Sashe 78
Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin kwanaki kaɗan komai ya kankama na karatunsa, Gaddafi ya ɗaukesa sukaje har makkah yay addu'oi ɗakin ka'aba na neman nasara da haske a dukkan al'amuransa, makkah ma ta ƙawatar dashi ainun, yay ziyarce-ziyarce sosai kafin ya fara zuwa makaranta, shine har Madina bisa jagirancin Gaddafi dai.
Aiko Alhmdllh, dan tunkan ai nisan zango yafara cin karo da hasken, dan kuwa yanda ya kamata yana fahimtar karatun da yazo dominsa.
Satinsa biyu a gidan gaddafi ya samu wajen zama shima, hakan yasa ya tattara ya koma can, gashi abin jin daÉ—i kusa da makarantar.
KwaÉ—ayin son faÉ—aÉ—a ilimin addini dan amfani da damar da ALLAH ya bashi, ya sakashi ma Gaddafi maganar son komawa makaranta, sosai Gaddafi yaji daÉ—in wannan al'amarin, kuma Ahmad ya birgesa, babu bata lokaci nanma ya shiga shigi da fici har Ahmad É—in ya samu shiga wata islamiyya ta dare da aka buÉ—e domin magidantan da basu da lokacin kai da rana da irinsu Ahmad da karatu ke cinyema lokaci, nanma dai Ahmad ya fara karatunsa cike da nasarori kuma ya maida hankali dan kuwa masu iya magana sunce gemu baya hana ilimi.
Kullum da dare sai yayi waya da iyalinsa, Rumana taita masa shagwaɓar da ke tada hankalinsa dajin buƙatar son ta matso kusa dashi.
Haka kwanaki sukaita jaa, abubuwa nata faruwa, inda kafin kace kwabo Ahmad ya ja watanni huɗu da tafiya, tun yana ƙaraminsa mutum ne shi mai zuciyar nema, hakan yasa ko a ƙasar ta saudia bai zauna ya dogara da karatunba kawai, dukda duk watan duniya albashinsa na shiga asusunsa, wanda aciki yake fidda hidimar iyalansa da ahalinsa.
Shawara ya nema wajen Gaddafi akan son fara yin wani abun, Gaddafi yay murna da wannan zuciya ta Ahmad, nan take ya bashi shawara ƙyaƙyƙyawa kuwa, da taimakonsa suka haɗa ƙarfi da ƙarfe duk da dai na Gaddafin sunfi suka fara kasuwanci, dan dama shi Gaddafin yanayi.
A lokacin da Ahmad yake watanni na goma sha ɗaya sai dai muce Alhmdllh, dan kuwa dai-dai gwargwado yasamu rufin asirin da zai iya maido su Rumana nan, babu ɓata lokaci yasa aka fara musu shirin tahowa harda Zainab, Abu kuwa anan porthercout ɗin yasa ake nema masa admission, dan dama yana zuwa wajen Nura tare suke zama wajen sana'ar kayan yarinsu Ahmad ɗin.
Randa Ahmad ke sanarma Rumana suyi shirin tafiya kano tayi farin ciki sosai, dan tafiyace dake nuni da sun tafi kenan daga can jirginsu zai É—aga zuwa saudia.
Harda Abu suka taho kanon, amma shi zai dawo ne tunda komai na karatunsa ya gama kammala.
Sosai Rumana kum taji kewar Port, zuwa yanzu kuma babu inda Haysam baya zuwa da ƙafarsa, yayi wayo sosai har magana yakan ɗan dagula duk da bata fita da ƙyau sosai, ta kuma yayesa ba tare da kowa ya saniba hatta da shi Ahmad ɗin kuwa..
Kowa yayi farin ciki da wannan zuwa nasu, sai dai banda irinsu mama gaje da har yanzu suka kasa samun mafita balle damar cutar dasu.
Haysam É—an dangi, kowa sai É—aukarsa yake da jinjina saurin wayon yaron.
Dukda Rumana taɗan rame saboda rashin mijinta a kusa hakan bai hanata sake yin ƙyauba, fatarta sai ɗaukar idanu take.
Wannan zuwan bata zaunaba, ta shiga ziyarce-ziyarcen dangi dayin sallama, itace har katsina wajen Fa'iza dake fama da cikin da har ya fito, da alama dai kusan lokaci É—aya suka samu ita da Salima ma, duk da sun huta sosai sunci amarci kafin ALLAH ya kawo cikin.
Fa'iza tayi farin ciki matuƙa da zuwansu, ranar sunsha hira sosai, suka kwana suka hantse washe gari da yamma suka taho suka barta cike da kewarsu.
Wannan karon ta samu har tsohon gidansu taje domin gaida su Maman Ama, sai dai tayi rashin sa'a ta iske maman Ama bata nan, wai tayi yaji saboda faɗa da sukai da mijin akan zai ƙara aure ya faffale fuskarta da maruka.
Kausar kawai ta iske sai waÉ—anda suka kama hayar É—akin da suka zauna yanzu, sosai Kausar ta ruÉ—e da ganin yanda Umm-Ruman ta sake canjawa, tamkar ba ita bace ta zauna a gidan nasu, gashi ta girke ta zama mace sosai, keko shekara kusan biyu kenan basuga junaba, tun arba'in É—in Haysam da gashi yanzu yana takawarsa.
Duk sai Kausar ta raina kanta, tanatama Rumana Gulmar maman Ama, ita dai Rumana bata tofa tataba sa ALLAH ya ƙyauta da tace, da tagama abin zai wuce makaɗi da rawa tai musu sallama ta taho, ta barsu da tafa hannaye na mamakin wai yanzu Saudia su Rumanan zasu koma?.
Aiko maman Ama na dawowa bayan kusan sati da zuwan Rumana da labarin zuwan Umm-Ruman ɗin Kausar ta tarbi maman Ama duk da a yanzu basa shiri anyi uwar watsi tuni, harda ƙara gishiri da magi😂.
Maman Ama taji takaici na rashin ganin Umm-Ruman, dan haka ta É—au aniyar sai tazo har gida taganta tunda Kausar tace sai nan da sati biyu Rumanan zasu wuce.
Sai dai kuma an taki rashin sa'a, dan kuwa kwanaki huɗu da zuwa Umm-Ruman maganar tafiyarsu ta tashi, haka sukai sallama da ƴan uwa da abokan arziƙi, suna kuka itama tanayi sukai mata rakkiya airport ita da Haysam da Zainab suka lula abinsu.
__________________________________
*_SU UMM-RUMAN A JIRGI ZA'A BAR ƘASA🥴😹_*
Cike zuciyarta take da kewar ahalinta, gefe kuma na cike da farin cikin zuwa ga mijinta da tai kewa tsawon watanni takwas, tare da ɗunbin ɗoki zuwa ƙasar da kowa ke fatar ganinsa a ciki.
Ahmad na filin jirgin tarbarsu tun kusan awa ɗaya saura su sauka, yana cikin tsagwaron zumuɗi da baki ma bazai iya furtawaba, Gaddafi da matarsa Jiddah da ƴarsu data haifa mai suna Subayya sunata masa dariyar zumudin da yake famar yi, bai kulasu ba, idonsa akan ƙofar jirgi da mutane ke fitowa
Can kuwa saiga taurarinsa guda uku na fitowa, Umm-Ruman ɗauke da Haysam a hannu tana cikin jallabiya ruwan siminti datai mata masifar ƙyau, ta naɗa gyale ruwan ƙasa da yay dai-dai da adon duwatsun da akai kwalliyar rigar mai zubin bubu dasu, sai Zainab dake sanye da wando da riga itama ta ɗora baƙar afterdress a sama, ta sake zama budurwa abinta, dan yanzu tana a shekara ta goma sha uku ne, Haysam kuwa yana sanye da wandon jeans da t-shirt mai ƙyau, shima ya ƙara girma sosai a idonsa yaron, ga kamaninsu da suka sake bayyana tattare da yaron musamman ma shi.
Ahmad ya sauke wani sassanyar ajiyar zuciya yana lumshe idanu, duk yanda yaso yin haƙuri su ƙaraso kasawa yay, ya shiga takawa zuwa garesu.
Inda itama Umm-Ruman idonta ya sauka a kanshi lokacin da Zainab ke faɗin, “Lah aunty Rumana kinga Yaya�
Da ƙyar Rumana ta iya haɗiye yawu da zuƙar numfashi saboda canjawar da Yayan nata kuma mijinta ya sakeyi, ya sake girma da ƙiba tare da wani ƙyawu mai ban mamaki saboda canjin wajen zama daya samu, sai kace baima taɓa aureba balle tunanin ajiye ɗa kamar Haysam.....
Jitai kawai an rungumeta ita da Haysam ɗin, hawaye suka silalo mata akan kumatu saboda buɗe ido datai ta sauke akan Ahmad dake rungume dasu su duka har zainab ɗin da itama ta ƙanƙamesa cike da farin cikin ganinsa.
Dukansu shida Rumanan sun kasa magana, sai ɗagowa yay suka zubama juna idanu tamkar baƙin ganin juna, ya ɗage mata gira yana cizar leɓensa na ƙasa, murmushi tayi tana duƙar da kanta ƙasa saboda kunya.
Shima ya murmusa yana maida idonsa ga Haysam daketa kallonsa, shi dai ya manta da Abban nasa, amma koda ya miƙa masa hannu bai musaba yaje garesa, ya shafa kan Zainab itama yana mamakin canjawar da duk sukai masa.
Gaddafi da Jiddah da suka matso ne suka katsesu, suka shiga yima su Umm-Ruman barka da zuwa.
Ansan juna a waya, dan suna gaisawa da junansu, hakan yasa babu tambaya Rumana ta ganesu, amsar Subayya dake hannun Jiddah, tayi tana mai yaba kÆ´awu da girman da yarinyar tayi a watanni bakwai da haihuwarta.
Gaddafi ma ya miƙa hannu domin amsar Haysam a hannun Ahmad, amma sai yaƙi, dariya suka sanya, Gaddafi yace, “Wato shi Abbu duk da ka daɗe baka gansaba ka gane abunka? Niko da baka saniba shine zakamin ƙiwa?�.
Dariya Ahmad yay yana kallon Haysam dake wasa da ƙasumbarsa, yace, “Sadaukina Uncle nefa, wanda ya baka mata tunkan kazo gata nan�.
Amamakinsu sai sukaga Haysam na dariya kamar ya fahimci abinda ake nufi, hakanne suma ya sakasu darawa baki É—aya.
Motar Gaddafi suka shiga gaba É—ayansu domin tafiya gida...........âœðŸ?
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋â¤ï¸NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋â¤ï¸NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋â¤ï¸SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋â¤ï¸NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* â¤ï¸ðŸ’‹NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuÉ—i gida masoyan asali😉😻🥰🥰ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜˜ðŸ˜˜ðŸ‘ŒðŸ»ðŸ’ƒðŸ»ðŸ’ƒðŸ»_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASANðŸ˜ðŸ‘‰ðŸ»ðŸ“»
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*ðŸ˜ðŸ™ðŸ»