Sashe 7
Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ahmad kam kalaman Samina ne suka É—an sanyaya ransa, ya jingina da bango yana lumshe idanu, shi kansa baisan iya adadin son da yakema Samina ba, bashi da burin daya wuce a yanzu ya mallaketa matsayin matarsa ta aure.
Yayi zurfi a tunani ya tsinkayo muryar Baba na faɗin, “Amadu! Kai Amadu shin barci kakeyine a shagon wai?�.
“A'a baba�. Ahmad ya faɗa da sauri yana miƙewa tsaye.
A ƙofar shagon yaga baba tsaye, “Sannu baba, wani abu kake buƙata?�.
“A'a babu komai, na fitone zan rufe gida saina leƙa ɗakinku naga Mudan ne kawai a kwance, shiyyasa nai tunanin ko kana nan, nakumaji ba ɗinkin kakeba ashe?�.
Shafa kansa yay yana faɗin, “Eh wlhy baba, ɗinkin dai na fara sai kuma allura ta karye na tsaya sakawa, ashe babu mai ƙyau a shagon ma sai mun nemota da safe�.
“To ALLAH ya kaimu, ka rufe kaje ka kwanta hakanan, kanaji jiya sai da ɓarayi suka shiga gidan Alhaji mamman�.
“Wlhy kuwa baba, haka nima nakeji ɗazun da safe, ALLAH ya rufa mana asiri to�.
“Amin ya rabbi� baba ya faɗa yana juyawa gida.
Komawa cikin shagon Ahmad yay ya kashe fitilar sannan yazo ya rufe shagon ya koma cikin gida bayan ya rufe gidan.
Uzirinsa ya shiga bayi yayi, yay alwalar barci daya sabarma kansa kafin ya nufi É—akinsu.
Mudanseer na ɓararraje a katifarsu yana jan nasharin barci, Ahmad ya shinfiɗa abin salla a gefe yana girgiza kai, salla ya tayar yay sha'i da wutiri, bayan ya kammala yay addu'oinsa ya cire rigar jikinsa dan sam baison kwanciya da kaya takura masa sukeyi.
Da ga shi sai boxer ya kwanta, bayan ya tura Mudanseer gefe da ƙyar saboda shima dai ƙatonne masha ALLAH.
Bargonsa yasa ya rufe jikinsa ruf har saman kai, dan komai zafi saiya lulluɓa yake iya kwanciya, sannan komai sanyi saiya cire kaya yake iya barci.
★★★★★★★★
Iya na zaune tsakar gida ta zabga uban tagumi tana jiran taga ta inane Samina zata ɓullo.
Inna mari kuwa babu ruwanta, tuni ta shige ɗaki tai kwanciyarta tana shaƙar barci.
Sai wajen sha biyu da kwata sabon saurayin Samina yay haramar tafiya, ya kalleta ido cikin ido yana wani narkesu a cikin nata.
Hakanne yasaka tsigar jikinta tashi, tai saurin janyewa ƙirjinta na wani irin bugawa, tabbas batajin magana, amma har yanzu rawar kanta bai taɓa sawa ta yarda wani namiji ya taɓa aikata mata wani abu mara ƙyauba koda runguma kuwa, duk da kuwa tana jin sha'awa sosai irin wadda kowacce mace mai lafiya kanji a lokacin da takai shekarunta.
“Babie zan tafi, amma babu abinda zan samu�. Yay maganar cikin raɗa kuma a saitin kunnenta.
Matse jikinta tayi kaɗan, muryarta naɗan rawa tace, “Yallaɓai kamar mi kenan?�.
Wani mugun murmushi ya saki yana sake matso da kansa jikin wuyanta, sai da ya busa mata iska a wuyan kafin ya kai hanci yana shinshinar ƙamshin turarenta, cikin raɗa-raɗa ya sake faɗin, “Komai ma na samu inaso babie�.
Yanda gashin jikinta ke miƙewane yasata ɓalle murfin motar ta fice ba tare data shiryama hakanba, ya bita kallo da idanunsa da suka fara rinewa yana murmushi, “Babie akwai wayo, shikenan na gode ga wannan kiyi amfani dashi wajen kwalliyar gobe�.
Kamar bazata amsaba sai kuma ta ƙyalla ido taga yawan kuɗin, wani irin taji a ranta, tai azamar miƙa masa hannu tana faɗin, “Nagode sosai, amma kamar sunyi yawa ka rage�.
Wata siririyar dariya yayi mai sauti yana dukan sitiyari kaɗan, ya maido kallonsa gareta har sannan da sauran dariyar a fuskarsa, “Babie nawanema waɗanan kuɗin da har kike tunanin sunmiki yawa? Ai ƙyauta bata yawa, yanzunma dan babu kuɗine a jikina shiyyasa, kinga shiga gida sai da safe�.
Kanta kawai ta iya É—aga masa, ta wuce sim-sim kamar wata munafuka.
Sai da yaga ta shige sannan ya tada motar yabar wajen yana dariya abinsa.
Da sauri Iya ta miƙe tana kallon Samina data shigo kamar a tsorace, tai kanta tana faɗin, “Samina kinada hankali kuwa? Tafiya biki shine har sulisin dare?�.
Ƙaramar ajiyar zuciya Samina tayi, taɗan marairaice yanda iya zataji tausayinta,
“Iya wlhy mota muka rasa tun ɗazun, da ƙyarma muka samu wannan ta kawo mu�.
iya batace da ita komaiba, itama sai ta raɓa ta gefenta ta wuce zuwa ɗakin iyar ganin Inna Mari harta rufe ɗakinta ma ita.
Dan gidan nasu É—aki biyune kacal sai runfar girki, É—akin inna mari sai É—akin iya Atine.
Iya dai bata yarda da maganar Samina ba, amma sanin bata da wani ƙarfin iko a gidan sai batace komaiba, ta ɗauki butarta ta zagaya ban ɗaki, koda ta fito ta shiga ɗakinta sai taga Samina na ƙoƙarin cusa abu cikin tsummo karanta na wanki data ƙule da safe zata aikama ƴarta dake aure ta wanke mata, saboda ita bata iyawa.
Nanma kallo ɗaya tai mata ta ɗauke kanta, ta haye gadon ƙarfenta rakuminka ɗaka tai kwanciyarta.
Samina kaÉ—ai taita shigi da fici a tsakar gidan, sai da ta kammala shirin barcinta kafin ta kwanta kusa da iya a kan gado, babu abinda ke mata yawo arai sai haÉ—uwar sabon saurayinta.
Ya haɗu iyakar haɗuwar da zuciyarta ke tabbatar matama yafi mijin novels, da alama kuma sunada kuɗi kamar yanda kullum take mafarkinta akan mijin aurenta, ga ƙyaƙyƙyawar nasaba da itama take masa hasashe. Shin dama marubuta da gaske suke akwai mazan novels a zahiri kenan? A tunaninta koda akwaisu bazasu so ƴaƴan talakawa ba kamar yanda na littafi keyin soyayya da ƴanyan talakawa irinta, sai gashi a dare ɗaya tayi gamo da Ma'aruff. Ta lumshe ido a hankali, wani irin daɗi na kamata, yau gata zata mallaki mijin novel.....
“Yah Ahmad fa?�
Wata zuciya ta ambata mata acan ƙasan ranta, da ƙarfi ta rintse ido tana sama da ƙasa da numfashinta, dan wani irin faduwar gaba taji a ranta, tabbas tanason Ahmad, tanada tabbacin kuma yafi dukkan maza matsayi a ranta, sai dai bashida kwalitis ɗin da take buƙata ga namiji, tabbas tanason namiji ƙyaƙyƙyawa, Ahmad ƙyaƙyƙyawa ne, tanason namiji mai suffa mazan gaske, Ahmad yanadashi, tanason namiji ɗan gayu, Ahmad ba ɗan gayu bane, tanason namiji mai dukiya, Ahmad baya da dukiya, tanason namiji mai nasabar sanannan gida, iyayen Ahmad talakawane babu wanda ya sansu sai danginsu da iya jama'ar layinsu, tana so!, Tana so, tana so da yawa, sai dai Ahmad baida su, bai dasu da yawa.
Yaya zatayi kenan tunda a yanzu tasamu mai dukkan nagartar da ita take buƙata? Zatabar Ahmad ɗinne ta samu *CIKAR BURINTA?* kokuwa zata bar cikar burinta ta anshi *BUƘATAR ZUCIYARTA?......*
“K Samina wai mike damunkine haka?�
Firgigit ta dawo hankalinta, ta juya kwanciyarta tana faɗin, “Babu komaifa Iya, kawai ina lissafine na jarabawar dake tunkaromu kwanan nan, saboda Yah Ahmad yace na dage da karatu�.
“To ai bakiji maganar tashiba, tunda kinyi watsi da ita kin koma bin gidajen bikin da ba tsarankiba, Samina karki ruɗar da kanki, karki bari ƙarya ta lulluɓe ganinki, karki yarda da wasiwasin zuciya, kar dauɗar duniya ta toshe jinki da tunaninki, inba hakaba wlhy zakiyi *GUDU DA WAIWAYE...* ƙarshe kuma zai kawo miki *mugun zato ne* ga duk masu ƙoƙarin ɗora tunaninki akan *keken ɓera*�.
Shirun da Samina taji Iya tayine ya sakata gane ta gama, maganganun Iya sunyi tasiri sosai a ranta, sai dai sheɗaniyar zuciyarta na mata kutse cikin tunanin dake nuni da (A'a), baki ta ciza da ƙarfi kamar zata huda laɓɓanta, gaskiya tana buƙatar dogon tunani akan wannan al'amarin, idanma son samune harda shawara.
Da wannan tunanin ta ingije abun a ranta ta samu barci ya saceta mai cike da mafarkin Ma'aruff.😳🤫
*Washe gari*
Asubar fari Ahmad ya farka tamkar yanda ya saba, da addu'ar tashi barci ya buɗe idanu, ya miƙe zaune yana janye bargonsa tare da yin miƙa mai ɗauke da hamma, sai da yaɗanyi minti biyu a zaunen kafin ya miƙe da ƙyar, fitowa yay daga ɗakin nasu zuwa soro daga shi sai boxer ɗin, ɗan jujjuya jikinsa yay yanda ko ina zai motsa kusan na mintuna biyar, kafin ya koma ɗakin ya ɗauki jallabiyarsa ya saka ya ɗau buta zuwa cikin gida.
Babu wanda ya fito harya shiga bayi ya fito, ya zauna saman É—an dutsin dake tsakar gidan kusa da kwatanniyar ruwan agwaginsa ya fara alwala.
Ayyah ce ta buÉ—e É—akinta ta fito, ya kalleta yana kuskure baki, isowarta kusa dashi yay daidai da zubda ruwan bakinsa,
“Ayyah na kin fito?�
Yay maganar cikin yanayin muryar wanda ya tashi a barci, yana kai ruwa a hancinsa zai shaƙa.
“Eh ɗan albarka, ka tashi lafiya dai ko?�.
Sai da ya face ruwan daya shaƙa ya amsa da “Alhmdllh�.
Bayi ta shige ba tare data sake cewa komaiba, shima ya cigaba da alwalarsa.
Yana kammalawa zai miƙe Ayyah ta fito daga bayi, sai ga Gwaggo ma ta fito daga lungun ɗakin baba.
Itama barka da fitowa yay mata yana nufar hanyar soro.
Kamar yanda ta saba haka ta amsa cikin halin ko in kula.
Ahmad ya yarfama Mudanseer dake jan nashari ruwa a fuska, kamar kullum ya farka a fusace yana ƙun ƙunin faɗin,
“Kai yah Ahmad, kai yah Ahmad, ni ALLAH ka dainamin abunnan, sai kace wani ɗan riƙo kullum kaita tadani da ruwa?�.
“Kai dai ka sani uban ƴan mita, dilla tashi kai alwala mu wuce masjid, saura ka tsaya shegen kashinka na ƙa'ida harmu makara kamar jiya�.
Cikin tuttura baki Mudanseer ya É—auki buta ya fita yana layin barci kamar zai faÉ—i.
Ahmad ya girgiza kansa kawai, sallar raka'atainul fijir ya tada kafin Mudan yagama kalularsa su wuce...........âœðŸ?
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋â¤ï¸NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋â¤ï¸NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋â¤ï¸SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋â¤ï¸NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* â¤ï¸ðŸ’‹NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*