← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 94

Sashe 80

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Lamari ya sake caɓewa sosai a gidansu Samina ko nace gidan Ma'aruff, dan tunda Mufida ta haihu komai ya ƙara canja salon taku.
Irin shagalin da akai wajen wannan haihuwa da ɓarnar kuɗin da Ma'aruff yayi abin har ba'a cewa komai.
Dan mahaifiyar ma'aruff kanta lamarin ya girgizata, hakama ƴan uwansa tunda kowa yasan ba haƙƙinsa bane shi kaɗai kuɗin da yake ɓaragaza dasu, amma saboda son ƙuntatama Samina sai basu nunaba balle zance ya fito, kowa ya haɗiye abun a ransa, dan dai kam tabbas Mufida bawai tabar Ma'aruff hakanan bane duk da kuwa mahaifiyarsa ta tsaya tsayin daka akan sai ya auri mufidan.
Rabonda Ahmad ya shigo sashen Samina da ƙudirin sauke haƙƙinta harta manta watan, dukta fige, dan ko lokacin bikin su Fa'iza a wannan tashin hankalin tajesa, to bayanma bikinsu Fa'izar sai abubuwa suka kuma taɓarɓarewa.
Dan ganin Ahmad a wajen taron bukinnan ya dawo mata da sabuwar zazzafar ƙaunar da take masa, wanda kwaɗayi da son duniya ya danneta a wancan lokacin, kullum shine a mafarkinta, shine tunaninta, saboda shi duk dare saitayi kuka mai yawan gaske, ga tashin hankalin gidan miji, gadai ci da sha amma babu miji babu farinciki babu ƙauna daga ahalinsa, ya kuma hana kowa zuwa gidan a ƙawayenta, wannan yasa ta haɗu ta kuma lalacewa, ko gidansu batason zuwa, indai ta fita iyakarta gidan inna mari, acan suke haɗuwa da mama gaje, mutanen gida kuwa duk sun ɗauka ko laulayin ciki Samina keyi shiyyasa ta ɗaukema gidan ƙafa, amma kuma basuji wani labariba har tsawon watannin da zuciya zata iya ɗauka wannan hasashe.
Ta amshi Number Ahmad, daga baya kuma sai aka sanar mata ai bamaya ƙasar, dan ita batasan zai tafi saudia ba, mama gaje bata sanar mataba gudun kar ranta ya ɓaci😹.
Babu kalar ƙulle-ƙullen da basuyiba amma asirin nasu yabar tasiri a halin yanzu, sun rasa a ina matsalar takene?.
Basusan matsalarsu itace Mufida ba, dan itama sai da tai duk wani yunƙurin daƙilesu kafin ta kafa nata shaiɗancin tsubbun ga Ma'aruff da ahalinsa.

A yanzu babban tashin hankalinta shine Ma'aruff kullum cikin zarginta yake akan wai maza takebi, dan watannin daya ɗauka baiyi tarayya da itaba bazai yuwu ta iya haƙuriba tunda yasanta ita karyace.
Tamasa rantsuwa yafi shurin masaƙi amma yaki saurarenta, abinda kuma bai saniba komai yawan bukata na ɗan adam inhar yana cikin tashin hankali bayama tuna wata sha'awa, musasaman ma mu mata da muke da rauni, ƙaramin ɓacin rai kan gusar da sha'warmu muji bama bukatar namiji.
Wasa-wasa abu ya fara tsamari tsakaninta dashi akan wannan magana, to abune lamari na kwakwalwar É—an giya da babu Mathematics sam aciki, balle ga sammu na É—awainiya da rayuwarsa.
Yau da su Rumana ke cika wattanni biyu da tafiya rikici ya ɓalle tsakanin Samina da Ma'aruff akan saita faɗa masa da wa suke cin amanar aurensa, dan da daddare ya shigo gidan a make Mufida ta hanashi shiga sashenta shine ya nufo nan, ya iske Samina nata sambatu akan begen Ahmad.
To da yake a make Ma'aruff yake sai ƙwalwar kansa ta bashi wani abu daban, tun a daren ya fara dukanta sai dai abun bai nisaba ta gudu bayi ta ɓuya, shine ALLAH ya taƙaita abun.
Da safe kuma bata fitoba har yabar gidan, ya kumaje ya yini da abun a ransa ko a office É—inma, shinefa yana dawowa abinci kawai yaci a sashen Mufida yanufo sashen Saminar É—auke da yarinyarsa da Mufida ta haifa masa.
Sai kuma gashi ya taki babbar sa'ar isketa a falo kwance tana tunanin Ahmad da ayanzu ya zamemata abokin rayuwa.
Ganin yana cikin hankalinsa yasa tai tsamanin babu abinda zai faru, sai dai ina, batasan a yanzunnema zai farunba.
Basu yarda ta É—aukar musu yarinya, dan haka yanzuma kallo É—aya tai musu shida Æ´ar tashi ta É—auke kanta, sai dai tambayar daya jeho mata makamanciyar ta jiya ya sata tashi zaune a rikice.
Tun ana zancen da fatar baki har takai ya ajiye yarinyar ya maƙure Samina, dan ya tabbatar mata idan bata sanar masa dawa take tarayyaba sai ya halakata.
Tashin hankalin da Samina take cikine ya sata birkice masa itama, yana kai mata duka tana ramawa, kafin kace kwabo sun kaure.
Sosai hayaniyarsu ta kaure gidan, a kuma lokacin ne Afrah ta rarrafa zuwa ga wata kwalbar ruwan lalle da Samina ta ajiye gefen kujera ta É—auka ta saka a baki, sunata danben bala'i itako tana wasa da ita har ALLAH ya bata nasarar buÉ—ewa ta juye ruwan cikin bakinta ta shanye.

Mufida duk tana sashenta tanajin wannan bala'i, sai kwasar dariya takeyi, daga ƙarshe ta fito da nufin zuwa tasha kallon zahiri baji da kunneba, sai dai ta iske kallon zahiri kuwa wanda batai zatoba ko tsammani.
Dan daidai baby Afrah na shure-shuren mutuwa ne ga dafara na fita a bakinta fara tas ta kumfa, ihun da ya dawo da hankalin Ma'aruff da Samina ta ƙwala tana nufar Afrah, suma duk sai suka kalli wajen.
Ma'aruff shima ya isa da gudu suna jijjiga Afrah tare da Mufida, daga ƙarshe dai ya fisge yarinyar ya fita da gudu da ita waje, Mufida da Samina suka take masa baya a matukar tashin hankali.

*_RUBUTACCIYAR ƘADDARA_*

Tabbas wannan yanayi ya cancanci a kirashi da suna Rubutacciyar ƙaddarar Samina, dan kuwa bayan ankai Afrah Asibiti, likitoci na amsarta mufida na kuka ta kira ƴan sanda akan bazata yardaba Samina ce tai yunƙurin kashe mata ɗiya, mai makon Ma'aruff da yasan gaskiyar lamari ya hanata, tunda dagashi har Samina basusan mi Afrah taci ba ko yay sanadin shigarta wannan hali, sai yay shiru Mufida ta kira ƴan sandan.
Samina na gida cikin matuƙar tashin hankali, dan basu bari ta biyosu ba, bayan tafiyarsune kuma ta fahimci abinda Afrah tasha ɗin.
Ƙaddarar dake biye da ita ta sakata ɗauke kwalbar ruwan lallen tasa a shara tare da goge wajen wai dan kar Mufida ta juya abun kota zargeta🤦🏻‍♀.
Batasan hakan datai shine babban kuskuren data tafkaba a rayuwarta kuwa.
Dan tana kammalawa babu jimawa sai ga Mufida da Æ´an sanda, basu wani tsaya jan zanceba suka wuce da Samina tana kuka da rantsuwa akan ita ba ita ta aikataba.
Sai dai sunƙi saurarenta, haka suka wuce da ita station.
Kafin aÉ—auki dogon lokaci kuma magana ta fara baje dangi, har gidansu Samina takai.
Babu kuma mai faɗin gaskiyar lamari sai cewa ake Samina ta bama ɗiyar kishiyarta fiya-fiya ta mutu saboda ita tana baƙin cikin bata haihuba.

A asibiti kuma babu wani bayani dangane da jikin Afrah daga likitoci, sunata dai shigi da fici ɗakin da aka kwantar da yarinyar saboda Adam da ya tsaya tsayin daka akan komi...............✍�

_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_

_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_

Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻

............Komai ya hargitse, gaskiya ta gaza fita a bakunan mutane, kowanne furuci ya fito na zargin Samina ne kai tsaye.
Ca ake bata ɗauki ranta a bakin komaiba ita kanta dama, dan ta taɓa shan fiya-fiyan shiyyasa yanzu ma ta bama ƴar mijinta.
Mama gaje ta koma tamkar ƙaramar mahaukaciya, hakama inna mari, ga baba Yusha'u yace babu hannunsa a ciki, Babansu Ahmad da Mudanseer ne keta shigi da fici station ɗin amma ko ganin Samina an hana misu, dan ƴan sanda sunci kuɗi sunyi haniƙan wajen Mufida data sake ɗaure komai da wasu zantuttukan, Ma'aruff kuma ya gaza kare Samina ko sau ɗaya.
Afrah bata mutuba, amma yarinyar na cikin mawuyacin hali, harma takai sai an mata aiki a ciki saboda ɓannar da ruwan lallen yay mata a wani sashe na kayan hanjinta.
Yanzu ana maganar shiga kotune, dan haka akace su baba suje kawai su nema lauya😢.

*_YARO TSAYA MATSAYINKA, KADA ZANCEN ƳAN DUNIYA YA RUƊEKA_*
Chapter 80 · 0% Book details