← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 94

Sashe 24

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kamar yanda na saba da safe nai ƙokarin fara sharar tsakar gidan, lokacin Yah Ahmad ya koma barcin safe dana kula ya iya, kuma tunma yana gida dama yakan taɓa wani lokacin.
Dariyar da naji a bayana ya sakani ɗan waigawa, wadda nake ƙyautata zaton amaryace naga sun fito daga ɗakinta da angonta, kallo ɗaya zaka fahimci suna a cikin nishaɗi, tana ɗaure da zanine sai tawul data yafa, shikuma jallabiya yana riƙe da botikin ruwa.
Janye idona nayi daga garesu, sai da sukazo gittani ne na gaishesu.
Duk sun amsa min sannan suka wuce Bayi a tare, babuko kunyata suka shiga bayi suka rufo suna cigaba da dariyarsu ta nishaÉ—i.
Ni dai sharata kawai na cigaba dayi ba tare dana sake bi takansu ba har suka fito suka wuceni zuwa ɗakinsu tana masa shagwaɓa wai ya ɗauketa ya kai har ɗakinsu.
Tofa, yau naga abinda ya girmeni.
Na faÉ—a a zuciyata ina kwashe sharan dana tattara.
Daga haka na É—iba ruwa na wanke bayi shima kamar yanda na saba, sannan na fara jan ruwa a rijiya na zuba a banbuna na É—aki dana waje duk da dama ina da ruwan.
A lokacinne maman Ama ta fito, muka gaisa na tambayi lafiyar yara ina ƙoƙarin shigewa ɗakina, dan na lura bakinta da magana sosai, niko banason wannan halayyar sam.
Ƙofar ɗaki na kawo risho ɗina kamar yanda na saba na ɗora ruwan zafi, yana tafasa na juye a filas na saka ɗumamen tuwo shima, kwanikan dattin na zubasu a roba babba a nufina bayan mun karya saina haɗa duka nayi.
Ina gama É—umama tuwo na juye a kula na kashe risho É—in na zuba ruwan wanka abina.
Lokacin nake jiyo gulmar da Maman Ama keyi da mijinta daga kicin ɗinmu da ita kawai ke amfani dashi, danni tunda nazo gidanma ban taɓa koda leƙashi ba balle akai ga amfani dashi.
Kaina naÉ—an girgiza ina mamakin wai maza ma sun iya kananun magana, ni dai na wuce bayi nayo wanka nazo na shige É—akina kawai.
Yanda kukasan mara gaskiya haka naita ƙumu-ƙumun saka kaya a cikin hijjabi, duk da nasan dai Yah Ahmad barcinsa ma yake, na gama ina tsaka da shafa mai ya farka, zaune ya tashi fusaka duk babu walwala, na ɗan saci kallonsa na kauda idanuna ina shafa kwalli a idona.
Tashi yay ya fita bayan ya ɗauki brush ɗinsa da ya sakama makilin akan madubi, hakan yasa na miƙe da azama nahau gyaran gadon, dan nasan maybe ya jima bai dawo ɗakinba, ilai kuwa harnai shara ma da sauri-sauri bai shigo ɗinba, sai da ina kwashe ƴar ƙurar dana tattarane ya dawo, matsa masa nai ya shigo ni kuma na fita zubar da sharan.
Koda na dawo bakina da nashi bai saɓa ba, nagama jera abincin a gabansa, duk da dai kulan tuwon dana ɗumama ne kawai sai filas ɗin shayi da kofi, sai ko guntun biredin jiya dake a leda da saurin sukarin da ya siyo gwangwani ɗaya, sai madara sacet uku nescafe guda uku shima duk a ledar.
Gani nai ya miƙe bayan ya ɗora idonsa akan ledar biredin dana ajiye, ya ɗauki wandonsa daya cire jiya ya ciri kuɗi ya fita.
Da kallo kawai na iya binsa, danni wannan halayyar tasa tana damuna bata damuna, abinda yasa nace haka dama can na saba babu wata shaƙuwa ta zaman hira ko abinda ya danganci hakan a tsakaninmu, nasan ko ba ƙaramin abu bane ace yanzu da wuri mun saki jiki wa juna da yanda naga ma'aurata nayi, abinda yasa take damuna kuwa shine kaɗaici, a gidan dai shi kaɗai nasani, ko yaya ina buƙatar sassauci daga garesa kodan nima naji sanyi a raina, na tabbata da aunty Samina ya aura da ba'aga haka daga garesa ba, dan bazasuyi kalar wannan zamanba saidai na farinciki fiyema da yanda naga amarya da angoncan yau.........
“K wai tunanin mi kikeyi haka?�.
Maganarsa aɗan zafafe ta katseni daga dogon tunani na, bansan ya dawoba sam wlhy, ina fiki-fiki da idanu nace, “Ba komai�.
Banza yaymin bai tankaba, hakan yasa nima na shiru na fara ƙoƙarin haɗa masa shayin da akema shan dai-dai ruwa kawai.
Nasan tunda akwai tuwo bazai ci biredi ba, dan haka na saka masa tuwon na tura gabansa, niko na haɗa tea ɗin nasha da biredin daya rage, na ɗan ɓalla a wanda yaje ya siyo saboda wancan guntune.

Abinda ya bani mamaki koda muka gama karyawa yau bai fitaba, zamansa yay a gidan, sai ma waya da ya É—auka ya kira Yaya Mudan ya kawo masa wasu kaya zai yanka a gidan.
Ni dai ƙala banceba, sai dai zuciyata nata zungurata akan nai masa maganar wanka.
Na daɗe ina mulmula maganar kafin da ƙyar na iya fiddata, “Yaya ko zakai wanka tunda akwai sauran ruwan zafi a filas?�.
Shiru banji ya amsaba, hakane ya sakani satar kallonsa, sai naga ashe ni yake kallo shima, jinai duk na daburce, dan kallon dai irin na kinma samin idon nan ne, to amma ya zanyi tunda nai suɓutar baki.
Banyi zatoba naji yace, “Haɗa ruwan�.
Ai zumbur na miƙe kamar dama a ɗofane nake, ina kallonsa ya kauda kai yana murmushi, da alama dai yanda nake a tsoracene ya bashi dariya shima.
Duk da ya kauda idonsa kar naga murmushin naji sanyi a raina sosai, dan na jima banga hakan daga garesa ba.
Ina dawowa daga kai masa ruwan na haÉ—a wanke-wanke na fice abina gaban rijiya.
Ina ƙoƙarin farawa yazo ya gittani ya shiga bayi.

Kamar jirana maman Ama take sai gata itama ta fito dana wanke-wanken daga É—aki tazo ta tsira kujera gefena ta fara.
Da farko tsokanar Amatullah na fara muna dariya, sai ta rage murya ƙasa-ƙasa tana faɗin, “Amarya anya kuwa wannan amaryar jiyan zamu dai-daita da ita? Babu wanda zaice gidanan ga yanda daren farkonki ya kasance saboda kunsan kanku daga ke har mai gidanki, amma ita jiya ihu taitaima mutane na rashin mutunci, ita ba budyrwa ba balle ace�.
Sosai gabana ya faÉ—i jin ta ambaci daren farkona, gefe kuma ina mamakin wannan saka ido irin na maman Ama, wato ita idonta na kammu ashe akan taji yaya mukai daren farko? Tab anya kuwa zaman gidannan bazai canja saloba?.
Ban samu bata amsa ba naji motsi a bayanmu, da sauri na waiga sai naga Yah Ahmad ne, da alama dai yama ji duk mi maman Ama ta faɗa, dan wata uwar harara ya zabgamin yana ƙaramin tsaki ya shige ɗaki.
Innalillahi kawai na iya ambato a raina, na kai kallona ga maman Ama dake cigaba da zabga surutu ita koma lura da yah Ahmad É—in bataiba......
“Amarya wai yanaga kinyi shiru....?�
Murmushin yaƙe nayi ina girgiza mata kai, “Babu komai maman Ama, kawai dai banda abin faɗane, ni kitsoma nakeson naje, nasan kuma Yaya bazai barni naje gidaba, ko akwai maiyi anan kusa?�.
Nai maganar domin kauda surutanta marasa ma'ana.
Tace, “Eh to sai dai nan gidan matar Ali, ta iya kitso kam sosai wlhy, dolene kikayi oga sai yayi biyan da bai shiryaba�.
Nanma Murmushi kawai nayi, hakan kuma yay dai-dai da sallamar Yah Mudanseer daga soro. Na gane muryarsa shiyyasa na amsa masa ina faɗin “Ya Mudan ka shigo mana�.
Ya shigo da sallama, ya gaida maman Ama ba tare da ya kalli inda muke ba ya shige É—akinmu.
Nima tashi nai na zubar da ruwa dan na gama sai tukunya, itama a tsaitsaye nai wankinta na kwashi kayan nabar maman Ama a wajen.
A É—aki na iske Yah Mudan suna hira da Yah Ahmad, sai tsokanarsa yake yana murmushi, nima ina shiga ya dawo da tsokanarsa kaina, dariya kawai nayi na ajiye kwandon wanke-wanken dana É—ora a tire ina gaidashi, a kuskure muka haÉ—a ido da Yah Ahmad dake duba littafi turamen zani kusan shida ajiye a gabansa.
Babu shiri na É—auke kaina, shima sai ya ajiye buk É—in yana kallon Mudanseer.
“Mudan zokaje can wajen kaɗanyo mana cefane kafin ka wuce, dan yankannan zai iya ɗaukata dogon lokaci ban iya tashi nayo ba�.
“To yayana ɗan gidan Ayyah, angon ƙanwata Umm-Ru ma na�.
Ya ƙarasa sunana da ɗai-ɗai saboda hararar da Yah Ahmad ya banka masa.
Fita yay yana dariya, Yah Ahmad yace, “Shashasha kazo ka amshi kuɗin�.
Daga bakin ƙofa yace karka damu akwai kuɗi jikina, ƙanwata mi za'a sayo?�.
Kallon Yah Ahmad nayi dan nima dai bansan mi za'a sayo ɗinba tunda ba taɓa tambayata yay ba idan zaiyo cefane shi, niko kullum abincina baya wuce taliya da mai da yaji saboda shegen kwaɗaina, sai shinkafa da wake, ko dafa duka.
Shima da ya kalleni sai ya janye idonsa ya maida ga Yah Mudan ɗin, shine ya lissafa masa abinda zai sayo, ya miƙa masa ɗari biyar yana cewa, “Ka ƙara da wannan tunda cefanen da yawa�.
“A'a kabarsa yaya, akwai kuɗin ɗinki da yaron malam ya bani yanzun nan zanzo nan, bara naje na dawo�.
Yah Ahmad ya maida kuÉ—insa a aljihu, Yayinda Yah mudan ke ficewa shi kuma.
Ni dai duk ina zaune gefe ne ina saurarensu, tsarinsu na ƙara birgeni, dama can kowa yasan akwai shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninsu.
Chapter 24 · 0% Book details