fiye da kowa yanzun a duniya, dan a ganinta kakarta inna mari ce silar komai, sai ƙawayen banza mugaye irinsu Nafy, tare da son zuciya da ruɗi na neman wayewa da son duniyar da baida amfani, domin ita dai gashi bai mata amfaninba.

_______________________________
Chapter 82 · 0% Book details