← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 94

Sashe 38

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Lallai Umm-Rumana taga daren alkairi na haƙiƙa, dan Ahmad baije da wasaba, sosai ya nuna gwarzantakarsa a zahiri ba tareda tunawa da wadda yake a filin dagarba, gashi ya hanata dukkan damar da zatai kukan da wani zaiji, dukda ma ruwan da ake zubawar kuwa bazai bar wani jin nata ba.
HaÉ—iyar zuciya kawai take a jikinsa dan zuwa yanzu kukanma ya gagara zuwa da hawaye, shi kansa yayi laushin da ko hannu ya kasa É—agawa domin lallashinta, ya dai turata jikinsane tamkar zai maidata ciki, idonsa na zubarda hawayen da shi kansa baisan dalilinsu ba, kawai saukarsu yakeji akan kumatunsa.
A haka wahalallen barci ya sace Umm-Ruman dake ta sauke tagwayen ajiyar zuciya har lokacin, yaja kusan awa ɗaya bai iya taɓukama kansa abun ƙwarai ba balle ita da yakejin illahirin jikinta ya ɗauki zafin zazzaɓi, haka ya daure ya janyeta a jikinsa tare da bargon ya sakko daga gadon yana layi na rashin ƙwarin jiki saboda faruwar sabon al'amari da gaɓɓansa basu taɓa fuskantaba a rayuwarsa.
Ya ɗauki filas ɗin shayinsu kozai samu ruwan zafi, sai dai wayam, dan ɗazun dashi Rumana tai masa amfani, tsaye yay yana nazarin mafita, dan kuwa dai ya zame masa tilas taimakama Rumana tun a daran kodan yanayin gidan da suke ciki, basai da asuba yace zaita faɗi tashiba ana ƙare musu kallon ƙurilla.
Dole ya ɗauki shawarar zuciyarsa ta ƙarshe ya kunna risho ya saka ruwa a tukunya ya ɗora.
Babbar roban Rumanan daba fitama take da itaba sai zatai wanki ya É—auka ya ajiye a tsakar É—akin, sai da ruwan yay zafine sannan ya juyesa ya sake É—ora wani ya nufi gadon.
Har yanzu ajiyar zuciya kawai Rumana ke saukewa cikin wahalallen barcin daya ɗauketa, ya janye bargon da take ciki yana ƙoƙarin ɗagota, amma koda ta buɗe ido saita fashe masa da kuka saboda azabar da illahirin jikinta ke mata.
Yatsansa ya ɗora saman bakinta yana faɗin, “Shiiii� dole tai shirun kuwa tana haɗiye kukan da ƙyar.
Sosai yay mata gashin datasha kuka kuma taji daÉ—insa, sannan ya nuna mata yanda zatai wankan tsarki dukda bashida haufi akan ta iya tunda suna zuwa islamiyya.
Kafin ta kammala ya koma gaban gadon ya kunna fitilar wayarsa ya haska zanin gadon, bawani ɓaci yay sosaiba, amma dukda haka yasan za'a iya ganewa, dan haka ya yayesa gaba ɗaya, dirowarsu ya buɗe ya ciro ɗayan da dama guda biyune kacal zanin gadon, ɗaya mai tsada ɗaya mai ƙaramin kuɗi, shiya shinfiɗa, dai-dai Rumana daketa hawaye ta kammala tsarkale jikinta, da kansa yazo ya taimaka mata ta fito a roba, sai faman kare ƙirjinta take da hannu wai karya gani😜.
Ya maida mata rigarta yana zaunar da ita saman gadon, sai mutsu-mutsu take saboda zafin da takeji zaman neman gagararta yakeyi, lura da hakan da Ahmad yayine ya sakashi faɗin, “Sorry�.
Banza tai masa, shiko ya dubo paracetamol a kayansa yazo ya zauna gefenta riƙe da kofin ruwan daya ɗebo ya bata, dayake bata da matsala da shan maganin saita amsa tasha, ya taimaka mata ta kwanta ya lulluɓeta.
Shima tsaftace jikinsa yayi a ɗakin, ya buɗe ɗakin ya watsa ruwan dan har lokacin ruwa ake makawa sosai, goge duk inda suka jiƙa yay tsaf, ya maida komai inda ya ɗakko sannan yasaka abin salla yay nafila raka'a biyu yana miƙama UBANGIJI sinƙi-sinƙin godiya, ya daɗe yana zubama ALLAH kirari da doguwar addu'a ga Rumana harma da iyayensu da suka kasance sanadin komai.
Kafin shima yasha paracetamol ɗin daƙyar dan wani zazzaɓine ke neman rufesa shima ɗin, cikin barci Umm-Rumana tajisa cikin jikinta dake zafi zau da zazzaɓi, da yake shima nasan ya ɗau zafi sai baiji natanba sosai, haka ya kuma maƙalƙaleta yana gyara musu bargo............✍�

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏼*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo

*_GDW_*

*(22)*

...............Da asuba Ahmad ne ya fara farkawa, ya buɗe idanunsa da ƙyar saboda nauyin da sukai masa na rashin samun isashshen barci, Umm-Ruman na kanannaɗe a jikinsa, sai dai su duka zazzaɓin ya sauka.
Wayarsa ya lalubo ƙasan filo ya kunna fitilar, gaba ɗaya ɗakin ya gauraye da haske, ya shafa kan Rumana dake lafe saman ƙirjinsa a hankali, komai na daren jiyane ya shiga dawo masa, ya sauke sassanyan numfashi yana faɗin, “ALLAH yay miki Albarka� akan laɓɓansa.
Cikin rashin son ya tasheta ya ƙoƙarin zameta daga jikinsa, tako sake riƙeshi dan sanyin da takeji bataso ta rabu da koma miye ta maƙalƙale.
Murmushi ya sauke a hankali tareda busa mata hucinsa cikin kunne, É—an sautin hucinne ya sakata motsawa kaÉ—a.
Ganinfa da gaske ba tashin zatai ba sai ya kai bakinsa saman kunnenta ya fara magana, “Ruman kibar Yayanki ya tashi lokacin salla yayi�.
Sarai Umm-Ruman taji maganar Ahmad cikin kunnenta, dan tunda ya kunna fitila ta farka, amma kunya ta hanata koda motsin da zai gane.
Sake shige masa jiki tai tana faɗin, “Uhm-uhm�.
“Uhm-uhm ko? to ai nasan maganink......�
Kafin yakai ƙarshe tai azamar raba jikinta da nashi, ta matsa baya tana juya masa baya.
Sosai abin ya bashi dariya, dan haka yay murmushin da har take jiyo sautinsa.
Bargon ya yaye yana zura ƙafarsa ƙasa da faɗin, “Matsoraciya da ki tsaya mana�.
Ita dai batako motsaba harya buÉ—e É—akin ya fita bayan ya zira doguwar riga.
Har lokacin ana É—an yayyafi, shiyyasa Ahmad da yayo alwalan sai ya dawo É—aki.
“Wai bazaki tashiba?� yay maganar idonsa akan Umm-Ruman da har yanzu take naɗe akan gadon, ita duk wayonta sai ya tafi salla zata tashi, amma jin ya dawo ɗakin ya bata tabbacin anan zaiyi shima.
Tashi tai da ƙyar, dan har yanzu gaɓɓanta ba daina mata ciwo sukaiba, ga ɗan zafi har yanzu tanaji, bata yarda tama kalli sashen da yakeba koda wasa, shiko yana tsaye saibin ta da kallo yake sabida ganin yanda take tafiya da ɗan ɗingishi, duk da ya lura da ɗunbin jarumtar da takeson nunawa dan ganin tafiyar ta tafi dai-dai.
Sai da ta ficene ya sauke ajiyar zuciya yana lumshe idanunsa da buÉ—ewa lokaci É—aya.

Cikin dauriya da ƙarfafa kanta take taku saboda ruwan da akasha, danma tsakar gidan nasu duk sumintine, alwala itama tayi bayan ta shiga bayi ta fito.
Lokacin data dawo ɗakin yana zaune yana jiranta, miƙewa yay idonsa a kanta, itako taƙi yarda yanzun ma ta kalli ko sashen da yake, baice da ita komaiba harta kimtsa tazo inda yake tunda taga alamar jiranta yake ya jasu sallar.
Hakan kuwa akai ya jasu suka sallaci asubahi, bayan sun idar yaja dogayen addu'oi a garesu da al'ummar musulmi baki É—aya.
Koda suka shafa Rumana na zaune a bayansa batako motsaba, kanta dai a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.
Zamansa ya gyara ya jingina da jikin hado yana mai fuskantarta, sai dai baice komaiba kallonta kawai yake tamkar ya samu tv.
Ai sai jikin mutuniyar taku ya nemi fara tsuma, cikin salƙewar halshe ta fara gaishesa,
“Uhm u..hm Yaya ina kwana, ya gajiyar tafiya?�.
Guntun murmushi yayi yana ɗora dukkan hannayensa saman gadon cikin miƙar dasu, har sannan kuma idon nasa a kanta yake.
“Lafiya lau Amaryar Ahmad, ya ƙoƙari?�.
Shiru tai dan bata fahimci ƙoƙarin mi tayi ba.
Ya sauke hannayensa tare da kai na damar ya ɗago haɓarta, “Kalleni nan� yay maganar babu wasa.
Dolenta ta É—ago idanunta a hankali ta saka cikin nasa daya kafeta da su.
“Bakin ya mutu ne?�.
Yay maganar yana matso da fuskarsa daf da tata.
Itakam ta rasa yaya zatai da Yah Ahmad, shi baisan kunyarsa takeji bane halan? Tun daga dawowarsa jiya ya koma mata tamkar bashiba a komai.......
Iskar daya busa mata saman idanu ya sata lumshesu sosai tsigar jikinta na tashi, ya jawota gaba ɗaya jikinsa, ya cire mata hijjabin tare da faɗin, “Yaya jikin?�.
Baki taɗan kumburo masa kaɗan da faɗin, “Nidai lafiyata lau fa Yaya�
“Oh ALLAH? Shike nan kinga to bara mu maimaita�.
A zabure tace, “Yah Ahmad mi?�.
Yanda tai maganar hawaye na zubowa lokaci ɗaya saman kumatu ne ya sakashi yin dariya, yaja hancinta kaɗan tare da dungure mata kai yace, “Mai raki kawai, iya tasan har ita kika kira saboda ragwantakarki saita miki dariya�.
Cusa kanta tai a jikinsa tana murmushi, jiya kam a ƴan gidansu ai babu wanda bata lissafo ba, har Tahir dake shan nono bata mantaba, yo taji azaba, ashe abun da gaske babu sauƙi........
Ahmad ya katse mata tunani da faɗin, “Kinga tashi kije ki kwanta, wannan barcin da muka ɗau bashi idan bayinsa akaiba zai haddasa ciwon kai�.
Da ƙyar Rumana ta bar jikinsa ta miƙe, bata yarda ta kallesa ba taje ta haye gadon ta kwanta, shima da yake binta da kallo tashin yay yacire rigarsa ya hau gadon.
Jinsa a jikinta ya saka sabon tsoro bijiroma Rumana, ta lafe tamkar mai barci tana sauraren mizai biyo baya, sai bataji komaiba, hakan ya sata sauke ajiyar zuciya a hankali.
Ahmad daya jita ya murmushi kawai.

★★★★★★�
Chapter 38 · 0% Book details