Sashe 87
Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
..............Æangaren Ma'aruff abubuwa sam babu daÉ—i tsakaninsa da Mufida, dan tun bayan barin Samina gidan suka dawo gida zaman lafiya ya gagara a tsakaninsu saboda videos É—in da aka fidda na abinda ya faru tsakaninsa da Samina.
Asiri yana ɗawainiya da Ma'aruff sosai, hakan yasa yake masifar tsoron Mufida, a lokacin taso ƙwarai da gaske su rabu, sai dai iyayenta suka tsawatar mata saboda akwai wata manufa a ran mahaifinta, duk da mahaifinta ƙanin maman Ma'aruff ne bashi da wani buri da ya wuce ya mallake company ɗin su Ma'aruff ɗin, bayan rasuwar mahaifin su Ma'aruff yaso ya tattare dukiyar yaran ya riƙe a hannunsa akan shi ne zai kula musu tunda dai mahaifiyarsu macece.
Amma sai sam taƙi aminta da hakan, dan gudun kar a salwantar da dukiyar marayu, a lokacin shi ma'aruff yana Germany yana karatu, ya kammala degree ɗinsa na biyu zai tafi na uku ne ta matsa masa akan ya dawo gida dole, yabar karatun wanda yayi ya wadatar.
Badan Ma'aruff yasoba ya dawo Najeriya, daga nan ta danƙa masa dukiyar a hannunsa, shi kuma sai ya gyara company mahaifin nasu na yin takalma kawai aka cigaba da harka.
Wannan al'amari yayima mahaifin mufida ciwo a rai, amma sai ya danne, kullum dai yana neman hanyar da zai mallaki dukiyar har zuwa yanzun, bayan auren Samina da Ma'aruff ya fahimci ƴar uwarsa bata ƙaunar matar ɗansa, dan haka yayta sake tunzurata a ƙiyayyar Samina, yana cusa mata son haɗa zuminci tsakanin ɗiyarsa da Ma'aruff.
Tun abin bai tasiri ga maman su Ma'aruff ba har taji ta aminta saboda basu barsu hakaba, dan bin bokaye wajen maman mufida lamarin sai dai gyaran UBANGIJI, hatta da videos ɗinnan ƙanin Mufida ya sakesune da gayya saboda Samina ta barma ƴar uwarsa gidan, tunda shima yasan dukiyar Ma'aruff mahaifinsu ke ƙulafuci, idan kuma an samu shine zai mora tunda shine namiji babba a gidansu.
Rikicin dake yawan faruwa tsakanin Ma'aruff da Mufida ne ya nema fara susutar dashi, dan sai shan giyarsa ta ƙaru fiye da da, da yake ALLAH ba azzalumin sarki bane sai kuma ya koma begen Samina, da yasha yay ɗaɗil sai yayita ambatar sunanta a cikin shirmen surutansa na maye.
Maman Ma'aruff sam batasan mike faruwa ba, tana can ta saki baki akan tunda Ma'aruff ya rabu da Samina maƙiyiyarsu shikenan ya samu salama a rayuwarsa kenan, yanzu zasuyi zama na arziƙi da ƴar uwarsa.
Sai dai hankalinta ya fara tashine ganin kusan sati uku Ma'aruff bai zo inda takeba, al'halin baya iya kwana uku baizo gidanba.
A lokacin ta danne abin a ranta da tunanin ko ruÉ—anin tsiyar da Samina ta tafka musune bai sakesuba, tare da videos É—in dake yawo yakema kunyar zuwa gidan.
Kwanaki sun sake shuɗawa, har kusan sati na shidda babu Ma'aruff babu dalilinsa, ranar wata asabar sai gashi yaje gidan, hankalinta yay masifar tashi da yanda ta gansa, dan ya rame sosai yayi baƙi.
Zaunar dashi tai tana jera masa tambaya akan mike damunsa?, amma sam ya kasa faɗi mata komai, ganin bazai sanar mataba sai ta haƙura, dan a tunaninta dai wancan abunne ke damunsa har yanzun.
A ranar ya wunine anan gidan, ba komai ya kawosaba kuma sai umarnin Mufida akan yazo ya É—auka mata takardun company É—insu, to amma da yazo ya rasa hanyar da zaibi ya É—auka, dan suna É—akin mamansune, shikuma ba shiga É—akin yakeba sai da dalili.
Har dare bai samu yanda yake soba, maman kuma ta sakashi ya tafi gida dole harda bada abu a kaima Afrah, tunda ita batasan dawan garinba.
Tunda ya shigo gidan Mufida taga babu takardun ta hausa da masifa kamar uwarsa, yay shiru kawai yana kallonta, daga ƙarshe ya koma bata haƙuri, amma taƙi koda saurarensa, ganin abin zaiyi yawa sai yay ɗan irin buɗe mata wuta ɗinnan wai ko zataji shakkarsa ta saurara masa, dan duk tsiya da zagin da take masa maigadi na jiyosu.
Aiko sai saukar mari yaji a fuskarsa, ya dafe kunci yana kallonta da ɗunbin mamaki, “Mufida ni kika mara?�.
“An mareka, ko zaka ramane?! Wawa da kai lusari, kana abu tamkar ba namijiba, ɗakko takardu su gagareka a cikin gidanku......�
Raɓata yay ya wuce bai iya sake magana ba, ransa a ɓace ya shige sashen da Samina ta zauna, dukda har ya fara ƙura haka ya faɗa cikin kujera ransa na masa zafi, bai san miyasaba idan yana gaban Mufida bai iya komai a rayuwarsa, sai yabar inda takene zai dingajin ciwon abinda take masa, ya kai dubansa ga kwalaben giyar da ya baza a falon na Samina kaca-kaca, cikin rawar jiki ya miƙe, inda ya ajiye kwalayen giyar kusan biyar ya nufa, ya ɗakko biyu ya dawo ya zauna, ransa na masa zafi ya ɓalle ya hau kwankwaɗa.
Sai da ya jisa mankas sannan ya zube a wajen yana surutai da zagin Mufida tare da begen Samina.
★★★★★★�
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya abubuwa nata sake tsauri tsakanin Ma'aruff da Mufida, kullum tana aikashi ya É—akko mata takardun Company ALLAH bai bashi ikon É—akkowaba.
Yanda take matsa masa akan waÉ—annan takardu haka mahaifinta ke matsa mata itama.
Abu kamar wasa watanni suka shuɗe shekara ɗaya ta kusan haɗuwa, zuwa lokacin hankalin momin su Ma'aruff yakai ƙololuwar tashi da canjawar Ma'aruff ɗin, dan takai hatta da aiki yanzu Ma'aruff sai ya gadama yake zuwa, al'amuran Company sun fara taɓarɓarewa.
Ranar dai tai shiri da kanta tazo gidan, a lokacin Ma'aruff na sashen Samina yayi mankas da giya, da wannan damar Mufida tai amfani ta ƙalama Ma'aruff sherin wajen mahaifiyarsa, ta nuna dai duk wannan abu da yakeyi akan Samina na ne, nan take Mamansa tace ai asiri iyayen Samina sukaima Ma'aruff.
Aiko ta kira mahaifin Mufida ta sanar masa, koda yazo gidan shima sai ya nuna shiga tashin hankali kamar gaske, ya kuma zugata akan suje su saka Æ´an sanda su kama iyayen Samina.
Babu musu ta yarda da wannan shawara, sukaje kuwa police station suka kai report, Æ´an sanda sunji kuÉ—aÉ—e babu wani bincike suka nufi gidansu Ahmad, sai dai koda sukaje an sami akasi, dan a ranar su baba duk basa nan, suda matan gidan duk suna Shema wajen biki, su Mudan ne kawai a gida.
Koda Æ´an sanda suka sanarma Mudan dake shago yana É—inki abinda ya kawosu tsabar iya shegensa sai ya turasu gidan inna mari akan cewar ai iyayen Saminar yanzu sunbar gidan sun koma can.
Ƴan sanda babu man kai suka yarda😂, suka kuwa kwashi ƙafafunsu sai gidan Inna mari bisa kwatancen da Mudan yay musu.
Koda suka isa gidan Maman Ma'aruff taci karo da Inna mari bayan sunyi sallama ta fito dan taga wanene sai cewa tai “Yauwa yallaɓai ga kakarta nan, ku haɗa da ita�.
Inna mari na tambayar ba'asi aka cukuykuyeta zuwa cikin motar ƴan sanda, sannan suka kutsa kai suka tattaro Mama gaje dake tsakar gida zaune zataci abinci, iya kuwa ta fita sayo waken ƙosanta na gobe.
Itama dai kwasarta sukai sai cikin mota, duk da roƙon da take musu da tambaya sunƙi saurarenta.
Babu tausayi babu imani mahaifin Mufida yasa aka jibgi su Inna mari duk da tsufanta, sai da sukai musu lilis sannan suka barsu.
Iya na dawowa ƴan anguwa suka sanar mata abinda ya faru, nan take ta rikice tahau kuka, ta saka aka kira mata ƴarta a waya ta sanar mata komai, hankalinta tashe tazo gidan ita da mijinta, haka suka bazama neman station ɗin da aka kai su mama gaje tare da ƙanin mama gajen shima isa, amma basu samuba har dare, dole suka dawo gida.
Washe garima haka sun fita bin stations suna tambaya, amma duk inda sukaje sai ace ba nanbane, har inda aka kai su inna mari sunje amma ance ba nan bane, a kwana na huɗu sukaga abin yafi ƙarfinsu sukaje suka faɗa gidansu Ahmad.
Shi Mudan ma ya manta da anyi abun, dan bai sanarma kowaba, koda suka dawo daga Shema, sai randa su Iya sukazo.
Kai tsaye Baba Yusha'u yace shikam babu ruwansa, dan baida alaƙa dasu yanzu kam.
Baba Hamza ne ya tsawatar masa akan wannan furuci, ta ya zaice baida alaƙa da mama gaje bayan gasu binta, dole Baba Yusha'u yay shiru.
ALLAH sarki Baba Hamza, haka ya tasa ƙeyar Madan gaba akan suje su bincika suma, su Iya kuma suje gida su huta, amma sai sukace karya damu suje taren kawai.
Da farko Mudan yaso yin yawo da hankalinsu, to amma da ya tuna dashi za'asha wahalar, ga kuma dinkuna jibge a shago suna jiransa ga zuwa makaranta sai kai tsaye ya rakasu station ɗin da yake da tabbacin su Mama gaje nacan, amma a zuwan dai bashi da tabbas dan kar baba yaci ƙaniyarsa.
Suna isa kuwa suka iske maman Ma'aruff a wajen.
Su baba sunsha wahala kafin a basu su inna Mari, dan sai da ya saka Mudan ya kira Ahmad a waya suka haÉ—ashi da d.p.o din wajen, baisan mi Ahmad É—in ya faÉ—a ma d.p.o É—inba ya yarda, kuma da yake shi baba tare sukazo a wancan lokacin da aka rufe Samina akan faÉ—ansu da Basy sai d.p.o É—in ya sake aminta da maganar da sukai da Ahmad, nan take ya bada belin su Mama gaje.
Hankalin su Baba ya tashi ganin yanda aka fiddo su Inna mari, jiyay ƙwalla sun cika masa idanu, harya kasa haƙuri sai dai yayma dpo ɗin ƙorafin irin wannan duka da sukaima mata haka, matanma tsoffi kamar waɗannan, musamman ma Inna Mari.
Dpo yayta bama Baba haƙuri akan wlhy shi bayanan komai ya faru, hasalima baisan halin da su Inna Mari sukeba sai yanzu, yay taima ƴansandan da sukai abin faɗa tamkar zai cinyesu ɗanyu.
Su dai su baba sun kwashi su mama gaje zuwa asibiti kamar yanda Mudan ya bada shawara, dan tausayi suka koma bashi, harma yay dana sanin bai tura Æ´an sandan can gidanba.