← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 94

Sashe 77

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tafiyar Ahmad ta gama kankama, zai fara yin gaba kafin yaga abinda ALLAH zaiyi game da iyalinsa da yakeson su bishi, yana tare da damuwa game da karatun Zainab data fara za'a datse mata, dan bazai yuwu su koma can su kaÉ—ai su zaunaba, amma da yay shawara da su baba sai sukace aje da Abu can porthercout É—in sai ya zauna dasu Rumanan har aga abinda ALLAH zaiyi.
Kowa yayi na'am da wannan shawara.
Tare sukai shiri suka koma port, suka sake barin Æ´an gidansu da kewa, kowa kuma nabin Ahmad da addu'ar fatan alkairi da É—unbin nasara.
Duk jarumtarsa sai da ya share hawaye, dan yanaji a ransa kamar bai zama lallai ya sake ganawa da wasunsu ba, koshi ya mutu, kosu wani ya mutu.

Wannan tafiyar harda Abu aka yita, hakan yasa Ahmad da Umm-Ruman suka zauna a baya, Abu da zainab kuma na gaba dan shata ya É—auka wannan karonma.
Sun isa gidansu da sukaima yajin sati biyu, a ranar da suka isan dai babu abinda suka iya tsinanawa saboda jigata, dan wannan tafiyarma tiɓis su Rumana suka isa, hatta da Abu kansa dan shima bai taɓa doguwar tafiyaba irin haka.
Haysam kam wannan karonma ragal yake yaronnan, sai dai yayi barci ya farka.

Washe gari kasancewar Abu ba mutum mai ganda ba da taimakonsa Umm-Ruman ta gyara ko ina ya É—auki haske, Ahmad kam ma tunda safe ya fice gidan, bai dawoba sai yamma tare da Happy.
Duk da Rumana tayi mamakin ganinsu taren sai batace komaiba, ta tarbeta da mutunci kamar yanda ta saba, sai da suka shiga É—aki Ahmad ke sanar mata anan Happy É—in zata kwana.
Murmushi kawai Rumana tayi batace dashi komaiba, ya riƙo hannunta yana tsatstsareta da idanu.
“Naji bakice komaiba?�.
“To Yaya mizance? Tunda da dai ga ɗakin Zainab basai tai kwanciyarta ba�..
Baice komaiba ya sake mata hannu, ta fice shikuma ya bita da kallo kawai yana girgiza kai, akan laɓɓansa ya furta “Kishi kenan Gwal?� babu mai bashi amsa, dan haka ya taɓe baki kawai.

Washe gari ranar tafiyar Ahmad, bayan ya gama kimtsawa suka rankaya domin masa rakkiya a motar daddyn Happy da sukazo.
Kallo ɗaya zakaima Umm-Ruman kasan ta ƙwaɗi kuka a daren jiya, shi kansa Ahmad wannan tafiyar jiyake kamar yayta kukan, Haysam nata barcinsa har suka isa Airport ɗin.
Zaman da baifi na mintuna talatinba aka fara sanar da shela akan matafiyan, nanfa ran Umm-Ruman ya sake dugunzuma.
Ahmad dake zaune kusa da ita ya sauka yay durƙuso a gabanta tare da kama hannayenta duka cikin nashi, yau ko kunyar Abu da Zainab baijiba.
“Haba Babie R ki daure Please, insha ALLAHU kuma nan bada jimawaba zaku bini, saboda inason ku kasance kusa dani yasa na zaɓi ƙasar saudia domin yin karatunnan koda aka bani zaɓi, saboda inason yarana su tashi da cikar burina, insha ALLAH bazan ɗau lokaciba zaku matso kusa dani kuma kinji, ki kulamin da Sadaukina, idan kuma nayi ajiyar ƙanwarsa anan itama a bata kulawa�. ya ƙare maganar da shafa cikinta
Kanta ta ɗaga masa tana share hawayenta da murmushi a lokaci ɗaya, ya miƙe tsaye tare da sumbatar goshinta yana saka mata albarka shima da murmushi shinfiɗe a tashi fuskar.
Barin gabanta yay yaje ya sumbaci Haysam dake barci a bayan Zainab, itama ya kuma mata gargaÉ—i akan karatu.
Ya matsa yayma su Momyn Happy sallama yana sake musu godiya, sai ga Happy na hawaye, badan tasan bayaso ba da babu abinda zai hanata rungumeshi.
Ya bama Abu hannu shina yana sake jaddada masa ya kula sosai, cikin girmamawa Abubakar ke amsawa yayan nashi, tare da jera masa addu'oin fatan alkairi da nasara.
Harya tafi ya dawo wajen Umm-Ruman da duk suka miƙe tsaye ya rungumeta, dole Abu da Zainab sai ƙasa sukai da kansu.
Jin sunansa da aketa ambatane ya sakashi sakinta ba tare dayace uffnba ya juya ya fita.
Momyn happy tazo ta rungume Rumana a jikinta tana lallashi, da ƙyar suka samu tai shiru.

Sai da jirgin su Ahmad ya lula sannan suka bar airport É—in, har gida su Dadyn Happy suka maidasu sannan suma suka wuce.
Umm-Rumana ta shiga ƙunci akan tahowar Ahmad porthercout balle barin ƙasa baki ɗaya, ranar har Haysam saida ya shaida tana fushi, dan ƙiri da muzu taƙi bashi nono sai tea sukaita banka masa da abinci.
Ƴan gida sunata kiranta harda amare su Fa'iza, sanda suke waya da Ammi saita saka mata kuka, Ammi ta yanke wayar kawai.
Haka ma baba kuka taitai masa, shidai ya allasheta da kalamai masu daɗi akan tabi mijinta da addu'a ba kukaba, kalaman babane suka sanyaya ranta harta daina kukan..............✍�

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*_64244456G_*

..............Ahmad an sauka ƙasar saudi-arebia, ƙasa mai tsarki, mahaifar MANZON ALLAH (tsira da amincin ALLAH su ƙara tabbata a gareshi), wajenda ɗakin ka'aba yake, gari mai farin jini da tarin al'umma, mai tarin ni'ima da burin zuwa ga kowa.
Jirginsu ya sauka a filin jirgin birnin Dhahran, Baisha wata wahala ba saboda haɗashi da yaron ogansa daya koya masa sana'ar ɗan kunne da akai tunkan ya taho, shima yana karatu anan ne, sai dai shifa ustazu ne na gaske, dan yana karatune ɓangaren islamic, an kwankwaɗi madarar ilimi sosai, sai dai muyi fatan ALLAH ya bada ikon amfani da shi, da amfanar da sauran al'umma.
Kasan cewar an tura masa hoton Ahmad shima kuma Ahmad É—in yana da hotonsa sai babu wahala suka gane junansu.
Cikin al'ada irin ta larabawa suka rungume juna kafin suyi musabaha kamar yanda ustaz ya nuna yafi buƙata, kowanne fuskarsa ɗauke da murmushi shinfiɗe, bazasu gaza sa'annin junaba, dan shima ɗin dai kwanan nan akai masa aure aka turo masa matar nan.
Suna riƙe da hannun juna har lokacin Ahmad yace, “Muh'd Gaddafi Umar ko? Idan banyi mantuwa ba�.
Murmushi yay masa shima yace, “Hakane abokina, kaima Ahmad Hamza Rabi'u.
Ahmad yay ƙaramar dariya yana jinjina masa kai, abinka da masu ilimi, sai suka sake da juna dandanan kamar sun daɗe.
A gidan Muh'd Gaddafi Ahmad ya samu masauki, inda akai masa tarba ta mutunci da bazai taɓa mantawa ba, duk da amaryar Muh'd na fama da laulayin ciki haka ta shirya musu liyafa, Saudia taima Ahmad ƙyau, musamman birnin Dhahran da ya sauka, jinsa yake a yau tamkar wani sabon mutum, har suka iso gidan Gaddafi idonsa bai daina kalle-kalle ba.

Bayan sunci sunsha aka kaisa inda zai kimtsa ya hutama ransa, yakoji daɗin hakan dan hutun yake buƙata dama sosai, sai dai koda ya kwanta sai tunanin ahalinsa ya hanasa rintsawa, ya tabbata yanzu Rumana nacan cikin damuwa har yanzu, tafiya iya porthercout kawai ta saka kanta a matsananciyar damuwa inaga yabar ƙasarma baki ɗayane, ko Haysam zaiyi kuka in bai gansaba oho.
Yata tunane-tunane kafin barci ya sacesa.

Rayuwar gidan Gaddafi ta birge Ahmad sosai, dan ya fahimci akwai tsantsar ƙauna a tsakanin ma'auratan da soyayya mai tsafta, hakan sai ya tada masa nasa tsumin akan tashi gimbiyar da a yanzu ta zama wani sashi na rayuwarsa, sai murmushi yake saki tare da ƙara jin ƙaunarta da begenta mai tsanani.
Ya ƙanƙame filo a ƙirjinsa yana sauke nannauyan numfashi tare da rumtse idanunsa da kiyasto Baby R ɗinsa a yanayin da yazame masa sirri mai daraja da mutuwace kawai zata iya masa shamaki da tunawar.

_________________________________

Kwanaki Biyu Rumana na a sukuku da ita, kafin kuma ta saki jikinta ta koma normal, dan Ahmad ya kirata a ranar da Safe da wayar Gaddafi, tayi farin ciki sosai kuwa, yanda yake bata labarin kansa a saudia sai taji kamar tai tsuntsuwa ta ganta acan.
Su Zainab ma duk sai da ya gaisa dasu, hakama Haysam an saka masa wayar yanaji hayaniyarsa duk da shi yaron baisan anaiba ma.
Gidama Ahmad ya kirasu dan su sami kwanciyar hankali, aikam duk sunji daÉ—in hakan sosai, sunata jifansa da addu'oin fatan alkairi.
Cikin jin daɗi da tsantsar kewarsu yake amsawa har yanajin ƙwalla ta taru masa a idanu, ahalinsa suna da muhimmancin da bakinsa bazai iya furtawaba a rayuwarsa, yana addu'a rabbi ya azurtashi da halalinsa mai albarka da zai tallafi rayuwar sauran ƙannensa masu tasowa, suma su sami ilimi wadatacce kamarshi, ba dole sai na boko ba, na addini shine jagaba akan komai, shine kuma ake ribantuwa dashi a duniya da lahira, dan haɗuwa da Gaddafi ya sake tada masa kwaɗayi akan son sake zurfafa ilimin addini a rayuwarsa, sannan yanama ƙannensa sha'awar hakan suma.

___________________________________

Duk wani shigi da fici na karatun Ahmad da taimakon Gaddafi da yasan gari yayisa, sosai jami'ar *_King Fahd University of Petroleum & Minerals_* ta ƙayatar da Ahmad, ya zama ɗan ƙauye a cikinta, “kaga gini tamkar ba hannune yayisa ba malam Gaddafi?�.
Gaddafi dake kallon Ahmad yay murmushi yana mai sake bin makarantar da kallo shima, yace, “Ai Birnin Dhahran yana cikin manyan birane na duniya masu ƙayatarwa, shiyyasa da yawan Universitys da sauran makarantu dake wannan birnin zaka samesune a ƙawace, birnin da fadar saudiyyarfa yake kenan, kasanko ai dole komai na cikinsa ya ƙawatar�.
Ahmad ya sauke numfashi yana faɗin, “Lallaikam, cigaban da ya gagari namu ƙasashen kenan, kowa da ga aljihunsa saina ƴaƴansa da iyalansa ya sani, ALLAH ka azurtamu da jannatulfirdausi maɗaukakiya�.
“Amin ya rabbi abokina�
Gaddafi ya faɗa yana maijin takaicin al'ummarmu da suka dauki zalunci ƙaramin abu da bazai taɓa komai na rayuwarsuba, balle ya ragesu, sun manta da inda ake biyan zalunci komin ƙanƙantarsa da ayyuka, ranar da kowa ayyukan yafi buƙata ruwa a jallo, ranar da in baka da ayyukan kwarai a taskarka zunibin wanda ka zalunta za'a ɗiba a maka maka (Ya rabbi ka rabamu da rufaffiyar zuciyarda shaiɗan ke gadinta, ka azurtamu da ganin gaskiya komai dacinta garemu, ka hanamu zalintar duk wanda ALLAH ya haɗamu zama dashi koda ba'amuhalli dayaba, ka hanamu hassada da ƙyashi wa kowa, ka hanamu ƙuntata zuciyar kowa a rayuwarmu, ka hana maisan ƙuntata mana samun nasara a kayinmu😭🙏🏻).
Har suka isa gida suna cigaba da tattauna matsalolin ƙasarsu ne da suka baro.
Chapter 77 · 0% Book details