Sashe 15
Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Ranar da yamma aka sallamo Samina, ma'aruff ya É—akkosu a motarsa ya kawosu gida, Ahmad sai mashin ya hawo ya biyo bayansu.
Babu wanda yace komai akan hakan, kowa ya shiga yay mata sannu, hakama maƙwafta sunata shigowa, ƴan son ganin zahiri a ɗauka ai gaba sunta gumtsar gulma.
Ahmad dai tunda suka dawo yana É—akinsu kwance, sai bayan sallar isha'ine ya shiga gidan, Ayyah ta samu ta titsiyeshi yasha furar data saya masa tun da rana.
Bayan ya gama sha ne yaje É—akin baba ya amsa kiran da yay masa, sun É—an tattauna kafin su fito zuwa sashen malam Rabi'u.
Kamar yanda Ahmad ya bukata dukkan iyayensu mata da maza sun hallara.
Ahmad na share hawaye tamkar mace ya fara magana cikin nutsuwa.
*_“Da farko dai ina godiya ga ALLAH sannan a gareku iyayena, nasan kun nuna dukkan hallacinku gareni, tareda ƙoƙarin ɗaura igiyar da zata ƙulle zumincinmu fiye da da, ina neman afuwa a gareku badan, kubani dama na aiwatar da abinda zai kawoma kowa kwanciyar hankali, ba tare da abinda muke gani dai-dai ya koma kuskureba. Son gaskiya nake miki Samina, wanda babu ta yanda idan na musalta za'a fahimceni, a tawa fahimtar ka bama abinda kakeso kowacce irin damar da yake buƙata kuma zata kawo masa kwanciyar hankali da farinciki shine soyayya ta gaskiya, na fahimci a yanzu sam hankalinki baya gareni, to bazan tursasakiba, ni Ahmad Hamza Rabi'u ku shaida daga yau, na saki matata Samina saki daya, domin sadaukar da soyayyata ta gaskiya, taje ta auri wanda takeso, ALLAH ya basu zaman lafiya da zuri'a ɗayyaba�._*
Ahmad ya ƙare maganar yana share hawaye masu zafi dake gangaroma kumatunsa.
Tsit ɗakin yayi, hatta da Samina sai da taji wani iri a ranta, amma tai saurin ture tausayinsa tana sauke numfashi irin na na rabu da ƙaya ɗinnan.
Malam Rabi'u ya saki murmushi irin nasu na manya, cikin muryarsa ta tsufa yace, “Amadu ALLAH yay maka albarka, ALLAH ya tsare gabanka da bayanka, ya share hawayenka, ya sanya farinciki a rayuwarka har gaban abadan, lallai kacika namijin gaske mai soyayya dan ALLAH, inaji kuma a raina koda ba'a nan duniyaba zaka samu ƙyaƙyƙyawan sakamako�.
A tare baba Iliyasu da baba Yusha'u sukace, “Insha ALLAHU� daga nan suma suka ɗora da sanya masa albarka, baba Yusha'u yace, “Ahmad a karo na biyu inhar ka amince na baka auren Umm-Rumana, badan komai nake ƙwaɗayin wannan haɗinba sai ƙyawawan halayenka, duk uba daya mallakeka matsayin ɗa ya gama hayewa a rayuwarsa, hakama duk surukin da ya sameka matsayin suruki yaci riba, yanda naso wannan haɗin zumincin bana fatar bijirewar wadda bata ɗaukeni da muhimmanciba zaisa gwiwa ta sarewa�.
Murmushi nanma malam yayi, idonsa kafe akan Ahmad da ya kasa koda motsi, shida yake ƙudirawa a ransa safiyar gobe zai bar garin gaba ɗaya yay nesa dasu shine za'a masa wannan dabaibayin kuma?.......
Cikin katsema Ahmad tunani malam yace, “Amadu inhar wannan haɗin bai maka ba karka cutar da kanka, dan kuwa ba tilas bane a gareka, amma ni kaina nayi maka sha'awar hakan, dan Umm-Rumana yarinyar kirkice da kowane miji zaiyi fatan samu�.
Innalillahi...... Ahmad yaketa ambata a ransa, wannan magana ta masa girma, shidai a yanzu bai dace ya bijirema iyayensa ba kodan abinda Samina ta aikata, sannan koba komai itama zai maida mata murtani, kamar kuma yanda yay alƙawarin haƙura da ita auren Umm-Rumana ne kawai zai tabbatar masa da hakan tunda ubansu ɗaya...
Ayyah ce ta dafashi, hakan yasa yay saurin kallonta, da ido taimasa alamar ya amshi auren, dan haka ya maida kansa ƙasa ya duƙar yana faɗin, “Na amsa baba, ALLAH yasa haka shine mafi alkairi�.
Dandanan fuskar kowa ta washe da murmushi, banda Samina da mama gaje, dan mama gaje ma baki ta taɓe ta miƙe riƙe da hannun Samina da tai gajeren tsaƙi suka fice.
Babu wanda yabi takansu, balle a nuna an damu dasuma.
★★★★
A wannan daren kam inhar Ahmad yayi barci to sai dai ɓarawo kuwa, dan komai ya juye masa, har mamakin abun yake da tunanin koma dai mafarki yakeyine?.
Ya ayyana hakan a ransa yafi sau dubu, harma Mudanseer dake kwance gefensa ya kasa jurewa ya tashi ya fara masa nasiha da shawarwari duk da kasancewarsa yayansa, tare da haƙuri akan canjin da ALLAH yay masa akan Umm-Rumana, inhar yay haƙuri ya riƙe watarana zaiyi dariya insha ALLAHU, ya cire zancen Samina a ransa, ya fuskanci sabuwar rayuwar gida wata soyayyar, kamar yanda itama ta nuna ta manta da shi da komansa.
Yaji daɗin shawarar ƙanin nasa sosai, dan haka ya samu ƙwarin gwiwar tashi yayo alwala yazo ya fara nafilfili yana miƙama ubangiji kuka sa.
Ranar haka ya kwana kan sallaya, sai da suka dawo sallar asubahine ya samu ya kwanta ramuwar barci.
**********
Æangaren Samina jinta take sakayau, duk da wani gefe na zuciyarta yana suka akan maganar haÉ—a Umm-Rumana aure da Ahmad, sai dai kuma tana Æ™okarin kauda abin a ranta baki É—aya, musamman yanda jikinta har yanzu babu Æ™arfi, ga Mama Gaje kuma nata zuga Æ™oÆ™arinta akan abinda tayi har Ahmad ya saduda ya saketa.
Ranar dai da tsantsar farin ciki tai barci, kusan raba dare sukai tana hira ita da Ma'aruff a waya, kowa na ƙara jadadama ɗan uwansa irin ƙaunarsa da yakeyi cikin zuciya da ruhi.
Umm-Rumana kam batasan bikin da akeba a kanta, dan babu wanda ya sanar mata da komai, ko mahaifiyarta batace mata komai akan maganarba.
Amma batayi baƙin ciki akan aurar da ɗiyarta ga Ahmad ba, dan kowa yasan mutumin kirkine, bashi da wani mugun halin da za'ace abin gudu a rayuwarsa, to mizaisa tayi baƙin ciki da hakan, tunda har mahaifin Umm-Rumana da kansa yaga nagartar Ahmad yakuma ji a ransa zai masa halacci da ɗiyarta, fatan alkairine kawai nata da musu ƙyaƙyƙyawar addu'ar zaman lafiya.
___________________________
Babu wanda yay tsamanin a ranar za'a sake ɗaura auren, sai gashi kusan ƙarfe goma sha ɗaya na safe motocin ƴan shema har huɗu sun dira maza da mata, dandanan gidan ya kacame da hayaniyar ƴan bikin da sam babu shiri, hakama dangin Ammi mahaifiyar Umm-Rumana sun cika gidan, dangin gwaggo ma haka na kusa sai ɓullowa sukeyi ta ko ina, to abinka da maganar waya.
Duk wannan abu dake faruwa Ahmad bai saniba, sai da Mudanseer ya tadashi akan ya tashi lokacin salla yayi, mamaki ya kamashi lokacin daya shigo yaga gidan a cike.
Babu kuma wani ɓoye-ɓoye Ayyah ta sanar masa aurensa za'a sake ɗaurawa bayan sakkowa masallacin juma'a da Umm-Rumana.
“Ayyah da wuri haka? Nazata ai za a bari sai nan gaba ta kammala makarantarta�.
“Haba ɗan albarka, minene wani abin jinkiri anan, Rumana dai ai ta isa aure, kuma ba baƙuwarka bace balle kace kanason sanin halayenta, kaima ba baƙonta baneba, idan batun soyayya ne kuje can a gidanku zaku ƙullata, tamafi ta shirmen wajen nan daɗi da nagarta, makaranta kuma duka wata nawa ya rage, idan taje gidan naka saita karasa ai, muma munfison ayin kawai hankalinmu ya ƙwanta, dan nafison ka riga yarinyarnan yin auren, muyi addu'a kawai ALLAH yasa haka shi yafi alkairi, maza je kayi wankan ga waɗannan kayan saika saka�.
Jiki a sanyaye ya amshi farar shaddar dake a cikin leda viva yay mata godiya..........âœðŸ?
*_ALLAH ya gafartama iyayenmuðŸ˜ðŸ™ðŸ»_**ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*ðŸ™ðŸ½
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuoeSgXuo
*(10)*