← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 94

Sashe 31

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahmad kam tunda suka ɗauki hanya ya jingina kansa da kujera yay shiru yana tunanin rayuwa da abinda ya zamo masa sanadin barowa gida, wani sa'in idan ya tuna rayuwar da sukai da Samina a baya sai yaji kamar zai yarda da maganar wasu mutane dakan ce asiri akai mata, sai dai wani sashe na zuciyarsa na saurin ƙaryata wannan magana, sai ya bijiro masa da ainahin gaskiya aka lamarin Samina ta gujesa ne kawai saboda burin banza da wofi da son duniya, wanda a wannan zamanin mafi yawan ƴammata shine yake ruɗarsu ya halakasu, wasu zaka samu da taimakon iyayensu, wasuko sun zubda tarbiyyar iyayen ne sun ɗauki ta ƙawaye ko samari, san zuciyane kawai kesa a zagi ilimin boko, amma wlhy bashi da alaƙa da lalacewar yaranmu, lalacewar kawai tafi yawa daga zuciya ko tarbiyya da dai sauransu.
Yayi zurfi a tunaninsa sosai, har sukai tafiya mai nisan zango dashi kansa baisan adadinta ba, sai da na kusa da shine ya taɓasa lokacin da suka iso wani gari aka tsaya domin yin salla sannan ya dawo hankalinsa.
Bayan salla suka sai abinci kamar yanda yaga abokan tafiyarsa nayi, dan duk inda ya saka ƙafa tarene suke da makwafcinsa da suka zauna kusa da juna.
Bayan sun dawo kuma sai ƴar fira ta fara shiga tsakaninsa da abokin zaman nasa, wanda yace shi sunansa Nura, shima dai neman arziƙi ya kaisa rayuwar garin porthercout.
Tun Ahmad bai sake masaba dai harya saki jikinsa kular da yay kamar Nuran baida yawan hayaniya, ahaka har suka isa garinna port gabannin asubahi.
Dole Ahmad yabi Nura masaukinsa da safe kamar yanda ya buƙata, dan kuwa inma yaƙi dai bashi da wajen zuwa, tunda ba kowa ya saniba balle yace zai nemeshi.
Masaukin na nura dai bawani waje bane face gidan biredi, inda sukan maƙala ƴan kayansu su wuce wajen sana'a, idan sun dawo su yada zango a ƙofar wani shago da ire-irensa su rage dare, zuwa ƙarfe goma su nufi gidan biredi su kwanta, asubar fari kuma za'a tashesu saboda za'a fara aiki.
Sana'ar kuma Nura Shu-shaina ce, dan haka koda Nura yayma Ahmad bayani sai bai jayayya ba yace shima zaiyi, tunda bada wani jari yazo ba balle yace, dama iya kuÉ—in motane, sai kuÉ—in da suka rage masa a aljihu naira dubu É—aya da É—ari bakwai.
Da waÉ—annan kuÉ—inne Nura ya rakashi ya sayi Æ´an abubuwan bukata da zai fara wannan sana'a, a ranar babu hutu suka fara zagayawa kuwa.
Ahmad yasha matuƙar wahala, duk da ya saba da wahalhalun talla ba irin wannan baneba, saboda banbancin gari da jama'ar garin, sauƙinsa ɗayama yayi karatu, shine ya taimakesa wajen furta magana da mutane, dan inhar kaji hausa to sai dai idan suna tare da bahaushene waɗanda suka kasance ƙalilan a garin kuma.
Sai yamma lis suka dawo yanata yaƙe, ga ƙafafunsa sai ciwo suke, harya yi aniyar cema Nura shi dai bazai iyaba, sai kuma wani tunani yazo masa a rai, idanma yace bazaiyiba to yanada jarin yin wata sana'arne bayan wannan? Wannan tunanin shine ya danne dukkan yunƙurinsa ya sama zuciyarsa haƙuri.
Hankalinsa bai kuma tashiba sai da sukazo kwanciya, yaga kowa na ƙokarin jera kwalin da zai kwanta, ƙwalla ne suka cika masa idanu, dukda kasancewarsu talakawa ko kwanan tabarma bayi yakeba sai ta kama, ko yaya dai sunada ƴar katifar barcinsu.
Shi aranarma sun manta basu sayo masa kwalinba, sai na Nura suka gitta suka kwanta iya ƙirjinsu kawai wai dansuji ɗan taushi, ƙafafu kuma na saman suminti, Ahmad da ya saba rufa zai iya barci sai gashi yau babu abin rufar, aiko duk yanda yaso yin barci kasawa yayi, ta ko ina babu daɗi, zuciya sai tuna masa matarsa da iyayensa harma da Samina take.
ƙarfe uku da rabi aka tashesu, har lokacin kuma Ahmad bai rintsaba, haka suka fito kamar awaki, kowa yaɗan samu waje a waje ya maƙale dan ya ƙarasa daren, wasuko basu kwantaba suka hau hidimar shirin fita kasuwa sai kace fataken dare.
Wannan ƴar kwanciya dasu Ahmad suka samu ƙofar wani shago ce ta jawo masa barci yaɗan figesa, sai da Nura ya tashesa da asuba da ƙyar.

Gaba É—aya komai ya rikiÉ—ema Ahmad, dukya fita hayyacinsa tamkar ma wanda baisan A ba, gaba É—aya ya rikiÉ—e matsayin É—an ciraninsa, kwanansa huÉ—u sannan ya samu damar kiran Æ´an gida a waya.
Yaci faɗa wajen baba saboda ƙin kira ya sanar ya sauka da baiyiba, sai da yayta bama baba haƙuri sannan ya sakko.
An bashi ya gaisa da kowa, harda Mudanseer, yace masa yaje da dare ya kaima Rumana waya su gaisa.
Aiko kamar yanda ya buƙata da daddare ya kaima Umm-Ruman waya, lokacin su Fa'iza masu tayata kwana suna gidan. Gaisuwa kawai sukai ya tambayata babu dai wata matsala ko? kuma ta daina kukan?.
Ta faÉ—a masa eh tana haÉ—iye kukanta.
Daga haka bai ƙaraba yay mata sallama, itako ta mikama Mudanseer wayar.
Tun daga ranar bai sake neman Rumana ba, sai dai duk kwana biyu yakan gaisa da baba, idan yaga kuÉ—in zasu isa a haÉ—ashi dasu Ayyah, idan bazasu isaba shikenan yace baba ya gaishesu kawai.
Tun Ahmad na jigata harya saba da sanar tasu, ya dake zuciyarsa sosai, komai ya zame masa jiki.
Kafin wani nisan zango sai ga wata ɗaya ta shuɗe babu labarin Ahmad balle dawowarsa, da yake yakanyi waya da Madan ya sanar masa ƴan kuɗin ɗinki da ake samu suna riƙesu har Rumana sai hankalinsa yakan ɗan kwanta, amma ya turama Mudanseer kuɗi sau biyu duk da basu da yawa kuwa.
Baba ya fara magana akan zuwansa gida, hakan ya saka Ahmad shiga damuwa, dan shidai alokacin baima fara fahimtar komaiba game da abinda ya fito nema balle kuma ace yaje gida, ko kuÉ—in mota kawai sun isa gayya.
A haka wata ɗaya ya kuma shigewa suka zama biyu, dukda takurawar baba yanata jansa da ban haƙuri shidai tare da wasu dabaru.
Wannan sabuwar rayuwarce ta fara saka zuciyar Ahmad mantawa da wata Samina, dan shi kansa yakan manta da kansa balle ita, ibadar ALLAH da sana'arsa ce kawai damuwarsa, sai ƴan uwasa da basa barin zuciyarsa a koda yaushe, Umm-Rumana ma takan faɗo masa arai lokaci-lokaci, musamman ranar dazai taho da taita kuka ta kasa barin ransa, sai kuma randa tai targaɗe a ƙafarta tayi masa kukan taɓara.
Yakanyi murmushi idan hakan yazo masa a rai kuwa.
A hakane kuma suka samu aikin gadi shi da abokinsa Nura, babu musu suka amsa, dan kuwa mai wajen da zasuma gadin yay musu alƙawarin biyansu kuɗi masu ɗan tazara, dan duk wata dubu talatin su biyu su raba.
Ahmad yay murna, dan tun zuwansu bai tara kamar waÉ—annan kuÉ—inba.
Da rana zasuyi yawon tallarsu, da dare kuma suzo su kwana yin gadi a wajen.

_________________________

Ɓangaren Samina kuwa yanzu abubuwa sunyi nisa tsakaninta da Ma'aruff, kamar yanda mama gaje take buƙata Ma'aruff na kashema Samina kuɗi tamkar baisan ciwonsu ba, amma kuma yana lalubeta kullu yaumin a mota, yanzuma abin yakai har gidan gonar nan yake kaita susha masha'arsu.
A sheɗanci kuwa shigartane kawai bai taɓa yiba, amma duk wani ƙazamin romance Ma'aruff yanayi da Samina, idan ta dawo gida kuwa ko ranar abubuwa sukai masa yawa bai zoba to ka'idane zata shiga bayi taita ɗauka masa hoton kanta tsirara tana tura masa, har video sakata yake yana faɗa mata abinda zatayi, koya kirata video call ahaka zasu gamsar da junansu😭.

Sanda taji Ahmad yayi tafiya tsakima tayi, acewarta sun rage ƴan saka idon anguwa masu zuwa lahira da ƙoƙwan dambu, waɗanda talauci ya zautar da kwakwalwarsu basa fahimtar komai sai saka ido ga abinda bai shafesuba.
Maimakon Mama gaje ta kwaɓeta saima ta kama dariya kamar wata zautacciya.
Kullum kuma cikin yima Ammin Rumana shaguɓe ake akan ɗawainiyar da Ma'aruff kema Samina.
Sam idon mama gaje ya rufe takasa fahimtar Æ´arta na cikin wani hali, abinda kawai tasani Æ´arta tana fitane zuwa makaranta, idan kuma Ma'aruff ya fita da ita to sunje ya mata sayayyane kawai.
Bata taɓa tunanin bincikar wayar Samina ba, musamman yanda Saminar bata barin kowa ya taɓa mata waya har ita mama gajen kuwa, ƙannenta ko dasun taɓa ne zata mammakesu ta amshe kayanta, maimakon mama gaje ta fara tunanin akwai abinda Saminar ke ɓoyewa a waya amma sai tayi biris da hakan.
Ita dai kawai da an kawo mata kuÉ—i da kayan makulashe da zannuwa masu tsada shikenan.
Iyayen Saminar maza da kakanninta kuwa taje ta dafko musu asirin daya rufe bakin kowa a gidan babu mai ma Samina faÉ—a akan komai, sai idanu da suka zuba mata duk da abinda take yana cin zukatansu kuwa.
Dan wataran baba yusha'u har kuka yi yakeyi akan halin da Samina ta jefa kanta sanadin son zuciya..

Kowa yasan zuwa yanzu idanun Samina sun ƙara buɗewa, ta fetsare sosai, dama karatun islamiyya kam ta ajiyesa gefe, na bokonma da take fakewa dashi yanzu bayi takeba, tunda da taje Ma'aruff ke zuwa ɗaukanta, wani lokacinma ko cikin makarantar bata shiga, kai tsaye gareshi take tafiya, abun yakai har Company dinsu Ma'aruff Samina zuwa take Office ɗinsa susha sha'aninsu.
Gaba ɗaya ta manta da wani halitta Ahmad balle rayuwarsu ta baya da ƙoƙarin gina rayuwarta da yayi, gaba ɗaya ita a dole yanzu ta zama babbar yarinya, budurwar babban yaro da ya fi mijin novels komai.
Abinda yasa Samina taƙi yarda ta bama Ma'aruff kanta 100% saboda tana tuna yanda marubuta kansa amarya tasha gata wajen minjinta a daren farko saboda budurcinta daya samu, amma yanda yasha kawo farmakin amsa da tuni ta bashi.
To tanason dai itama taga wannan gatan shiyyasa.

_________________________
Chapter 31 · 0% Book details