← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 94

Sashe 20

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahmad kuwa koda ya fita dauriya kawai yakeyi, dan bayajin ƙarfin jikinsa sam, ga zuciyarsa har yanzu a cunkushe take, kansa kuma bai daina masa ciwo ba.
A majalisar abokansa ya fara yada zango, ya zauna suka gaisa yana sake musu godiya, sukuma suna tambayarsa jikinsa da amarya.
Yaja kusan minti talatin a wajensu kafin ya miƙe ya ƙarasa gidansu, sashen su Malam ya fara shiga suka gaisa, Malam nata saka masa albarka, hakama tsoffin da aka bari ƴan shema su huɗu da Iya, yaɗan daɗe anan ma, ya fito yana murmushin ƙarfin hali na tsokanarsa da sukeyi irin dai wasan jika da kaka.
Sashen Baba Ilyasu ya shiga, ya gaida matansa sannan ya fito zuwa Sashen su Rumana.
A tsakar gida ya iske Ammi da Mama gaje, kowa na hidimarsa, ya risina ya gaidasu tamkar yanda ya saba, Ammi ce kawai ta amsa masa cikin jin nauyinsa da batayi da, Mama gaje kuwa É—aki ta shige bata amsashiba.
Bai damuba ya miƙe ya fito abinsa.
Ya shiga sashensu, ƴan biki duk sun kama gabansu, sai ƙanwar gwaggo kawai data rage bata wuceba inna Asma'u.
Da Ayyah ya fara cin karo a tsakar gida suna ƙoƙarin kwance zare a ƙafar ɗaya daga agwaginsa ita da Mudan.
Ya ƙarasa gabansu yana faɗin, “Ayyah miya sameta ne?�.
“Wlhy ɗan albarka zarene ya sarƙe ƙafarta, gashi nama lura kamar ƙafar tata ciwo take tun jiya wajen taron nan, to ALLAH baisa nasamu kamata ba suka fice sai yanzu abun ya faɗomin arai, shine nashiga nemanta sai kuma na ganta jikin kejin kajincan a takure kamar wadda aka ɗaure, ashe zarene ya dabai baye ƙafar�.
“To, bai dai ji mata ciwo ba ko?�.
“Eh bai jiba, amma Yaya ina ganin gara a saidasu kawai, kwanan nan naji ana maganar agwagi suna fama da murgwi, na gidan malam kalla sai mutuwa suke suma�. Madan dake maganar ya faɗa idonsa akan Ahmad.
Ahmad yace, “To Mudan saika cigita mai sayen muga idan zasu ɗanyi daraja, amma abar guda biyu, dan nagama wata fara mai yarfin baƙi kamar ƙwai takeyi�.
Ayyah tace, “Ai naga kamarma fa ta fara ƙyanƙyasa da safenan indai ƴar budurwar nance...�
Kafin Ahmad ya bada amsa Inna Asma'u ta fito daga ɗakin Gwaggo riƙe da kayan wankin Gwaggon.
“A'a, ango ɗan gidan Ayyah ne a gidan? Jiki yayi sauƙi kenan?�.
Maida hankali gareta Ahmad yayi, ya taka zuwa inda take yana risinawa ya gaisheta, ta amsa cike da kulawa tana tambayarsa jikinsa.
Ya amsa da cewar da sauƙi.
“To Alhmdllh, ai haka muke son ji, Ina ɗiyar tamu amaryar ƙamshi?�.
Kansa ya kuma sunkuyarwa ya amsa da cewar, “Tana lafiya itama�.
Daga haka ya miƙe ya shiga ɗakin Gwaggo.
Tana zaune Zainab durƙushe gabanta tana cire mata abu a haƙori, sai yarfa hannu take tana kukan shagwaɓa na autanci.
Zama yay yana kallonsu, Gwaggo da sallamarsa kawai ta amsa ta bige hannun Zainab dake riƙe nata, “Idan bazaki tsaya ba tashi kiban waje, ji iskanci saikace ina cire miki rai�.
“ALLAH Gwaggo da Zafi fa� Zainab tai magana tana share hawaye.
“To jeki kicire da kanki mana�.
“Yi haƙuri to zan tsaya ALLAH kuwa� Zainab ta bama Gwaggo amsa.
Ahmad dake kallonsu baice komaiba ya lumshe idanu yana cewa “Ina kwana?�.
Amsawa Gwaggo tayi kamar yanda ta saba masa, sai dai ta tambayi yaya jikinsa da Rumana?.
Yaji daÉ—i sosai, ya amsa mata murya a raunane.
Ita dai sharesa tayi, duk da kuwa É—unbin tausayinsa da ga shi har Rumanar nacin ranta.
Shiru babu wanda ya sake tankama wani, har Gwaggo ta gama cirema Zainab haƙorin makka data sa ya maƙale yaƙi fita, tashi yay ya fito da ga ɗakin yaje ɗakin Ayyah suka gaisa itama.
Sai jero masa tambayoyi take akan jikinsa, yay murmushi saboda ganin yanda damuwa ke kwance a fuskarta, kwanciya yay a gadonta dan wani sabon zazzaɓi yakeji.
Ayyah dake kallonsa ta ɗora hannunta saman goshinsa tana faɗin, “Ɗan albarka wani zazzaɓinne fa? Anya kasha magungunanka?�.
A hankali yace, “Nasha Ayyah, bani bargo sanyi nakeji�.
Babu musu ta É—akko Bargo ta rufa masa, ahaka barci yay awon gaba dashi.

Sai da aka kira sallar zuhur Ayyah ta tashesa dan yayi salla, yay alwala ya fito shi da Mudanseer, a soron gidan sukaci karo da Samina taci kwalliya zata fita, kallo É—aya yaymata ya É—auke idonsa, hakan yasa taja siririn tsaki.
Kasa jurewa Mudan yayi yay saurin kallonta yana cewa, “K da ubanwa kike?�.
Baki ta taɓe tana tauna cingam yay ƙara ƙas-ƙas tai fari da idanu, “Da wanda ya tsargu man....�
Bata kai ƙarsheba ya sauke mata mari, zai ƙara na biyu Ahmad daya juyo ya kallesu ya dakatar dashi da faɗin, “Kai wuce muje mana�.
Samina kuwa sai ta fashe da kuka dafe da kunci, da gudu ta juya cikin gida tana kwalama mama gaje kira.

Ahmad sun dawo salla suka iske marin da Mudan yayma Samina ya zama Hayaniya a gidan, dan kuwa mama gaje hannun Samina ta kamo har sashen su Ahmad akan bazata yarda ba, wai Ahmad yasa Mudan ya daki Samina.
Gwaggo uffan bata ceba, sai Inna Asma'u ce ta tanka, sai ko Ayyah data idar da salla itama ta fito ta taya inna Asma'u, nanko abu ya zama hayaniya Mama gaje nata daddatsa magana wa jama'ar gidan, har Malam da Iya bata bariba, Ammin Rumana kam ai tafi kowa shan Zagi da su Ayyah.
Ahmad ya raɓa ta gefensu ya shige ɗakin Ayyah ya sake kwanciyarsa, ko kallon ɗaya a cikinsu baiyiba.
Hakan da yayi ba ƙaramin ciwo yayma mama Gaje da Samina ba, dan sunso ya tanka su hau kansa.
Mudanseer kam cayay inhar Samina bata bar sashenba wlhy dukan mutuwa zai lakaɗa mata, abinda ya ƙara rura hayaniyar kenan, Gashi su baba basa nan, sai da Iya ta shigo tai magana su Ayyah sukai shiru, Mama Gage kam ai kamar tunzurata akayi, taita zuba tsiya har sai da ta gaji tai shiru dan kanta............✍�

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo

*(13)*

..............Koda Ayyah ta shigo É—aki nasiha tai tayima Ahmad akan wannan sabon lamari da ya shigo musu cikin gida.
Ahmad dake jin zazzaɓi yace, “Karki damu Ayyah, ni wlhy abunsu bai damuna, dan ALLAH kuma kubar biye musu, shima Mudan ɗin zan masa magana yabar shiga harkarta, tunda bata da kunya, duk yanda yake tunanin da da yanzu akwai banbanci�.
“Humm su dai suka banbanta da son zuciyarsu ɗan albarka, indai duniya ce kuma gasu gata nan, wanda ma bai zoba jiransa takeyi, wanda kuma duk yasai rariya yasan zata zubda ruwa, ni lalacewar wannan aurenma tsakaninka da yarinyarnan alkairine, dan kuwa na lura duk halin uwarsu ta kwashe, kuzo ku haihu kanaji kana gani ƴaƴanku su tashi ba tarbiyya, yanzu kuwa ALLAH yay maka sauyin alkairi, gidannan kaf babu mai cewa ga halin Umm-Rumana na banza, hakama uwarta, duk fitinar Gaje tayi ta barta, tunda ita dai ba tanka mata zataiba saboda haƙuri da kawaicin da ALLAH yay mata, dan haka ka kwantar da hankalinka akan yarinyarnan, insha ALLAHU wataran sai kace gwamma da akai hakan�.
Idon Ahmad a lumshe duk yana jiyo nasihar Ayyahn sa, wannan itace shawarar da kowa ke bashi, tare da faɗin gamma da akai, shidai jinsu kawai yakeyi, dan bazasu gane yanda Samina ta mallake dukkan zuciyarsa bane, yasan kozai shekara kwatanta musu irin mugun sonta da yayma zuciyarsa dabai bayi ba fahimta zasuyiba, gaskiya so bai masa adalciba, da yasan a haka wannan soyayyar tasu zata ƙare da ya roƙi ALLAH mutuwa kafin wannan lokacin, kawai dauriya ya keyi, dan mutane karsu kallesa mara zuciya ne kawai, amma ko yanzu Samina ta yarda zata zauna dashi zai saki Umm-Rumana ya sake auren Saminar.

Humm, turƙashi Ahmad, lallai zuciya batai maka adalciba kam.

_________________________

Anayin Sallar la'asar Ayyah tacema Ahmad ya tafi gida ya kwanta, dan su Fa'iza ma sun dawo anbar Rumana ita kaÉ—ai.
Badan ya soba ya fita Sufyan ya kaisa gida yauma a mashin É—in.
Rumana na sharar É—akin Ahmad ya shigo.
Yanda ya shigo kawai yasata gane babu lafiya.
Matsawa tai gefe ya shigo, tai masa sannu.
Hannu kawai ya iya É—aga mata ya haye saman gado hannunsa dafe da kansa ya kwanta.
Cikin damuwa ta kwashe sharar data tattara a ƙofar ɗaki, taje ta zubar ta dawo.
Ya lulluɓe har kansa da bargo, hakan yasa ta zauna ta zuba tagumi kawai tana kallonsa, tausayinsa na sake kamata...
A wannan halin tajiyo sallamar Sufyan, leƙowa tai suka gaisa, yace mata yazone da likitan da zai duba Ahmad.
Izinin shigowa ta basu, koda suka shiga saita fito ƙofar ɗakin ta basu waje.
Zuwa wasu mintuna Sufyan ya leƙo ya kirata, shiga tai ɗakin, saita iske za'a ɗaurama Ahmad ɗin ƙarin ruwane ashe, ƙusa suke nema da zasu rataya ledar ruwan.
“Aiko Yah Sufyan babu ƙusa a ɗakinnan, amma bara na tambayi maman Ama... Ko za'a samu�.
Har zata fito Sufyan yace, “Kinga bartama, bara mugwada ko tsahon zaikai jikin mirror ɗinan�.
Gwadawa sukai sai sukaga yama kai, hakan yasa suka ratayeshi acan, sai da ya fara shiga jikinsa komai yay dai-dai sannan suka fice bayan likitan ya nunama Rumanan yanda zata saka ɗayan idan wannan ya ƙare, dan leda biyu za'a saka masa.
Suna fita sai kawai rumana ta zauna ta hau rusar kuka.
Ahmad na jiyota sama-sama, sai dai baice mata komaiba har barci ya kwashesa mai ƙarfi.
Chapter 20 · 0% Book details