Sashe 50
Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Tsawon kwanaki huÉ—u Yah Ahmad na haushi dani akan kawai na tambayesa zuwa duba Yaya Samina, wannan abu nasa ya daÉ—e yana bani mamaki.
A ranar cikon ta huÉ—un ina cikin gyara kayana a drawer sai ga kira ya shigo min, bamma kawo shiÉ—in bane na zata ko Yah Mudan ne.
Ganin sunansa na yawo ɓaro-ɓaro a waya sai mamaki ya kamani, cikin hanzari na ɗaga saboda tana gab da tsinkewa.
A sanyaye nai sallama dan shi yayi shiru da ga can.
Yanda ya amsa da É—an dama sai naji sanyi a raina, na tambayesa ya kasuwa da jama'a?.
“Alhmdllh, ya jikin naki?�.
Da ɗan murmushi a fuskata nace, “Na samu sauƙi ai Yayanmu�.
Daga can Ahmad ya lumshe ido kewarta na cigaba da zungurinsa, cikin sanyin muryar datai kwana biyu bata jiba daga garesa yace, “Yanzu mikikeyi?�.
Daɗine ya kamani, nai murmushin da nakeji a jikina yayi tasiri a garesa, ƙasa na kuma maida muryata nace, “Ina gyaran kayane Yayana�.
Yaɗan sauke numfashi kaɗan daga can, “Sannu da ƙoƙari� ya faɗa a ƙasan maƙoshi.
Tunda nace yauwa sai mukai shiru mu duka, nice na katse shirun da cewa, “Yaya kayi haƙuri dan ALLAH na ɓata maka rai ranar, insha ALLAH bazan sakeba�.
“Ya wuce�.
Ya bani amsa a takaice, daga nan muka sake yin shirun na wasu sakwanni kafin ya kuma kauda shirin namu da cewar, “Ki zaɓa cikin gidajen su Yaya Maryam ina kikeason zuwa?�.
Wani daɗine ya kamani, cikin zumuɗi nace, “Ko gidan Yaya Maryam ɗinma yayi�.
“Ki shirya sai su Salima su rakaki gobe idan ALLAH ya kaimu kimata yini, saura kukai har dare acan�.
“Na gode Yayanmu, insha ALLAH zamu dawo da wuri�.
Yanda ya jiyo tana zumuÉ—i sai tausayinta ya kamashi, amma sai bai nuna mataba yay mata sallama akan idan ya koma gida zai kirata, yanzu yana kasuwa ne, kafin ta bashi amsa ya yanke wayar.
Sosai naita zumuɗin wannan fita, su Salima na zuwa na gumtsa musu bayani, dariya sukaita min, niko ban damuba dan ni kaɗai nasan daɗin da nakeji, tunda akai aurenmu ban taɓa zuwa gidan kowaba a cikin yayyenmu, aiko tun a daren na gama kimtsa hatta kayan da zan saka saboda tsabar zumuɗi.
Da daddaren ma ya kirani, duk da dai sama-sama yanzunma muka gaisa naji daÉ—i, koba komai dai inaji a jikina ya daina fushi dani.
Ƙarfe goma mun gama shiri, ko nace na gama su Fa'iza da suka je gida su faɗa nake jira su dawo mu wuce, sai kallon agogo nake ina zuba tsaki, aiko basu dawoba sai kusan goma da kwata, sunsha harara kamar idona zai faɗo.
Sukaita zubamin dariya, ban kulasu ba muka fito na kulle ɗakin, Mama Ama ce kawai a tsakar gidan, kausar na ɗaki inaga dai jikin nata babu daɗine, ganin takalmin mijinta yasa mukaima maman Ama salama kawai muka fice abinmu, duk da neman zance da take na tambayar “Su amarya yau kuma ina aka nufa?�.
Banko bata amsaba bayan murmushi da cewar “Zan ɗan fitane saimun dawo�.
Muna fitowa su Salima ke faÉ—in, â€Wai ita matarnan bazata canjaba?â€?.
Suma ban basu amsaba, muka tare Napep dai sukai ciniki sannan muka shiga.
Farin cikin da nai na fitar sai muka iske mafiyinsa a wajen Yaya Maryam, gaba É—aya ta gama rikicewa da murnar ganinmu, ta kasa zaune ta kasa tsaye.
Gashi dama ita kaÉ—ai muka iske a gidan kishiyarta wai tayi tafiya zuwa Zamfara biki.
Sosai ranar na tsinci kaina a farin ciki, domin na yini cikin Æ´an uwana munsha zuminci, Yah Ahmad ma ya kira suka gaisa da Yaya Maryam har take masa faÉ—an wannan karon baizo gidanta ba harya koma.
Bansan wace amsa ya bata ba, naga dai ta kalleni tana dariya da faɗin, “Zahiri kuwa ɗan ƙanina�.
Munsha yini cir, sai kusan biyar muka baro gidan, inaji ina gani muka biya ta ƙofar Gidanmu su Salima suka shiga suka ɗakko abu sukazo muka wuce amma ni sai dai kallo, sai da naji hawaye sun cikan idanu, banda aure waye ya isa maka katanga da gidanku? sai lokacin da akaso kaje.
__________________________________
Haka rayuwar taci gaba da shuɗawa, wasu abubuwan na wucewa wasunsu na biyo baya, wataran masu daɗi wataran saɓaninsu.
A wannan yanayin Samina ta koma gidan ma'aruff bayan sun masa shiri na musamman daga wajen malaminsu, tsafi gaskiyar maishi, a cewarsu sunga canji daga Ma'aruff ɗin, dan kuwa da kansa ma yazo ya buƙaci komawar Saminar.
Da farko ta tirje wai ita jan aji saboda taga yana lallaɓata, sai da Inna mari tai mata kaca-kaca akan ta zauna shirme ta lalata komai.
Aiko babu shiri ta dawo hankalinta ranar da yazo da dare ta shirya suka koma.
Tunda ta koma gidan ba'ace babu daɗiba, dan kuwa dai tana samun kulawa fiye da da, sai dai bai fasa shan giyarsa ba balle neman mata, yawan dukantane dai ya bari sai idan ya nemeta ne taƙi saboda warin giyar da bataso shinefa zai lakaɗa mata duka ya kumayi abinda yakeso koda ta ƙarfine, daga ƙarshe kuma yay mata wanka da amai mai uban wari.
Data lura gardamarta ke kawo irin waɗannan matsalolin saita fara sauke rawar kai koda yazo a bugen idan ya nemeta bata hanashi kanta, haka za'ayi tana toshe hanci, babu zancen jin daɗi ko farin ciki daga gareta, kawai ta miƙa kantane ya samu biyan buƙata dan gujema buyaginsa.
Sannan kullum safiya bayan sunyi breakfast sai ya bata ƙwayoyin hana ɗaukar ciki tasha a gabansa yanzu, idan tai gardama tasha mari kuwa, kuma tilas tasha.
Wannan abu na tadama Samina hankali ainun, su da sukeda burin ta haihu dashi amma shi shine yake gudun hakan?.
Ta rasa hanyar da zata ɓullowa al'amuran, tana son faɗama su Nafy tana tsoro saboda gargaɗin da Inna mari tai mata akan riƙe sirrinta ga ƙawaye.
Gefe ga tsangwamar dangin miji, ko wata sabga ake ya kaita gidansu komawa take kamar wata mujiya a cikinsu, babu mai mata kallon arziƙi, to ana harkar masu kuɗi ita talaka ɗiyar talaka wane damar hura hanci gareta?.
Waɗannan matsalolin ne suka tarumata akai ko ƙibar kirki balle murjewar kwanciyar hankali bataiba, ga dai gida iya gida da kayan alatu amma babu wadataccen kwanciyar hankali a cikinsa.
Wani lokaci idan Ma'aruff ya tafka mata wata tsiyar takan ji a ranta da Yah Ahmad ne hakan bazata faruba sam, har kuka takanyi akan hakan duk da bataji a ranta har yanzu ta aikata ma Ahmad É—in ba daidaiba.
★★★★�
Ga Umm-Ruman kuwa tanajin sabbin abubuwa a jikinta, musamman son kaza da jin bata sha'awar kaza, yawan barci da saurin fushi, lokuta da dama shi kansa Yah Ahmad É—in sukan haura sama ta waya, yakanyi mamakinta tunda tun fil azal yasan batada kwaramniya balle akai ga rashin kunya gana gaba.
Tayi wata irin murjewa, fatarta kuwa tai luff har ƙyalli take, sannan tai haske sosai kamar yanda su Maman Ama ke yawan gulmarta yanzu akan wai bilicin takeyi.
Shirmen ƙuruciya baisa Rumana ta fahimci wasu abubuwan da takeyi da sukai canji ko mata nisa a yanzu ba, da abun ya fara tsamari saita koma danganta hakan da wai shawara ke damunta😂.
Wata hikima ta UBANGIJI kuma sai ALLAH ya toshe ji da ganin Kausar da maman Ama akan fahimtar komai daga halin da Rumanan ke ciki.
Koda yake ita dai Kausar ma lafiyace ta mata ƙaranci, to maman Ama ma dai da alama laulayin sabon ciki takeyi, dan yanzu ko zamanma basa yawanyi sai lokaci-lokaci, shima zakiji gaisuwace sama-sama kowa ya samu waje ya kwanta.
Wannan yanayin ne ya kawoma gidan su Rumana yawan shiru, inba su Ahmad da Amatullah ke wasaba, gasu dai matan gidan babu mai ƙarfin yin wani motsi mai girma.
_________________________________