← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 94

Sashe 54

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To su dai su Ahmad ma basusan sunaiba, sunacan suna firarsu cikin nutsuwa da nunama juna zallar aminci ba tare dasun damu da kowaba ko lamarin kowa a gidan, dan in zaka karsu basa faÉ—a maka yanda kowacce take rayuwarta a gidan ba da mijinta.
Suko anbi an saka musu idanu ko wanne motsinsu abin ayi tsogumine.
Tana kwance kanta bisa cinyarsa yana wasa da gashinta, wayarsace a hannunta take kallon hotuna suna firarsu cikin nutsuwa.
Har kusan goma da rabi sannan Ahmad yace su tashi haka nan su kwanta barci yakeji.
Batai musuba ta tashi tai kaye-kaye tayo alwala da brush kamar yanda shima yayo, sanda ta shigo haryayi shirin barci ya haye gado, itama kimtsawa tayi bayan ta kashe fitilar É—akin har Ahmad na mata tambayar lafiya.
Ca tai masa babu komai.
Murmushi kawai yayi yaÉ—an girgiza kansa yana gyara kwanciyarsa.
Sai da ta gama ƙumshe-ƙumshenta sannan ta hawo gadon.
Yau ɗinma dai sun gwangwaje juna da soyayya mai tsayawa a rai, duk da dai Rumana ta yabama aya zaƙinta, dan Yah Ahmad ɗin bana wasan yara bane.
Shi kansa yasan tayi laushi bana wasaba, yau ma wankansu sukai a roba ya fita ya zubda ruwan ita kuma ta goge inda sukaÉ—an É—iÉ—É—isar da ruwan.
Aiko tunda suka kwanta Rumana batai ko juyiba tsabar gurzuwar da tayi, a hakan kuma bayan sunyi sallar asuba ya sake nuna buƙatarsa, babu yanda ta iya dole ta amince kodan gujema fushi.
Aiko harda ƴan ƙwallanta, dan ita kam jarumtarsa tsoroma take bata, inhar haka za'a cigaba dayi lallai akwai jan aiki a gaban mata kenan?.
Da ƙyar Umm-Ruman ta iya tashi bayan sunsha barcinsu kusan goma na safe, haka ta daddage ta miƙe domin haɗa musu abin kari.
Shima tashin yayi, ya zira jallabiya ya fita, babu jimawa sai gashi ya dawo, lokacin tana ƙofar ɗaki ta kunna risho.
Ciki ya wuce, ita kuma ta cigaba da ayyukanta, bayan ta ɗora ruwan cikin ɗakin ta koma, yana kishingiɗe a tabarma dan haka ta samu ta gyara gadon, ta ɗan share ɗakin ta gewayeshi, har tsakar gidan ta share ta wanke bayi, duk wannan hidimar da takeyi kuma Maman Ama bata gidan, tunda Kausar tai nauyin da bata iya zama suyi gulma to bata iya zaman gidan, to dama ita mijinta ƙarfe bakwai yabar gidan, shiyyasa sam bata kallon irin wannan lokacin matsayin safiya.
Rumana dai ta gama haÉ—a kalacinta, ruwan wanka ta sirka taje tayo, sai da ta fito sannan ta haÉ—ama Ahmad.
Koda ta faɗa masa ga ruwan wanka bai musaba ya miƙe yaje dan ya yo, saboda shima a damuwar son tsarkake jikinsa yake.
Kafin ya fito Rumana harta shirya, ta mulke jikinta da ƙamshi.
Koda ya shigo itace ta taimaka masa ya shafa mai kamar yanda ya buƙata, duk da tanajin nauyinsa haka ta daure danta lura bayason yace ai masa abu ake masa gardama.
Itako yanda yake sakewa da ita a yanzu ai bata fatan taga ɓacin ransa sam.
Iya gajeren wando da singlet kawai ya saka ya zauna sukai breakfast, bayan sun kammala yace ta fiddo masa kayan da zaisa, dan Sufyan zaizo suje makaranta ne.
Taji daɗin wannan girmamawa tashi, dan haka ta zaɓo masa kayan da tasan idan yasa suna ƙara masa kwarjini da ƙyau, da taimakonta ya saka hardasu hula, tsaf ya fito asalinsa na bahaushen arewa, ta saka masa turare.
Kuncinta ya sumbata yana miƙa mata agogonsa da faɗin, “Thanks�.
Kanta ta jinjina masa tana É—an murmushi, ta kama hannunsa ta É—aura masa agogon.
Ji take kamar tace ya zauna kawai taita kallonsa......
Ya katse mata tunani da faɗin, “Bara muje inaga ya iso ga kiranshi nata shigowa, sai mun dawo�.
“Tom Adawo lafiya, amma mi za'a dafa?�.
“Komaima ki dafa, Abu zaizo, ki duba a kayan dana cire zaki samu kuɗi saiki bashi yayo cefane�.
Yana gama faÉ—a ya fice, ita kuma ta bisa da addu'ar dawowa lafiya.

Ajiyar zuciya taɗan sauke bayan fitarsa, ta zauna a bakin gadon tana cije baki, wlhy jikinta sai ciwo yake mata, “kai Yah Ahmad babu sauƙi� ta faɗa a fili tana matsa cinyoyinta.
Dole ta sake daurewa ta tashi ta sake kimtsa É—akin da kyau, sai da taga komai ya mata yanda takeso sannan ta samu nutsuwa, barci ne sosai a idonta amma haka ta daure ta zauna jira Abu.
Shima babu jimawa yazo saboda kiransa datai ta waya, kuÉ—in ta É—akko ta bashi kamar yanda Ahmad ya faÉ—a, ta lissafa masa abinda zai sayo.
Da yake aiken na mai hankaline bai jimaba ya dawo, itama ta miƙe batai son jikiba tai abincin.
Dan danan ta kammala ta tsaftace wajen tamkar batai ba, alwalar azhar tayi ta shige ɗaki, har lokacin su Ahmad basu dawoba, aiko tana idan da salla kasa jurewa tai tasa filo ta kwanta a wajen, cikin mintuna ƙalilan barci yay gaba da ita.

__________________________________

Hajiya Samina matan masu hannu da shinu, yanzu kam babu laifi tana É—an samun yanda takeso wajen angon nata, sai dai fa shan giyarsa da É—ura mata maganin hana É—aukar ciki yana nan yanayi bai fasaba, idan tai masa gardama taci dukan banza.
Matsala ɗayace yanzu taso tasota a gaba, wato maganar ƙara aure da mahaifiyar ma'aruff take yawan yi masa, duk da shi dai bai amsa zaiyiba hakan na tada hankalin Samina matuƙar tiƙewa.
Dole ta lallaɓasa akan tanason zuwa gidansu cikin satin nan, dama baifi sau biyu ta taɓa zuwaba a cikin kusan wata huɗu da aure, amma gidan iyayensa kam dukda ana hantararta haka yake sakata taje dole, gidansu kam ya hanata, data ambata zaice mizataje tayo? Bayanma ba wani buƙatar ganinta sukeba ƴan gidan nasu, idan kuma kannenta sukazo yayta fushi yana faɗin shifa bayason wannan shigi da ficin.
Hakan na mata ciwo a rai, amma tana dannewa dan a zauna lafiya.
ALLAH ya dorata a kansa kuwa yau ya barta, amma yace sai ranar talata, batai musuba ta amince tunda dai ai nanda kwana biyune kacal.

___________________________________

Sai bayan la'asar su Ahmad suka dawo, tare da Sufyan suka shigo gidan, amma sai Sufyan ya tsaya a ƙofar ɗaki sai da Ahmad ya fara shiga saboda sunyi sallama basuji Rumana ta amsaba.
Kwance Ahmad ya isketa tana barci, da alama ma ko sallar la'asar batayiba.
Wani É—an tsigunno yayi a gabanta yakai hannu ya shafa fuskarta, jikinta da É—an zafi kaÉ—an, bai kawo komai a ransaba game da É—umin jikin nata, ganinsa kawai dan tana a cikin É—akine.
A hankali ya fara kiran sunanta yana cigaba da shafa fuskarta, “Umm-Ruman;�
A hankali ta buɗe idanunta a kansa, ganinsa tsugunne a gabanta ya sakata sake buɗe idanun nata sosai tana kallonsa, murya a sanyaye tace, “Yaya kun dawo?�.
Kansa ya ɗaga mata, ya miƙa mata hannunsa ta kama ya taimaka mata ta tashi.
“Koma salla bakiyiba halan?�.
“Eh wlhy Yaya banma san anyiba, banyi zaton barcin nawa zaiyi nauyi hakaba�.
Hijjab ɗin daya ɗakko yake ƙoƙarin saka mata, “Ai gara da kikayi ƙyaji daɗi, tare muke da Sufyan�.
Tayashi saka hijjab ɗin tai tana faɗin, “Yana ina to?�.
“Gashi a ƙofar ɗaki, munyi sallama ne baki amsaba shiyyasa ya jira na shigo naga lafiya?�.
“ALLAH sarki, kuyi haƙuri banjiba wlhy, ya shigo to�.
Izinin shigowa Ahmad ya bama Sufyan, ya É—aga labulen ya shigo sallama É—auke a bakinsa.
Rumana tai masa barka da zuwa ya amsa yana zama da tsokanarta.
Fuskarta ɗauke da murmushi ta ɗauki tiren data shiryama Ahmad abinci takai gabansu tana gaida Sufyan ɗin, koda suka gaisa saitai yunƙuri durƙusawa zata zuba musu abincin.
Ahmad dake latsa waya yana saurarensu ya ɗago ido ya kalleta, a hankali ya furta, “Jeki abunki zamu zuba�.
Yanda fuskarsa babu walwala yasa bata musaba tama fita domin yin alwala.
Lokacin data shigo harsun fara cin abinci, sallarta ita dai ta kabbara, koda ta idar saita fita tabarsu sunacin abincin suna hirarsu.
Koda suka kammala ma tare suka sake ficewa daga gidan Sufyan nata mata santi, ita dai murmushi kawai takeyi kanta a ƙasa har saida suka fice.
Ta tattare kwanikan ta fita dasu danta wanke, tana wanke-wanken suna ƴar fira da Kausar data fito take shan iska a ƙofar ɗakinta, Maman Ama dai bata gidan tana gidan maman Aysha.
A haka tazo ta samesu, kawai sai gani sukai ta ɓata fuska, ko zato take gulmarta sukeyi? Bata san su firar tasuma akan haihuwar Kausar ɗin bace..
Tunda Rumana taga yanda tayi saita miƙe abinta dama ta gama wanke-wanken ta koma ɗaki kawai.

★★★★★★

Yauma anayin sallar isha'i Ahmad ya shigo gidan, ledar daya sayo musu kayan fruits ta amsa tana masa sannu da zuwa, kwalliyar datai yakebi da kallo dan ta mata ƙyau, itama ta lura da kallon da yake mata tun shigowarsa.
Ta katsesa da faɗin, “Yaya a haɗa ruwan wanka?�.
A taƙaice yace, “Uhm�.
Sai da takai masa har banɗaki sannan ta dawo ta sanar masa, ya miƙe ya cire kayansa ya saka jallabiya ya fita.
Kafin ya dawo ta saka fruits É—in a filet mai É—an girma, tana fiddo masa kayan da zaisa ya shigo.
Da taimakonta ya shirya dukda dai ita takasa sakewa dashi yanda ya kamata har yanzu, sosai takejin nauyinsa, abinda yasa take daurewa saboda ta lura yana son tattali, nuna kulawarta a garesa sosai ke sakashi sakin mata fuska tana ganin fara'arsa, a ganinta ta wannan hanyarne zata cusa masa sonta a rai koda bata samu kwatankwacin abinda Samina ta samuba na soyayyarsa, itama ta samu wani yanki a ciki.
Sai dai abinda Rumana bata saniba shine tuni tayi mamayar da Samina batai koda kwatankwacinta ba a zuciyar gwarzon nata, kawai dai bai furta baneba.
Chapter 54 · 0% Book details