← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 94

Sashe 64

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

..............Koda Ahmad ya gama gaisawa da mutan gida da ƙannensa harma da iyayensa, yaci ya ƙoshi Ayyah tai masa maganar tafiya can gidan sai ya ɓata fuska.
Tace, “Tofa ɗan albarka yaya dai?�.
“Nifa Ayyah ni kaɗai zan koma can yanzu? Duk kowa yana nan ni sai a wareni?�.
Kasa daurewa Ayyah tayi ta kwashe da dariya, Rumana ma ƙasa tai da kanta tanayin tata, hakama Zainab da suka faɗa cikin ɗaki, dan bazasuyi a gaban saba tunda sunsan sauran.
Harara yaketa zubama Umm-Ruman yana sake kumbura fuska.
Ayyah tace, “To yanzu ya kakeso ayi kenan?�.
“Nima Ayyah ban saniba dai, ki kawo shawara�.
Ayyah tace, “Ga shawarar na kawo nace katafi gida ka huta ka kamamin shagwaɓa�.
Yace, “Toni Ayyah tsorofa nakeji, ni kaɗai a ɗakin ai sai wani abu ya cinyeni kafin safiya�.
Ba Ayyah ba hatta Gwaggo dake ta ayyukanta bata saka musu baki sai da tai murmushi tana girgiza kai, yayta mazurai wa yaran gidan da shan toka, amma idan yana gaban Ayyah jinsa yake tamkar wani ƙaramin yaro.
Zama Ayyah tai tana lallaɓa Ahmad, dan tuni su Fa'iza suka tafi kimtsa masa ɗakin, aiko da ƙyar ya yarda ya tafi.
Rumana ta sauke ajiyar zuciya tana maijin ƙaunarsa har can ƙasan ranta.

★★★★★★

Koda Ahmad ya isa gida ya iske su Salima sun gama komai suna wanke masa bayi ne da duk ya ƙazance, saboda su Maman Ama sai sun gadama suke wankewa, amma fa ba kullum bama saboda kowa na ganin ƙyashin ya gyara wani ya amfana, dai dai da tsakar gidan yasan Rumana bata gidan, dan duk ya fitta hayyacinsa, wani lokacinma Ahmad suke sakawa sharar ɗan ƙarami dashi.
Su Kausar dai mamakin yanda Ahmad kullum ya dawo sai kaga sabon canji tattare dashi sukeyi, harsu fa'iza suka wuce ya shiga wanka basu bar satar kallonsa ba.
Shi baima san sunaiba, saurin kimtsawa yay dan gidan duk babu daÉ—i yakejinsa, jinsa yake kamar wani maraya da baida kowa, gidan ya masa girma saboda rashin Gwal É—insa a ciki.
Sauri-sauri ya gama shiryawa ya sake fitowa, lokacin anata kiran sallar magriba.

Bayan anyi sallar isha'i Rumana na kwance tana kallo a waya bisa gadon Ayyah ƙarami na ƙarfe kawai sai ganinsa tai ya shigo ɗakin da sallama.
Da mamaki ta ajiye wayar ta yunƙura ta tashi zaune tana kallonsa, Yaya dama baka tafiba?.
Zama yay a bakin gadon yana harararta, “Oh baƙyason ganina ne?�.
“Taɓ ni na isa�.
Yace, “Ina su Ayyah?�.
“Su Ayyah sunje gidan Inna mariya wai bata da lafiya, dama da yamma sukaso zuwa dubata sai kuma ka dawo, shine sukace tunda sunyi niyya gwara suje dubata a darennan dan Sadiqu na nan gidan malam ne ya tafi kaisu�.
Gaba ɗayansa ya juyo yana kallonta, yace, “Tun yaushe suka wuce?�.
Rumana bata fahimci bin ƙwanƙwanton maganarba tace, “Yaya yanzun nanfa, dan namayi mamaki da baku haɗu dasu a ƙofar gida ba�.
Wani nannauyan numfashi taji ya sauke, yace, “Su fa'iza fa?�.
“Suma yanzu suka wuce makarantar dare, kusan tarema suka fita dasu Gwaggon�.
Shiru yay yana ƙiyasta nisan inda su Gwaggo suka tafi da lokacin da zasu iya ɗauke. Ita dai Umm-Ruman kallon mamaki taketa masa, gani tai kawai ya miƙe ya kama hannunta yana fadin,
“Kinga sakko muje kiga wani abu Gwal ɗina�.
“Wani abu kuma Yaya a ina?�.
Bai bata amsaba ya taimaka mata ta sakko, haka ya jawo hannunta suka shige É—akinsu Fa'iza, sam bata kawo komai a rantaba, ta daiga ya sakama É—aki sakata, dama É—akin babu fitila da wayarsa ya haska.
Yaja hannunta suka hau saman katifar, danma karta kawo masa togaciya yasha toka.
Tunda ya kashe fitilar wayar tasa kuma sai tsoro ya kamata, tace,
“Yaya wai lafiya?�.
“Shiiii!� ya faɗa yana kwantota jikinsa, da ɗora fuskarsa akan dokin wuyanta.
Duk yanda taso hanashi ta kasa, bawai itama bata buƙatar inda taga ya dosa bane, a'a kunya takeji da tsoron kar wani ya shigo gidan, tunda Abu da Mudan da Baba duk suna a anguwar, sannan su Ayyah ma ai zasu iya dawowa, kokuma wani a cikin gidan, musamman ma Iya da bata gajiya da leƙowa dubata, garama su Fa'iza da sauran lokaci.
Duk salon da yasan zai mata jikinta yay laushi shi yayta bi, sai da yaga tayi tuɓus ta miƙa wuya sannan.
Bakinta na rawa tace, “Yah Ahmad ba gidanmu bane fa nan, dan ALLAH kayi haƙuri....�
Muryarsa a sheƙe yace, “Idan nayi haƙurin kina da maganin bani ne na samu nutsuwa?�.
Kanta ta girgiza masa, ta sake buÉ—e baki zata masa bayanin da zai fahimta, ya rufe bakin gaba É—aya ma........

__________________________________

Tamkar jira, Ahmad na samun nutsuwa ciwo ya tashi daga Umm-Ruman, ta fara da kukan bayanta, mararta.
Saurin saka kayansa yayi itama ya maida mata nata duk ya rikice saboda kukan da takeyi.
Da ƙyar ya samu suka fito daga ɗakin tanata yarfa hannu da ƙara ƙarfin kukanta, dole dai ɗakin Ayyah ya maidata yay saurin nufar sashen Ayyah ya faɗa mata akan taje shikuma ya samo mota su tafi asibiti.
Amma sai Iya ta tsaidashi, a tare suka koma sashen nasu, lokacin sosai Rumana ma ta gama galabaita, dan har wani ruwa ya fashe mata, sai kiran sunan Yah Ahmad takeyi da Ammin ta.
Gabanta ya duƙa ya riƙe hannunta shima muryarsa na rawa yake faɗin, “Kinganni nan kusa dake Gwal ɗina, kiyi haƙuri yanzu zan samo mota muje asibiti kinji ko�.
Cikin kuka rurus take É—aga masa kai alamar to.
Iya ta korashi waje dan ta kula haihuwace gadan-gadan ta tahoma Rumana.
Koda Ahmad ya fito jingina yay da bango ya lumshe idanu, ji yake kamar ya taya Babie R ɗinsa kuka, dan sosai kukanta ke sukarsa, gani yake laifinsa ne, da bai kusanceta ba ƙila hakan da bai faru ba, shikuma kasa jurewa yay, dan a jigace yake da son jinta a jikinsa.
Dai-dai nan su Ayyah suka shigo gidan, duk sai da gabansu ya faÉ—i ganinsa a wajen, dan kukan da Rumana keyi idan ba matsowa kai kusaba ba wai zaka jita bane, zuwa yanzu ma ta bar kukan sai nishi da Iya ke cewa tayi.

Kafinma su Ayyah su sami damar tambayarsa suka jiyo nishin Rumana, hakanne ya tabbatar musu haihuwace, jin iya ce a ciki sai Ayyah ta shiga danta taimaka mata, Gwaggo kuma ta fara yunƙurin ɗora ruwan wanka bayan ta shiga ɗakin baba ta ɗakko wasu sassaƙen magunguna.
Kaf gidan babu wanda yasan hidimar da ake sai iya su, ko Abu da yake baida man kai daya shigo cin abinci bai fahimta ba, ya ga dai Ahmad sai kai kawo yake a tsakar wajen cikin damuwa, da yake ba wasa yake da suba sai bai iya ya tambayesa ko lafiya ba?.
Cikin amincin ALLAH mai rahma mai jinƙai ALLAH ya sauki Umm-Ruman lafiya bayan baƙar wahalar data gama sha, duk da a hakanma su Iya sunce haihuwar tazo mata da sauƙi, ballema tana da dauriya, dan bata irin ihun nan kamar ɗiyan maguzawa.
Tunda Ahmad yaji kukan jinjiri ya sauke wani nannauyan numfashi da har Gwaggo sai da ta jiyosa ta kallesa, duk da itama ta sauke ajiyar zuciya, tausayi ya bata daga shi har Umm-Ruman É—in dake filin daga.
Ayyah ta fito ta É—auki abu ta koma, tana cema Ahmad ya samu waje ya zauna tunda an sauka lafiya ai.
Nanma ya sake samun nutsuwa, sai bin gwaggo da kallo yake yaga ko zaiga yanda zata nuna, sai dai bai fahimci komaiba daga fuskarta, ta dai É—auka buta tayi alwala ta shige É—aki abinta.
Kansa ya duƙar ƙasa yanata cigaba da jeroma ubangiji godiya da kirari akan wannan ƙyauta da yay masa.

A haka su Fa'iza suka shigo gidan suka iskesa, sannu duk sukai masa, a mamakinsu sai sukaga fuskarsa washe da fara'a, su dai É—akinsu suka shiga dansu ajiye littatafan hannunsu da hijjabai.
Sadiya tace, “Oh ni waye yayma katifarnan haka? Zainab halan kece?�.
Zainab sarkin tsiwa tace, “Kai Yaya Sadiya, ALLAH zai sakamin dan wlhy bani baceba�.
Duka Sadiya ta kai mata, ita kuma ta fita da gudu zuwa ɗakin Gwaggo dan takai ƙara.
Gwaggo dake ƙoƙarin fitowa sukaci karo da Zainab, tace, “K kuma lafiya?�.
“Gwaggo ba yaya Sadiya bace, wai dan mun dawo munga an hargitsa katifa shine wai tace nice, kuma wlhy ni bani bace nama rigasu tafiya makaranta......�
Kafin Gwaggo tace wani abu Sadiya ta fito daga ɗakin tana faɗin, “Nifa Gwaggo daga na tambayeta ne, maimakon tace ba ita bace shine harda wani cewa ALLAH zai saka mata na mata sharri ma kenan?, bakigafa yanda akaima katifarba kaca-kaca kamar wani ya hau yay danbe�.
Fa'iza tace, “ƙilama aljanune wlhy Gwaggo, ni dai yau ban kwana a ɗakin nan�.
Ahmad duk yana zaune yana saurarensu, amma ko kai bai É—ago ya kallesu ba, balle ya nuna yasan wanda yayi.
Gwaggo da batace uffanba ta nufi É—akin dan ta gani, dai-dai nan kukan É—an jariri ya kuma cika sashen.
A take su Fa'iza duk suka fiddo idanu waje alamun mamaki, har haɗa baki suke wajen ambaton, “gwaggo Rumana ta haihu ne?�.
Da hannu tai musu nuni da suyi shiru, aiko sai kowacce tai ɓam da bakinta amma tsagwaron murna ya mamayesu, suka kama tsalle tare da afkawa ɗakin suka haye katifar da suke cewa sunajin tsoro, kota kan Gwaggo dake ƙarema katifar kallo basu biba.
Itama sai tai fitowarta bata tanka musuba.
Chapter 64 · 0% Book details