Sashe 29
Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan sallar isha'i Ahmad ya fita zuwa gidansu, dan tun dawowar da yay bayan sallar juma'a bai sake fitaba sai da zaiyi sallar magriba, daga nanne kuma bai komaba har akai isha'i ya wuto nan.
Ƙannensa dake cin abinci a ƙofar Ayyah duk suka gaishesa.
Amsa musu yayi cikin rashin sakewa, hakanne ya sakasu fahimtar yana cikin damuwar abinda ya faru É—azun har yanzun kenan.
Daga can ƙarshen tabarmar da suke zaune ya zauna, a haka Ayyah ta fito daga lungun Baba ta sameshi..
Da damuwa sosai a fuskarta tace, “Ɗan albarka dama kana nan?�.
Kansa ya ɗago yana kallonta, ya girgizashi kaɗan yana faɗin, “A'a Ayyah, ai tun tafiyar da nai ɗazun ban dawo ba, yanzu ma nazo wajen baba ne�.
“To lafiya dai ko?�.
“Lafiya lau Ayyah, magana kawai nakeson muyi, amma inaso ma ace kema kina wajen�.
“Shike nan tashi muje ai yana ciki�.
Tashi yay tsaye, Ayyah na gaba yana biye har lungun baba dake zaune a ƙofar ɗaki saman tabarma, kwanika na gefensa da alama abinci ya gama ci, dan hannu ma yake wankewa lokacin da suka shigo.
Zama sukai suka jirashi ya ƙarasa, ya ajiye butar yana fesar da ruwan bakinsa da ya kurkure, sannan ya jawo da baya ya zauna sosai.
Gaishesa Ahmad yayi, ya amsa cike da kulawa yana tambayarsa Rumana.
“Tana lafiya baba, tace ma a gaisheku�.
“Muna amsawa, amma lafiya na ganka haka kamar mai fama da ciwo?�.
Kan Ahmad a ƙasa yay murmushi, murya a sanyaye yace, “Lafiyata lau Baba, kawai dai yanayin garinne�.
“Amadu yanayin gari kokuwa abinda ka kasa yakicema ranka?, bara na faɗa maka gaskiya, inhar baka cire yarinyar nan da halayenta a ranka ba bafa zaka zauna lafiya cikin salama ba, ka cire duk wani abun da ya faru ko yake faruwa a gidannan ka fuskanci matar da ALLAH yay maka zaɓi madadin son zuciyarka, Ahmadu idanfa kai saken da yarinyar nan Rumana ta farajin ciwon wannan shirmen naka har taso guje maka wlhy zakayi *GUDU DA WAIWAYE....*, kasan kuwa da ga karshe iyakarka mugun zato, amma baka da karfin ɗaukar mataki, ina saka maka idone kawai dan naga iya gudun ruwanka, to na lura bamai sanin zuru bane kai, yanzu abinda akace yarinyar nan ta maka yau a gaban saurayi da mutanen anguwa idan kai da mai zuciyane bai cancanci ka ɗauke kanka daga gareta ba har abada?........�
“Ayi haƙuri dai malam, ai kowa yasan yanzu hankalinsa baya a kan Samina, sai dai mu tayasa da addu'a kuma, kasan dama irin wannan fitarsa a rai sai dai a hankali�.
“Kayya Ruƙayya, ke dai bar lamarin shirmen wannan ɗan naki, inda har bai saka abun a ransaba ai da yabar damuwa da lamarinta, ya kuma tashi ya nema ma kansa mafita ko�.
Ahmad da kansa ke a ƙasa yace, “Baba kuyi haƙuri ku gafarceni, yanzu ma haka nazone da wata mafitar, fatana dai ta zama mai amsuwa a gareku�.
Baba yace, “To babu laifi, muna saurarenka�.
Sai da Ahmad ya kuma luliya maganar a zuciya kafin yace, “Baba dan ALLAH inason a bani izini na bar garinnan�.
“Kabar gari kuma? To zuwa ina kenan?�.
“Duk inda ALLAH ya rubuto mani, inason fita nema ne kawai, bawai dan anmin gorin rashin arziƙiba, ba kuma dan ban godema ALLAH da sana'ar da ya baniba, hakan zaisa zuciyata mance komai dai insha ALLAHU�.
Baba dake jinjina ka sa yace, “Banƙi ta taka ba, amma dai abin dubi anan ita matar taka fa? Duk auren naku kwanansa nawa? da za'ace ka tafi wani waje ka barta, sai naga kamar akwai wauta�.
Shiru Ahmad yay, dan haka baba yace, “Jeka tsakar gida ka jiramu, amma ka turo mani Suwaiba�.
Ahmad ya amsa da to yana miƙewa ya fita, da kansa ya leƙa ɗakin gwaggo ya sanar mata kiran baba.
Batace dashi komaiba ta kashe redion da takeji ta tashi ta fito amsa kiran.
Koda tazo ta zauna Baba yay mata bayanin komai da Ahmad yazo dashi, bata ce komai ba a kai, dama sunsan bazata ce ɗinba, sai Ayyah ce ta bama baba amsa da “Niko malam sai naga kamar babu komai insha ALLAHU, musamman dai da itama Rumana tamuce, kuma itama barinsa garin zai kawo mata salama harya fuskanceta, sannan kuma bamusan alkairi. da ke cikin wannan tafiyaba da yaketa ambato, amma duk hukuncin da ka yanke akan hakan mu masu biyayyane akansa, dan abinda ka hango mu bazamu hangosa ba sam�.
Baba dake sauraren Ayyan ya sauke nannauyan numfashi, kafin yace, “Tunda har kun aminta da hakan kuma ai Alhmdllh, ni dai dama ba matsala bane, tun kuma maganar farko da kikaimin na sanar da su Iya, suma basuyi jayayyaba, sun dai ce na dakata har sai ya sake kawo maganar da kansa, to tunda yanzu ya sake maganar ai ina ganin sai kawai mu bisa da fatan alkairi ko?�.
Cikin faɗaɗa murmushi Ayyah tace, “Hakane malam, mun kuma gode da wannan amincewa, sai aita tayamu da addu'a kuma�.
“Addu'a ai dolece Ruƙayya, shi mai yara inhar da hankali jikinsa ai kuma isasheahen barci ya kare masa kenan, ALLAH dai ya cigaba da mana jagora da tsare mana su baki ɗaya�.
Amin ya rabbi, Ayyah da Gwaggo suka amsa a tare.
Ayyah ce ta leƙo da kanta tai kiran Ahmad, dan haka ya tashi ya koma.
“Amadu mun amince kaje, amma da sharaɗi�.
Ahmad ya É—ago yana kallon baba, don san jin minene sharaÉ—in.
Baba ya cigaba da faɗin, “Sharaɗin shine karka yarda dogon lokaci ya riskeka baka ziyarci gidaba, sannan inhar kai dawowar farko naga ka canja daga Amadun dana sani to lallai bazaka sake komawa ba�.
“Baba na amince da dukkan sharaɗin, fatana dai kuci gaba da min addu'a�.
“Za'a cigaba dayi insha ALLAHU, yanzu yaushene kake shirin tafiyar?�.
“Eh to asan samuna insha ALLAHU ranar laraba, zanyi ƙoƙari na kammala dukkan ɗinkunan mutane dake hannuna, daga nan na damƙa komai a hannun Mudanseer, sannan inason itama Rumanan ta koma makaranta tunda sun kusa fara jarabawa, inaga hakan zai rage mata kaɗaicin�.
“E lallai kayi ƙyan kai, ALLAH yasa haka shine mafi alkairi, duk da ni yanzu karatun bokon nan ma tsoro yake bani, to amma ita rayuwa ba'ai mata kuɗin goro, dan wani ya bijire dalilin hakan bazakai imani cewa kowama zai kasance hakanba, ALLAH ya cigaba da tsare mana ku baki ɗaya, yanzu kafin ka wuce saika sanarma su Iya duk yanda mukai, nima zuwa safiya zan shiga mu tattauna harma dasu Yusha'u akan batun�.
“To Baba nagode ALLAH ya saka da alkairi, ya kara muku lafiya da tsahon kwana�.
Su duka da amin suka amsa. Daga nan Ahmad yay musu sallama ya tafi, sai da ya shiga Sashen su Iya kankanninsa, bayan sun gama É—an wasansu na jika da kaka ya zayyane musu komai, babu wanda ya musa a cikinsu, saima albarka da fatan alkairi da nasara sukaita saka masa, zuwa kusan sha É—aya malam yace ya tashi yaje dare yayi haka nan.
_________________________
Lokacin daya shigo gida Umm-Rumana har tayi barci, hakan yasa bai tadata ba shima ya kimtsa ya kwanta, ya daÉ—e yana tunani kafin barci ya É—aukesa.
Washe gari da safe suna karyawa ya sanarma Umm-Ruman maganar tafiyarsa, duk da tasan ba wata soyayya a tsakaninsu É—an zaman nan da sukai shakuwa ta fara tasiri a garesu, hakanne ya saka duk sai taji babu daÉ—i.
Amma tayi farin ciki da yace zata koma makarantar ta, hakama islamiyya duk zata koma, dan bayason tanama zama a gidan balle ta koyi halinsu maman Ama.
Duk da ya gindaya mata sharaɗin saka dogon hijjab da niƙaf a makarantar hakan bai ɓata ranta ba sam.
A gaba ɗaya kwanakin da suka biyo baya na shirin tafiyar Ahmad ne, yay ƙokarin kammala ayyukan jama'a daya amsa, sannan yaje makarantar su Rumana yay maganar dawowarta da faɗar matsayinta na matar aure a yanzu tunda makarantar ta ƴammatace, hakama islamiyyarsu yaje ya daidaita mata komai, acewarsa bazata shiga ta matan aure ba, mafi yawan makarantun matan sunfi maida hankali ga saida abubuwa da gulmae juna.
Daren da zai tafi ya zaunar da Rumana yay mata Nasiha sosai, tare da kafa mata shariÉ—É—a na zaman gidan, duk kuma abinda takeso ta tambayi Mudanseer zai kawo mata, sannan Fa'iza da Salima zasu dawo nan su ringa tayata kwana.
Taji daÉ—in zancen dawowar su Salima, dan har akan fuskarta sai da yaga haka, amma sai yay tamkar bai fahimceta ba.
Dama tun da daren yay sallama da kowa nasa, iyayensa kakanninsa abokansa dama duk wanda yasan suna huÉ—É—ar mutunci dashi.
Dan haka yana dawowa sallar asuba ya shigo gidan bayan sunyi sallama da mazajen su maman Ama, jakkarsa daya zuba kaya kala uku kawai ya É—auka, dan ko wanka baiyiba, sai kuma Umm-Rumana taji hawaye na zuba mata.
Tsayawa yay kawai yana kallonta, shi kansa baisan shaƙuwa ta shiga har haka a tsakaninsuba sai yau, ya tako a hankali zuwa gabanta, babu tsammani ya jawota jikinsa kawai ya rungume, ƙanƙamesa tayi tana mai fashe masa da sabon kuka, baice komai ba ya shiga bubbuga bayanta a hankali yana mai lallashinta ta hakan, ganin zata ja masa makara sai ya ɗago kanta ya sumbaci goshinta, murya ƙasa-ƙasa cikin kunnenta yace, “Haba Ƙanwata kuma amaryata, kimin addu'a kinji, amma ba kukaba, ALLAH yay miki albarka, insha ALLAHU lokaci zaiyi da zaki mallaki Ahmad da komansa, ke dai ki zama mai yawan haƙuri da yanayinsa na yanzu kawai�.
Ƙara faɗawa jikinsa Rumana tayi tana wani kukan, yay murmushi mai sanyi yana janyeta a jikinsa, taimaka mata yay ta hau saman gado, ya lulluɓa mata bargo tare da ƙara sumbatar goshinta, yace, “Karki manta dani duk runtsi�.
Abinda kawai ya faɗa kenan ya juya ya fita yana ja mata ƙofar.
Lokacin data jiyo ƙarar rufe ƙofar gidan sai ta kuma fashewa da sabon kuka mai cin rai da tsuma zuciya, tasan dai ba soyayya bace a tsakaninsu, amma tanajin wani ɗacin na wannan nisan nasu.