← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 94

Sashe 61

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su Mama gaje sunta jiran suji sakamakon aikinsu amma tsit, sai ma Umm-Ruman da tazo gidan cikin ƙoshin lafiya, hankalinsu ya tashi, a ranar taje ta sanarma Inna mari.
Sai ta hauta da faɗa akan kodai batayi yanda malam ɗin yaceba, tunda dai gashi aikin da yayma Samina yayi ƙyau, dan yanzu haka tana kan cin duniyartane da allura, duk da dai bawai yabar shaye-shayensa bane, randa kuma tsautsayi ya gifta yakan jibgeta, sannan tun randa yaga Rumana da Ahmad kusan kullum saiya mata maganar Umm-Ruman, har cemata yake da yasan da wannan ƙyaƙyƙyawar a gidansu mizaiyi da ita sauran bilicin.
Wannan abu na sosa zuciyar Samina, shiyyasa take sake jin tsanar Rumana a kowacce daƙiƙa ta rayuwarta, bataƙi ace yau ga gawar Umm-Ruman ba a duniya.
Mama gaje dai ta taima Inna mari rantsuwa akan duk tayi yanda yace, hakan yasa suka koma wajensa washe gari.
Bai ɓoyeba ya sanar musu gaskiya akan samun aiki yaci Rumana ko Ahmad abune mai wahalar gaske, danshi Ahmad ma akwai tsari tare dashi tun yana yaro cikin iyayensa sukaima duk yaransu, shiyyasama ko aikin farko da sukai akansa dan karya samo komai a neman kuɗinsa aikin yaƙi tasiri. shima sai daga baya ya fahimci hakan. Umm-Ruman kuwa bata wasa da ibadar ALLAH, tana cika kowacce salla ta farilla, sannan bata bari lokacinta ya shige akan ganganci sai dai kuskure.
Yace, “Kunsan ba aikin dake bamu wahala kamar na mutumin da bai wasa da salla, mukan daɗe bamuci galaba a kansaba, sai dai idan UBANGIJI ya ƙaddara hakan arayuwarsa. Yanzu gashi matsala ɗaya bata jini saboda ciki, amma da ace tanai sai mubi wannan hanyar musamu nasara. Idan kuma zakuyi haƙuri harta haihune to, randa ta haihuma zamu iya salwantar da yaron ita kuma aikinmu ya shiga jikinta�.
Shiru su mama gaje sukai suna nazarin maganarsa, Inna mari ta katse musu tunani da faɗin, “Babu damuwa mun yarda kawai malam, amma babu yanda za'ai kafin sannan aɗan saka rashin jituwa tsakaninta da mijin nata?�.
Dariya malam yayi yana faɗin, “Badai za'a barta ta hutaba kenan? To zan gwada na gani idan za'a dace, amma ita ƴar uwar tata Samina ta kwantar da hankalinta ta shiga jikinta sosai, ta wannan hanyarne kawai zamu san komai daga gareta har watan cikin nata�.
“To shikenan Malam wannan ba matsala bane zamu sanar mata�.
Sun masa sallama suka taso suka taho gida suna ƙara jin haushin Ammi da Rumana da basu tsare musu komai a rayuwa ba.

★_★“★_★”_�

Da ƙyar su mama gaje suka shawo kan Samina akan shiga jikin Umm-Ruman, dan da da farko taƙi, yanda ta tsani Umm-Ruman ai ko maganarta ta tsana a mata balle har akai ga ta raɓeta, ita yanzu hakama ko za'a kasheta bazata iya gane gidan da aka kaita kafin Rumanan ba.
Ta dai fara karɓar Number Rumana ɗin wajen yayarta Bintu da hakan ya ɗaurema kai, haka kawai hankalinta ya kasa kwanciya da ƴar uwar tata akan amsar wannan Number ta Rumana.
Da farko ma kamar karta bata, sai taga idanma bata batanba ai zataje ta samune wajen wani.

Abinda kuma su mama gaje basu saniba a yanzu duk motsinsu Ammi na hankalce dasu, sannan ta kuma dagewa tuƙuru wajen jefan ƴarta da addu'oi harma da cikin jikinta data lura shi ya tsone musu idanu.

_________________________________

Haka rayuwa ta cigaba da turawa, kwanaki na shuÉ—ewa suna zama satittika, yau da gobe kayan ALLAH har takai cikin Umm-Ruman ya fara fitowa sosai, danma dai cikin fari dama ba wani girma ya cikaba, sannan gata doguwa kuma masha ALLAH.
Ahmad ma dai ta ɓangarensa komai sai hamdala, dan kuwa ya fara zuwa aiki, gefe kuma ga kayan kasuwarsa sun haɗa hannu da Nura, shima duk ranar weekend yakanje kasuwa.
Ya samu ya sake aiko da kuÉ—in hayarsu, dukda ma tunaninsa ya fara bashi É—akko Umm-Rumana su taho nan, dan yanzu bazai dinga samun lokaci mai yawaba na zuwa gida ya jima kamar da.
A hakama da ƙyar ya fisge a wannan karon yazo gidan akan zaiyi sati ɗaya kacal.
Kowa yaga Ahmad yasan rayuwa ta fara canja masa sosai, musamman yanda yay ɓul-ɓul dashi ga alamun kwanciyar hankali na musamman tattare dashi, ya ƙara zama Gentleman na gaske, ga gayu tamkar ba shine yay shushaina ba da talla a titi.
Ita kanta Umm-Ruman bata iya ɗauke kanta daga garesa, dan gaba ɗaya ya rikiɗe ya canja mata, sunsha soyayyarsu mai tsafta tare da tattalin da yake nuna mata saboda tausayinta da yakeji a ransa na cikin jikinta, a ganinsama tayi ƙarama da ɗaukar cikin, amma yasan UBANGIJIN daya basu shine zai bata ikon haihuwa lafiya.
Yama su baba maganar tafiya da Rumana amma sai sukace ba yanzuba, ya bari ta haihu dan bazai yuwu ace sun tafi tana cikin wannan halin hakaba, balle cikin nama fari, kowa zaiso ta haihu a gida cikin danginta kodan itama ta samu kulawa.
Baiyi musu da suba ya haƙura duk da bai soba, ya tattara ya koma bayan randa ya cika sati guda.
A wannan tafiyarma sai da tai masa kuka, haka dai ya gudu ya barta.

Tun daga sannan duk ƙarshen wata sai Ahmad yazo gida, wani lokacin yay kwana uku, ko huɗu harma sati yakanyi.
Duk zuwan da yay kuma saisun tsinci kayan haihuwa sun ajiye a gidan yaya Maryam, hakan yasa Æ´an gidansu Rumana su Maman Ama ke dariyar gatsatsa, wai gadai Ahmad ya canja amma su basuga wani canjiba, koÉ—an kayan haihuwar da akan siya a yadda na haihuwar fari basu ganiba ga Ahmad.
Bai iya komaiba sai zaryar dawowa gida saboda fitina na cinsa.
(Kusan har yanzu basusan ya samu aiki ba ƙabayen😹).

🤦🏻‍♀kuji masifa, bayan da sunce masa lagwani😏😂🤣.

Duk da Umm-Ruman takan jisu wani lokaci bata ko kallonsu, ita dai fatanta a kullum ALLAH ya bata ikon zama dasu da zuciya ɗaya, ya kuma hanata yimusu ƙƴashi ko hassada a komansu.
Duk da wannan abun da suke mata haka zaki ganta da ɗiyar Kausar maƙale wani lokacin, dukda tana fama da kanta har goyata take su fita cikin gari wani lokacin, ta kama hannun Amatullah ga Surayya babyn Kausar kuma a baya.
Akwai randa taje gidansu Ayyah taita mata faÉ—a akan wannan gangancin goya Surayyan, takuma tabbatar mata karta sake É—aukama kanta wannan rigimar, ta bari har ALLAH ya sauketa lafiya sai tayi koma miye.
To tunma daga ranarne taɗan ɗaga ƙafa da goya Surayyan, amma hakan baisa tayi fari a idon Kausar ba balle taji kunyar zama yi da ita.
Tun farko dama bata saka lamarinsu a rantaba balle yanzunma ya dameta, harkokin gabanta kawai take da ƴar sana'arta data samu karɓuwa sosai, sai ko rainon cikinta da a kullum take addu'ar fitowarsa duniya lafiya.

___________________________________

Daga Samina har mama gaje sun saka a ransu aikin da Ahmad ya samu ba wani na kirki baneba, harda cewa ƙilama ƙaryane anayine kawai dansu, rashin ɗaukar abun da muhimmanci ya sakasu ƙin saka abun a ransu, sai cikin Umm-Ruman ne kawai yafi zame musu damuwa.

Ranar wata juma'a Samina ta shirya zuwa gidan Umm-Rumana kamar yanda malaminsu ya bata Umarnin ta fara shige mata tundaga sannan, dan cikin Umm-Ruman ya shiga watan haihuwa.
Taci adonta cikin kaya na alfarma, dan kuwa rantsatstsar doguwar rigace da taji adon duwatsu ta saka, komai nata dai ya kasance na matan manya, dan zuwa yanzu ƙawayen data ƙara masu rawar kai irinta sun sake wayar da ita fiye ma da da, ɗaukar kanta take sama sosai, balle gashi Ma'aruff yana a tafin hannunta ne sai yanda takeso za'ayi, uwarsa kanta da ƴan uwansa duk ta bi dasu babu mai mata kallon banza yanzun, shiyyasa take musu rashin mutuncin da duk suma sukai mata a baya, matsalarta dai kawai cikin datake ta zuba ido ya shiga saboda Ma'aruff ya daina bata magani yanzu bulum kakeji babu ko alamarsa, taje asibiti likita ya tabbatar mata cewar lafiyarta ƙalau, abin na tada mata hankali, dan babu abinda tafi buƙata sama da ɗaukar cikin ma'aruff a yanzu, a ganinta haihuwar da zatai dashine zai ƙara mata lasisin mallakar dukiyarsa, dan mahaifinsu ya rasu tuni, kuma ma'aruff ɗinne kaɗai namiji a gidansu, shiyyasa ya tashi cikin gata bana wasaba, duk dukiyar ƙannensa tana wajensa shi yake juya musu, dan Company ɗin ba nasa bane shi kaɗai, shaye-shayen da yakene ya saka duk yarinyar da ya nema auren ke lalacewa, ga neman mata ko bunsuru ya shafa masa lafiya.
Sau biyu ana saka masa ranar aure amma yana lalacewa saboda rashin mutuncinsa, wasu kuma saiya gama lalata musu rayuwa saiya gudu bazasu sake ganinsa ba, idan ma sunsan inda yaken kosun kawo ƙara gidansu a banza, mahaifiyarsa ca take ƙaryane, sharri akaima yaronta baya shan giya, abinda yasa bata saniba ma'aruff baya shan giya sai dare, dayasha kuma gida yake dawowa, da safe kafin ya fita ta sakeshi, to inba tare kake dashiba har barci bazaka san yanayiba, gashi komai da taku yake kayansa, hakan yasa ko ita Saminar bata taɓa saniba.
Sannan ita kanta Samina da shirin yaudararta yaje, daya samu abinda yakeso ya gudu, sai dai kuma su Mama gaje sun masa DAURIN GORO bai saniba, dan saka malam sukai yay ram dashi a hannu akan tilas ya auri Samina.
ALLAH kuma sai ya amsa musu akayi auren dama yake da alamar tambaya saboda cikin da taje dashi a jikinta.
Chapter 61 · 0% Book details