Sashe 3
Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tunda Ahmad ya shiga rayuwar Samina ya fara canjata sai baba Yusha'u kejin daÉ—i sosai, dan abubuwa da yawa sai Samina tabar biyema mahaifiyarta, dan a hannunta ta tashi, lokacin da mama Gaje ta dawo gidansu Ahmad sai tarbiyyar Samina ya banbanta dana sauran yaran gidan.
Daɗin hakan da Baba Yusha'u ya jine ya sashi zaunar da ƴan uwansa duka a gaban iyayensu su iya ladi, aka kuma kira masa Ahmad da Samina, a gaban kowa ya kuma sake damƙa ma Ahmad amanar kula da Samina, tare da alƙawarin aura masa ita a duk lokacin da suka kai munzalin girma, ya kumace ko bayan babu ransa bai yarda wannan alƙawarin ya tashiba.
Murmushi kawai Ahmad yayi kansa a ƙasa saboda kunya.
Yayinda sauran ƴan uwa da tsoffi su malam Rabi'u wannan abu yay musu daɗi, dankuwa koba komai zumincin ƴaƴansu zai ƙara danƙo da ƙarfi.
Albarka kowa ya sakama abin, tare da addu'ar kaiwa lokacin da rai.
Tun daga wannan lokacinne kuma Samina bata kula kowanne namiji, kowa yasan an mata miji Ahmad, hatta da danginsu na Shema kowa yasan hakan.
Mama Gaje dai batace hakan bai mataba, bakuma taji a ranta zuwa nan gaba idan Samina ta sami wanda yafi Ahmad zata hanata barin Ahmad ɗinba, idan kuma Ahmad yayi arziƙi dama ta dawo hannunta, dan kuwa sai yanda tayi dasu Ayyah akansa.
Tunda Ahmad ya gama secondary ya koya É—inki yana kama Æ´an kuÉ—aÉ—e sai nauyin Samina ya kusan koma kansa, shine duk wani bukatunta na makaranta, shine dinkinta da bukatun yau da kullum na É—iya mace, hatta dasu kayan ciki na mata bai gazaba wajen bata kudin saye.
Wannan hidima da yake da ita sai ta ƙara saka mata girmansa da ƙaunarsa a zuciyarta, bata da hira sai ta Ahmad, duk wani namiji a idonta mace ne, Ahmad ɗintane kawai take kallo da gashin arziƙi, shine kuma kawai nagartaccen namiji a idonta.
Bayan samina ta gama secondary lokacin Ahmad na shekararsa ta ƙarshe a jami'a sai yake bata shawarar komawa karatu.
Lokacin suna zaune a ƙofar gidansune a shagon ɗinkinsa suna hira, dama mafi yawan lokuta anan suke hirar tasu.
Kallonsa tayi da ɗan murmushi ta dukar da kanta ƙasa saboda kunyarsa, cikin muryarta mai cike da yanga tace, “Haba Hubby, kamar ka manta yanda al'amuran suke a gidannan namu, idan nace zan cigaba da karatu yanzu a ina baba zai samu kuɗin ɗaukar nauyina?, kullum ana haɗa na masara da ƙyar a ina za'a samo na karatu kuma?, sannan a ziri'ar mu kaf babu macen data taɓa gama secondary sai nifa, shima da taimakonka, saiko ƙannenmu uku mata da ayanzu suma zasu kammala, iyayenmu ma bazasu amince naje jami'a ba nima nasani�.
Murmushi Ahmad dake kallonta da tausayawa yayi, ya sauke ajiyar zuciya har lokacin idonsa a kanta, a hankali yace, “Samie na ai komai na ALLAH ne, indai kina da ra'ayin karatun baki da matsala, dan ba baba zamu dorama wannan nauyinba, nine zan ɗauki nauyin matata da kaina, kinga insha ALLAHU idan ubangiji ya shige mana gaba sanda zaki kammala ƙila koda karamin aikine na samu, sai maganar aurenmu ko, kodama baki gamaba inhar aka samu ɗan abin rufin asiri sai mu rufama kanmu asiri a wankemu a miƙamu daga ciki kowama ya huta�.
Maganarsa ta ƙarshe ce ta sakata jan hijjab ɗinta ta rufe fuskarta saboda kunya tana ƴar dariya.
Shima dariyar yayi mai sauti yana shafa kansa, yace, “Sorry bazan sake bama matata kunyaba, ammafa randa aka kaimin ita zan cire kunyarnan dukanta insha ALLAHU�.
Babu shiri Samina ta tashi ta gudu zuwa gida, duk kiran da Ahmad yake mata akan ta dawo su karasa magana kasawa tayi, dole ya haƙura ya ƙyaleta.
Daya shiga gidan suka haɗuma da sauri ta kauda fuska taƙi kallonsa, lokacin suna a tsakar gida itada su Rumana suna shafa kurkur a fuska.
Murmushi kawai yay yana ɗauke kansa, dan baya wasa da yaran gidan, idan ka cire Samina babu mai yawan ganin haƙoransa a cikinsu.
Duk sannu sukai masa, ya amsa kamar yanda ya saba, sai da yazo gab da shiga sashensu ne suka haÉ—a ido da Samina data saci kallonsa.
Ido É—aya ya kashe mata yana murmushi, tai saurin É—auke kai tana murguÉ—a masa baki.
Shigewa yay yana maijin nishaɗi da ƙarin kaunarta a ransa.
Da daddare Samina take sanarma mahaifiyarta yanda sukayi da Ahmad.
Mama Gaje da daɗi ya lulluɓe ta washe baki tana rungume Samina.
“Yo Samina wannan kuwa abin amincewane da guduma, damacefa tazo mana, ai wannan yaro bamusan abinda zamuce masaba a rayuwa, ALLAH dai ya saka masa da alkairi, yakuma kaimu lokacin aurenku, dan kuwa Suwaiba ta haifama Ruƙayya, niko Ruƙayya ta rainar mini�.
Duk da Samina bata fahimci zaurencen mahaifiyarta na ƙarshen maganarba Babu kunya ta amsa da amin, dan tana tsananin son Ahmad da har takai batajin kunyar yin duk wani abun daya shafesa a gaban kowa, iyayensu maza kawai take iya ɗagama ƙafa akan Ahmad.
Hatta kakanninsu Iya ladi da baba Rabi'u bata jin kunyarsu akan Ahmad.
Sai washe gari Ahmad ya samu saƙo a rubuce daga wajen Samina akan amsar cigaba da karatunta.
Yaji daÉ—in hakan sosai, a ranar kuma ya samu su baba da batun su duka harma da kakanninsu.
Da farko dai tsoho mai ran ƙarfe malam Rabi'u har yace a'a, danshi kam baiga dabara ba a wajen nan sam.
Amma sai Ahmad yayta lallashinsa da nuna masa ra'ayinsa akan matarsa tai karatu mai zurfi, tunda yanzu suna da dama saita fara kafin shi yaɗan samu madogarar da za'ai hidimar aurensu, in yaso ita saita ƙarasa karatun a gidansa.
Fatan alkairi yay musu, tunda ya fahimci Ahmad nason lamarin, bai kamata a katse masa hanzariba matsayinsa na babba namiji a gidan.
Kwana biyu dayin zancen Ahmad ya amshi takardunta ya tafi dasu makaranta.
Tun daga ranar Ahmad yashiga faɗi tashi wajen ganin ya samawa Samina gurbin karatu, kasancewarsa mai ƙokari a makarantar yasashi kusanci da mafi yawan malaman cikinta, ta hanyarsu ya samawa Samina gurbin karatu.
Lokacin da labarin hakan yazo mata tayi farin ciki harma ta rasa ina zata saka kanta dan daÉ—i.
Hakama iyayensu kowa yaji daÉ—i, babu kuma wanda ya nuna rashin dacewar hakan, dan a ganinsu Ahmad É—in yanada ra'ayin matarsa tasamu karatu mai zurfi shiyyasa ya maida Saminar makaranta.
Sauran Æ´an uwantama Æ´ammatan gidan sun tayata murna da wannan cigaba, koba komai suma zasu saka ran cigaban tunda aka fara daga kanta.
Nauyin karatun Samina daya dawo kan Ahmad sai ya sa abubuwa suka sake masa yawa, dan kuɗin shigarsa basu kai nauyin ɗukar hidimar da yakeyiba, gashi dai-dai da kuɗin mota wannan sai Samina tazo wajensa take amsa. Ga nauyin karatun Mudanseer ma shine yake bada mafi yawan ƙarfinsa, dukda mahaifansu na taimakawa tanan ɓan garen.
Kuma a gefen hidimar gidama baya zuba ido baneba, yanayin ƙoƙarinsa wajen taimakon mahaifinsu.
Wannan abubuwan da sukaimasa yawane ya sakashi fara tunanin faɗaɗa neman kuɗin nasa, akuyarsa da ya saya Ayyah na kula da ita yace zai saida ya zuba kayan ɗinki na saidawa, saboda akuyar ta haifi yara biyu sai Ayyah ta amince masa aka saida, da kuɗin akuyar yaɗan sayo kayan su zare da wasu ƙananun abubuwa irinsu allura, almakashi, zips da sauransu ya zuba a shagon, teloli dake cikin gida da masuma shagunan dake kusa sai sukanzo sukan saya anan, kamar wasa sai ALLAH ya sakama abin albarka ake ciniki, idan duk suna makaranta sukan ɗan ɗebo kayan sayarwar a ajiye cikin gida, duk wanda yazo saya sai yayi sallama a bashi.
Ahmad bai tsaya ananba kawai, har komawa yay idan ya taso makaranta ya sari lemuka ya É—ora a kansa yana zuwa bakin titi saboda motoci masu wucewa, wani lokacin kuma biredi, ko kayan fruits haka.
Da waɗannan sana'oi da wahalhalu Ahmad ya cigaba da kula da karatunsu shi da Mudanseer da samina, sauran ƙannensa ma yakan basu gudunmawa, hakama yayunsa dake gidan aure sukan taimaka masu da abinda ALLAH ya hore musu.
Ahmad ya kammala degree ɗinsa ya samu yay bautar ƙasa, daga nan kumane ya dawo zaman gida sosai, dan babu dai maganar aiki.
Yaci gaba da sana'oinsa na ɗinki da saida kayan ɗinki, zuwa yanzu kuma hannunsa ya faɗa sosai ya ƙware, ɗinkuna yake na zamani masu birgewa, duk wasu samari ƴan kwalisa da ƴammata zaka samu ɗinkinsu ya fitone daga shagon Ahmad, wanda aka fi sani da Ahmad sharukhan, idan ɗinki yaɗan kwanta saiya koma sana'arsa ta sai da lemo da ruwa, kokuma kayan fruits.
Yanzu dai haka takai Ahmad yana hayar keke napep ne, yay É—inkinsa da yamma ko dare, da safe zuwa la'asar yana neman taro da kwabo da adaidaitarsa a gari.