← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 94

Sashe 58

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahmad na fitowa Rumana da Sadiya suka shigo suma, sai kumbura fuska Rumana take saboda barcin data fara aka taso ta, ji take tamkar ta fasa ihu.
Ahmad ya sauke idanunsa a kanta, ta ɗan hasken farin watan daya gota sha biyar, hakan ya saka ƙyawunta kuma bayyana masa a cikin ido, ya sauke ajiyar zuciya kaɗan yana maida idonsa gasu gwaggo da Ayyah.
“Tom bara mu wuce sai da safen ku�.
Ayyah tace, “To ALLAH ya huta gajiya ɗan albarka, Umm-Ruman ALLAH ya ƙara lafiya kinji, aita addu'a dai ALLAH ya inganta mana ya kuma raba lafiya�.
Sadiya ce kaÉ—ai ta amsa, Ahmad da Rumana kunya ta hanasu cewa komai, hakama Gwaggo da tunda aka fara zancen cikin bata tofa nata ba, tana dai cikin tsantsar farin ciki a cikin ranta.
Itama Rumana tai musu sallama tabi bayan Ahmad da yay gaba.
Sai da sukaje soro ne ya juyo, hannunta ya riƙo ba tare daya ce komaiba, dan ya lura kamar barcin data fara bai saketa ba.
A ƙofar gida sukaci karo da motar Ma'aruff yazo ɗaukar Samina, amma sai masifa yake mata akan tun ɗazun yazo kusan mintuna talatin yana jiranta, itako sai faman lallaɓashi take dan karya ɗaga murya ƴan majalissar abokan su Ahmad su ji.
Fitowar su Ahmad ne ta saka ma'aruff yin shiru yana kafe Umm-Ruman da ido tamkar idanunsa zasu faɗo ƙasa, suko koma kallonsu basuyiba duk da su Ahmad ɗin sunji jarabar da yakema Saminar, sun gittasu Ahmad yajiyo warin giya ya buso, mamaki ya kamashi warin giya daga ina haka? Yasan dai mu al'ummar arewa kasantuwarmu mafi yawa musulmai bamu cika huɗɗa da giyaba musamman yankinmu da Hausawa sukafi yawa, sannan shi baima taɓa jin warin giyaba a ƙofar gidan nasu sai yau, to lallai yana zargin kamar mijin Samina ne kenan?.
“ALLAH ya ƙyauta� ya faɗa a zuciyarsa yana ajiye tunanin gefe guda dan ba damuwarsa bace. Napep ya tare musu suka shiga.
Rumana da idonta ke cike da barci ta kwantar da kanta akafaɗar Ahmad, kaɗan ya juyo ya kalleta, idanunta lumshe suke, hakan saiya kuma fiddo ƙyawunta sosai, ga kalar hijjab ɗin data saka ya kuma fiddo da ƙyawun fusakar tata ainun.
Hannu yakai ya shafa kumatunta a hankali, ta ɗan buɗe idanun nata tana kallonsa, nasa idanun ya lumshe mata shima yana faɗin, “Karkiyi barcifa fa, banida ƙarfin ɗaukarki�.
Fuska ta kumbura dama can haushinsa takeji yasa Ammi ta tada ita, dan tace ace ya barta ta kwana kuma Ammi ta hauta da faÉ—a dole ta taso.
Kansa yaɗan jingina jikin nata yace, “Ni bana faɗa yau�.
Murmushi tayi mai sanyi ta maida idanunta ta lumshe tare da riƙe nasa hannu sosai tana shaƙar ƙamshin turarensa na tun ɗazu dake manne da jikinsa.
Shima murmushin yayi idonsa akan hanya.
Shi dai mai napep yana daga gabane yana kallon ikon ALLAH ta madubi saboda fitilar daya saka a cikin napep É—in dake haska su Ahmad.
Koda suka isa gida bayan sun biyashi kuɗin, bai wuceba har sai da suka shige gidansu, Mai Napep yace, “ALLAH ka haɗamu da masoyan ƙwarai, kana gamo da irin wannan masoyan ai tuni kake tada ƙayar baya a gidanku ai maka aure yasin�.

Kunji mara man kai, sai kaje ka tada din😂⛹‍♀.

Ahmad ya amshi key ɗin ɗakin wajen Rumana ya buɗe, bata shigaba, hannu kawai ta zira ta ɗauki buta taje tayo fitsari sannan ta koma ɗakin, Ahmad na ƙoƙarin cire kaya ya tashigo, hijjab ɗinta kawai ta cire ta jefa saman gadon zata bishi ya riƙota.
“Daure muyi wanka saiki kwanta baki ɗaya kinji Babie R ɗina, maman kuma Babie na mai zuwa insha ALLAH�.
“Yayah Please wlhy barci nakeji, nidai yau bazanyi wankanba�.
Ya kula yau dai shagwaɓa takeji, sakata yay a jikinsa sosai suka zauna a bakin gadon a haka, cikin tausasa harshe yace, “Sorry Gwal ɗina daure kinji, zan saya miki sweet mai daɗi fa�.
“Kai yaya, wannan wayone fa wlhy�.
“Tab, waneni da yima Gwal ɗina wayo, ai kece Boss sai yanda kikeso za'ayi�.
Da wannan lallaɓar ya samu yaci galaba akanta harya cire mata kayanta, ya haɗa ruwan wankan da kansa ya tasata a gaba zuwa bayi.
Ita dai da ƙyar tai wannan wanka, suka fito kowanne yay alwalar kwanciya barci da brush, wajen shirin barcinma sai da yasha daga da ita, dan bil haƙƙi da gaskiya barcine taf idonta, to yau bata samu tayi ko barcin safe ba balle akai gana rana.
Duk ƙwazabar Ahmad kam ai dole yau ya ɗagama Rumana ƙafa sukai barcinsu, shi harma tsoro yake karya koma can kuma baya samu hakan ya damesa, duk yanda yaso dauriya da asuba kuwa ai bata yuwuba, sai da yaɗan rage zafi sannan yajisa dai-dai.

Shafin sabuwar tarairaya Ahmad ya buÉ—e ga Rumana, ita kanta abun har mamaki yake bata, data motsa zaice inane ke mata ciwo? Mi take so taci ko ta sha?.
Abun na bata dariya ainun, idan taso tsokanarsa har langare nasa take, sai ta gama tsurar dashi sannan ta dawo taita masa dariya.
Yakance babu komai i zai rama wataran, ta É—auka yanzu itace a ciki shine a kwana, amma wataran zata dawo kwanar shi kuma ya koma ciki.
Dole rayuwarsu ta burgeka, babu sanyi gaba É—aya, sannan kuma babu zafi mai tsanani.
Wataran ai farin ciki wataran saɓaninsa.
Inda ƴan gidansu abin ke ƙona musu rai, dansu UBANGIJI kan nuna musu farin cikin su Umm-Ruman ɗinne kawai.
Ɓacin ransu kuma suna ƙoƙari dannewa su shanye abinsu a cikin rai da cikin ɗaki, tunda ALLAH yayo Ahmad ɗin bamai hargagi ba, koda ɓacin ranne ya shigo cikin sanyi ake yinsa babu wani faɗa ko cacar baki a ciki.

_________________________________

Samina kuwa bayan wucewar su Ahmad ta jama Ma'aruff tsaki saboda kallon ƙurullar da yake binsu da shi, aiko yana juyowa ya daddage ya ɗauketa da maruka har biyu.
Da ƙarfin masifa ya turata mota ya rufe yana faɗin yau sai ta san ta masa tsaki wlhy.
Wannan abu kuwa duk a idanun abokan Ahmad dasu Mudan dake shago ya faru, sai yaran dake wasa a wajen, sunema suka kai labarin wannan mari cikin gida.
Baiko yi kaffara ba suna shiga cikin gidan ya hau jibgarsa ita kuma tana zaginsa da ja masa. ALLAH ya isa.
Sai da yay mata lilis da duka sannan kuma ya afka mata, taci wuya a hannunsa, dan yau ko aman da yay matama kasa tashi tai ta wankesa.

Washe gari kuwa labarin marin Samina yayta yawo cikin anguwa, Mama gaje taita masifa da cewar ƙaryane, kawai an sakama Samina idone anason ganinta cikin bala'i kuma baza'a ganiba, ƴan baƙin ciki sai dai su mutu.
Babu wanda ya kulata a gidan har taci ta tsire, sai daga baya ta kira Samina dan tasan tabbas da Ma'aruff bai mari Saminar ba da wannan zance bai fitoba.

Aiko Samina ta fashe mata da kuka, tare da zayyane mata dukan daya kara mata ma da suka ido gida.
Mama gaje tace, “Bar ɗan iska ai daga wannan karon dai ta ƙare, kedai kiyi duk yanda malam yace zaici ubansa ne matsiyaci, kuma zan koma zuwa gobe dan wancan cikin na shegiyar can baza'a haifesa ba, Ahmad bai isa samun ƴaƴaba har saikin samu Samina�.
Daɗi sosai yakama Samina, dan dama da baƙin cikin cikin nan ta fito Ma'aruff ya ƙara mata da haushin kallonsu Ahmad ɗin shine ta ƙare da cin duka a wajensa.

Washe gari duk da wuyar da taci a hannunsa sai da ya tsareta tai masa breakfast, yana fita aiki kuwa ta ɗakko abubuwan da malam ya bata ta fara ƙoƙari yin duk yanda yace tayi daki-daki.

Tsafi gaskiyar maishi, tun daga wannan lokacin Samina tace taga canji, dan yanzu kam ta sake kama Ma'aruff a hannu, koda giyarsa ya sha baya dukanta, sannan duk abinda ta tambayesa yimata yake, idan rashin kunyarta ta tashi kuma ta zuba masa gwargwadon iko baya iya ce mata komai.
A yanzu dai ta gama da matsalar ma'aruff kamar yanda ta faɗa, cikin jikin Rumana ne taget dinta na gaba, dan tayi alƙawarin sai yabi rariya, kuma da ga shi Umm-Ruman bazata sake ɗaukar waniba sai dai a lahira idan anayi.

Ni dai bilynku nace, “Hummm�.☹️😏

_____★_★_____★_★______★_★______

A wannan karon kwanan Ahmad tara ya juya, da zai tafinma sai da akasha daru shida mutuniyar, dan kuka taita masa ranarma, shi dai ya samu ya lallaɓa ya gudu yana jin ƙaunarta na mamaye duk illahirin gaɓɓansa da jijiya.

Ya tafi da kwana biyu Kausar ta tashi da naƙuda a safiyar Laraba, ranar dai kam a asibiti ta kwana, su Rumana nata mata addu'ar sauka lafiya.
Tasha wahala sosai kafin ALLAH ya sauketa lafiya ta santalo Æ´arta mace mai kama da ita.
Su Rumana na shirin tafiya dubota sai gasu sun dawo ma gida.
Daga ranar kuma aka shiga zaman bakwai, inda abin gutsiri tsoma ya samu ga maman Ama, dan duk abinda ba aima Kausar ba saita tanka, ita dai Rumana nata idone, sai idan dangin Kausar sun bukaci wani abu daga gareta ta basu, tanama É—aki kwance tana fama da kanta, dan tunda Ahmad ya wuce sai yazam bata cika jin daÉ—in jikin nata ba, dauriya kawai takeyi tunda dai ba sharkaf take a kwance ba.
A haka aka kwashe kwanaki shida da haihuwar Kausar, inda kuma aketa shirin suna gobe idan ALLAH ya kaimu.............✍�

Sai munzo cin rangam ni da Fans Kausar⛹‍♀

_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_

_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Chapter 58 · 0% Book details