← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 94

Sashe 42

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Samina na tsakkiyar ƙawayenta ana rangaɗa mata kwalliya wasu ƙawayenta biyu da suka iso kusan tare dasu Rumana suka shigo musu da labarin soyayyar da suka gani a waje na wasu sabbin ango da amarya, dansu basusan Ahmad ɗinba.
Tsigil wata ɗiyar ƙanwarsu mama gaje tace, “Aunty Samina Ahmad nefa da Rumana�.
Wani irin faɗuwar gaba Samina taji har tana kaɓe hannun mai kwalliyar, tayi kicin-kicin da fuska dan zuciyarta sai zallo take tamkar zata faso ƙirji ta fito, a yanda ƙawayenta ke bada labarin lallai show ɗin ya ƙayatar kuwa, ganin zata sauka a layi Nafy tai saurin ƙwaɓarta.
Duk yanda taso dai-daita kanta saita kasa, dan kuwa ahankali maganar abinda Ahmad ɗin yayi yaketa fitowa daga bakunan mutane, wasu suna ganin yayine dan kawai ya nuna yanzu Samina bata ransa, wasu kuma na faɗin kawai tsantsar ƙaunar dake tsakaninsa da matarsane ya nuna kishinta.
Samina jitake kamar ta fara dannama duk wanda ya ambaci sunan Rumana da Ahmad zagi a wajen............✍�

_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_

_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_

Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo

*_GDW_*

*(24)*

..............Su Rumana dai an shige cikin dangi, kowa sai haba-haba yake da ita, iya kuwa harda guɗa ta callara akan Umm-Rumana, hakan ya jawo kallon Rumana ya ƙara armashi cikin taron, dangin mama gaje da hassada keci sai kusheta suke, ƴan uwanta kuwa dana mahaifiyarta daɗin ganinta cikin shigar kamala duk sai ya lulluɓesu, ko ba komai dai Ahmad ya tabbatarma duniya ya amshi zaɓin ALLAH kuma yabi umarnin iyayensa.
Babu wanda yay tunanin ganinsa cikin taron bikin sai gashi harda matarsa, kuma abin birgewa cikin aminci da cikar haiba aka gansu, ba kamar yanda su mama gaje suke tunanin soyayyar Saminar ta cigaba da wajiga rayuwarsa ba har a wannan lokacin.
Dan bokanta ya tabbatar mata Ahmad tsiya-tsiya zai dawo daga neman kuɗin daya tafi, kuma bazai taɓa shiga gaban Samina ba ita zatai ta kasancewa a samansa, haka Rumana kuwa bazai taɓa ya kusanceta ba sai dai iyayenta su gaji su kashe auren.
Itama Umm-Ruman tun tana sinne-sinnen kunya harta saki jikinta acikinsu, dukda kuwa jitake kamar kowa yasan miya shiga tsakaninta da Ahmad, gashi dama bawani gama jinta tai dai-dai ba, irinsu Ayyah tsoffin mata dasu Iya kallo É—aya sukaima yanayin tafiyarta suka harbo jirgin.

A ƙofar gidama ga Ahmad dolene abun ya burgeka, harkokin gabansa kawai yake cikin abokansa, sam babu wata damuwa ko kaɗan a saman fuskarsa, shaftarsu sukesha cikin nutsuwa suna kwasar dariya.
Yanda ya nuna halin ko in kula ba ƙaramin burge iyayensa da abokansa yayiba.
Shiko harga ALLAH yanzu Samina bata gabansa, dan ƴan labaran daya samu akanta gameda rayuwar data zaɓama kanta da Ma'aruff ba ƙaramin tsanarta ya cusama ransa ba, balle yanzu da suka zama abu guda shida ƴar ƙanwarsa Umm-Ruman, saima ya kula dama can so yama rufe idanunsa bai kula Rumanan tafi Samina komai ba.

Har aka gama taruwa babu ango babu dalilinsa, hakama waliyansa, ga lokaci yanata ja, an tara mutane dukda sunada uzurorin gabansu, abokan ango dai sun iso, sai kiran wayar Ma'aruff ɗin suke amma tsabar wulaƙanci yaƙi ya ɗaga.
Sai da mutane suka gama ƙuluwa da takaici, wasuma harsun fara miƙewa sannan sai gashi, ko neman afuwar kowa baiyiba kuwa, da yake tare suka iso da waliyan nasa kawai ɗaurin auren akayi.
Kamar mutane akan ƙaya suke ana ɗaurawa suka fara watsewa, shi kansa angon dagashi har abokansa basu zaunaba suka ƙara gaba.
Aiko wannan abu ya zama ƙananun magana sosai a cikin gida, dan irin ƴar gaisuwar iyaye da anguna kanshiga yi su Ma'aruff basuyiba, balle amarya tai tunanin zasu ɗan ɗauki hoton tarihi haryaga kwalliyarsa ita taga tasa ya zamo musu ranar tunawa wata rana a gaba.
Samina ranta ya ɓaci, ta kira Number Ma'aruff amma yaƙi ɗaga mata, daga ƙarshema data jera masa kira kusan baƙwai sai ya kashe wayar gaba ɗayanta.
Wannan abu yaso É—imauta tunaninta kam, sai dai Nafy na tausarta saboda idon mutane.
A ƙofar gida kam yaran anguwa suka haɗa dj na shaƙiyanci, da waƙar MATAR JAMI'A ta Naziru Ahmad suka fara wadda kowa dai ya fahimci habaicine ga samina, daga nan suka cigaba da saka waƙoƙi kala-kala da dai ke gargaɗi ko magana akan butulci.
Ahmad da abokansa kuwa tuni sunbarma anguwar suma, dan dama sunada wajen zuwa auren kawai suke jira a ɗaura su ƙara gaba.

★★★★★★

Maganar farin ciki dai a wannan buki kam ƙalilanne, dan komai kaga yazo saika samesa a dagule da ɓacin rai, danma dai sunata ƙoƙarin rufe wani abun dan kar a fahimta ai musu dariya.
Da daddare ma sai da rai ya ɓaci akan ƴan ɗaukar amarya kafin abokan ango su iso, tsabar iskanci kuma dukda sun iso a makare sai sukace ƴammatan amarya kawai zasu ɗauka banda tsaffi.
Da ƙyar aka samo wani mai motar hayar taxi a anguwar ya ɗauki wasu a cikin iyayen Saminar tunda bazai yuwu ace ankai amarya babu danginta ko guda ba.
Abinda kuma basu saniba daga nan gidanma bawai gidanta aka nufaba da ita, hotel É—in da zasuyi dinner abokan ango suka nufa, shiyyasa ashe sukace Æ´ammata kawai zasu É—auka.
Ran wasu a cikin iyayen da suka bisu ya ɓaci sosai, dan dangin Ma'aruff ɗin sai kallon banza suke musu.
Ganinfa ana nemam wulaƙantasu suka zaro jikinsu suka fito domin dawowa gida.

Ga Samina kuwa duk ɓacin ran data shirya nunama Ma'aruff tana ganinsa sai taji ta daburce ta kasa ko tari, sai ma damuwa data shiga dangane da shashsharetan da yakeyi.
Har aka tashi wannan dinner bataga fara'arsa ba, sai dai idan abokansa ko danginsa sunzo kusa dasu yin hoto ko magana dashine zataga yana murmushi, amma ita magana ma idan tayi saiya ja lokaci yake bata amsarta, wata kuma ya share abunsa kamar bai jiba.
Ƙarfe ɗaya aka tashi, kowa ya kama gabansa bayan sunma Amarya da ango rakkiya gidansu, dan tsaruwa kam gida ya tsaru, dolene Samina ta kira kanta gwarzuwar shekara a wannan lokaci.
Sai dai suna shiga yaga abokansa sun wuce da ƴan uwansa ya saki hannun Saminar, ɗakinsa ya nufa ya barta a falo tsaye, tun tana tsammanin fitowarsa harta ƙosa ta bishi, tsabar rainin hankali iskesa tai harya shiga wanka, ɗakin ba baƙonta bane, tunda ansha kawota cikinsa a aikata abinda akeso da ita a ciki, sai dai an canja kayan cikinsa, waje ta samu ta zauna tana tsumayen fitowarsa.
Koda ya fito ya ganta kallo guda yay mata ya ɗauke idanunsa, cigaba yay da shirinsa kamarma baisan tana ɗakinba, ita dai Samina mamaki sai kuma ɗaure kanta yake, gani take tamkar ba Ma'aruff ɗinta bane mai sonta da ƙaunarta tare da tattalinta ga komai.
Bayan ya gama shirinsa tsaf yazo ya zauna a bakin gadon yana kunna lap-top, ga kofi daya ciko da fresh milk ya ajiye gefensa.
Kasa jurewa Samina tayi ta miƙe ta koma kusa dashi ta zauna tanata zabga ƙamshi mai daɗi kuwa.
Murya a raunane tace, “Wai lafiya kuwa Sweet?�.
“Mi kika gani?� yay tambayar ba tare daya kalleta ba.
Da ƙyar ta haɗiye busashshen yawun bakinta tana zuba masa mayun idanunta irin nasu Ahmad, “Sweet ka canja min, sai kace ba kaiba, kamar baka ɗokin ganina a gidanka matsayin amarya matarka ta sunna? Yanzu wane angone za'a kawoma amarya amma hankalinsa nakan aiki�.
Wata Æ´ar dariyar rainin hankali yayi ya juye gaba É—ayansa yana kallonta, yayinda yake kai kofin madararsa a baki yana sha.
“To ke kuwa banda abunki wane zumuɗi kike son ganina a ciki? Babu wani abu baƙon a gareni daga wajenki ai, kokuwa wannan faudar da zanen ƙunshin zan zauna kallo?� yay maganar yana lakato kwalliyar fuskarta a ɗan yatsa.
Wani mugun tsorone ya kuma dirar mikiya a fuskar Samina, tai galala da baki tana kallonsa ba tare da ta iya furta komai ba.
Bakinsa ya taɓe yana kauda kansa daga kallonta, “Miye abun mamaki a zancena, kema dai kinsan kowane ango yana rawar jikine ga amaryarsa saboda abunda zai amsa mai muhimmanci a gareta, to ni kuma an bani tun a waje ai, mizanma ɗoki kuma yau?�.
Hawaye masu azabar zafi suka fara gudu bisa fuskar Samina saboda kalaman da Ma'aruff yake gasa mata akan abinda shine yafi ƙarfinta ya amsa ba itace ta bashiba, hasalima tabi duk hanyar da zatabi danta tsare abunta sai irin wannan ranar amma saida ya ruguza mata shirinta.
Tashi tai ta fita da gudu tana kuka, ya bita da kallo yana taɓe baki, sai kuma yaja tsaki yana faɗin “Kajimin wawuyar yarinya, ballaga kawai mtsowww�.
Chapter 42 · 0% Book details