Sashe 74
Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
.............Su Umm-Ruman nada watanni na bakwai a port wani abin farin ciki da cigaba ya sake riskarsu, dan kuwa dai karatun da Ahmad keta ƙoƙarin komawa ya samu gurbin yinsa a ƙasar Saudi-arebia.
Cikin tsantsar farin ciki ya iso gidan, lokacin Rumana na kicin tana girkin dare, Zainab na Assignment ɗin makaranta a falo, sai Haysam da suketa rigima saboda rarrafe da yake yanason hanata abinda take, idan ta janye buks ɗinta sai ya haye mata saman wuya yana ƴar ƙara ta wasa da akasan yara dashi.
Rumana na jiyosu daga kicin ita dai.
Zainab ta amsama yayan nata sallamarsa tana masa sannu da zuwa.
Amsa wa yay da fara'ar data bata mamaki sosai, sallamar Ahmad ɗin ta saka Haysam dake riƙe da kayan wasansa da Zainab ta bashi dan ya barta shima rarrafawa da hanzarinsa ya nufesa, kasancewarsu basu da yawa a gidan, kuma ba wani waje ake fita da shiba yasa duk yasan ƴan gidansu, ko Zainab ta dawo makaranta haka yake mata, gashi da wayo masha ALLAH, bazaka taɓa ɗauka watanninsa taraba kenan, har tafiya yaɗan fara gwadawa, sai dai tsoro kan hanashi miƙewa shi kaɗai sai ya dafa kujera ko bango.
Ahmad ya ajiye takardun hannunsa ya ɗaukesa yana murmushi, “Oh my king yoyoyo�. Yay maganar da sumbatar kuncin yaron, zama yay a kujera Haysam na jikinsa, ya kalli Zainab yana faɗin, “Ina auntyn taki?�.
Zainab dake ƙoƙarin miƙewa tace, “Yaya tana kicin, bara na kirata�.
Wasa ya cigaba da yima Haysam, Zainab kuma ta nufi kicin kiran Rumana sai ma sukaci karo a hanya, dan dama Rumanan na jiyosu, kawai tana dai mamakin miya maidosa gida da wuri haka?.
Cike da shauƙi Ahmad ke kallonta, inba an faɗa makaba bazaka taɓa ɗauka itace ta haifi Haysam ba, musamman ma yanzu da Port ɗin ta kama jikinta, ta sake kyau dayin dumur-dumur abinta alamun samuwar kwanciyar hankali mai inganci.
Hannunsa ta taɓa, hakan yasashi kawo numfashi a hankali.
Ta ɗanyi murmushi tana faɗin, “Wannan kallonfa Zumana?�.
Sashin da Zainab take yakai dubansa, duk da dai yasan da wahala ace tana nan dan inhar yana falon bata zama sai indan sune suka kirata.
Umm-Ruman ma inda ya kalla tabi da kallo, sai kuma ta maido idonta kansa, dai-dai shima ya juyo idanunsu suka shige cikin na juna.
Cikin tare numfashinta yace, “Gwal ɗina kodai na sake yin ajiya ne?�.
Babu shiri ta waro idanu waje da faɗin, “Ajiya kuma Yaya? A ina?�.
Sai da ya shanye ruwan data miƙa masa sannan ya bata amsa yana nuna Haysam dake wasa da kwalliyar gaban rigarsa.
“Ƙanuwar Haysam mana�.
“Yaya rufamin asiri na mutu maza su kaini ba mataba, yaron da ko shekara baiyiba�.
Murmushi yayi yana shafa kan Haysam, yace, “Matsoraciya kawai, baki tambayeni na dawo da wuri ba?�.
“Wlhy da wannan mamakin na fito My boss, sai ka mantar dani da wannan ƙyaƙyƙyawar fuskar taka�.
“Kin rainani wlhy� ya faɗa cikin faɗaɗa murmushin fuskarsa har haƙoransa na bayyana.
Itama murmushin tayi, kafin ta sake magana ya miƙa mata takardun gefensa.
Amsa tayi cike da É—unbin mamaki, shikuma ya tsura mata idanu yaga yaya zatai.
Cikin tsagwaron mamaki ta ɗago tana kallonsa bayan kammala duba takardun guda uku, “Yaya dan ALLAH yimin ƙarin bayani, ban fahimci komaiba bayan sunan Saudia kuma da naka�.
Kunnenta yaja har saida ta riƙe hannunsa tana ƴar ƙara sannan ya saki yana dungure mata kai, “Ashe a banza aka cima su baba kuɗin tara�.
“Ba komai ai sun yafe� Rumana ta faɗa tana dariya.
Shima dariyar yayi yana amsar takardun daga hannunta.
“Kinsan takardun minene?�.
“Abinda nake jiran ji kenan Zumana�.
Sai da ya sauke Haysam dake ƙoƙarin sauka daga jikinsa ƙasa sannan ya cigaba da faɗin, “Na makaranta nane, ammafa a ƙasar Saudi-Arebia�.
Sosai Umm-Ruman ta waro manyan idanunta waje, “Yaya wasa ko gaske dan ALLAH?�.
Hannunsa ya miƙa mata ta kama, yay mata nuni daya taso, babu musu kuwa ta taso ɗin ya ɗorata bisa cinyarsa, cikin magana a hankali kamar mai gudin a jisu yace, “Indai haihuwar Haysam bata zama wasaba haka shima wannan ba wasa bane Babie R�.
Rungumesa Ruman tayi cikin murna tana dariya, hakan ya saka Zainab fitowa dan taga dariyar mi suke haka?.
Da sauri ta nema komawa baya amma sai Ahmad ya kirata, dole ta dawo kanta a ƙasa saboda a yanda suke, ya miƙa mata hannu itama alamar tazo, har lokacin kuma Rumana na jikinsa ya hanata tashi.
“Kinsa mi Auntynki kema murna?�.
Kanta ta girgiza har sannan ta kasa kallonsu.
Sanar mata yayi itama, babu shiri Zainab ta faÉ—a jikinsu tana ihun murna itama, hakan ya saka Haysam fashewa da kuka saboda tsoratan da yayi.
Sakinsu Ahmad yayi suka maida hankalinsu gareshi, ganin yanda ya raɓe jikin kujera kamar wani marayane ya basu dariya.
Aiko suka shiga masa dariya, Zainab ta É—akkosa itama tanayi.
Ahmad ya amshesa yana faɗin, “Sorry Abbanmu, kayi fushi kai ba'a faɗa makaba ko?, to tuba muke Sadaukina�.
Zainab da Rumana dai dariya sukeyi har sannan, Rumana ta kalli Zainab tana faɗin, “Zainab haɗo masa abincinsa inagama yunwa yakeji�.
Da to ta amsa ta nufi kicin, Rumana kuma ta nufi É—akin barcinsu domin haÉ—ama Ahmad ruwan wanka.
Bayan ta kammala haɗawa ta leƙo ta faɗa masa ga ruwa.
Amsa mata yay yana miƙama Zainab data fito Haysam.
Koda Ahmad ya shigo ɗakin Umm-Ruman saita sake rungumesa, alamar dai har sannan tana cikin farin cikin, ta haɗe bakinsu waje ɗaya, su oga Amadi dama kaɗan ake jira, koda Rumana taso janye bakinta sai yaƙi, ya kuma ƙanƙameta cikin sauke numfashi yake faɗin, “Yarinya ai kuma baki isaba, kin kawo kanki ai�.
Za tai magana ya kuma maidawa, dole tai shiru ta koma amsar saƙwanninsa masu tsayawa a rai.
Daga ƙarshe dai tare sukai wankan🤫.
★★★★★★
Sati ɗaya da samun wannan takarda Ahmad ya tafi gida, wannan karon Rumana ta saka ran zaije dasu, amma sai yace saboda makarantar Zainab, dole ta amshi uzirinsa ta haƙura ya tafi ya barsu da kewa.
Ya zoma ahalinsa da farinciki mai yawa, yayinda maƙiya abin ya zafesu a zuciya, dan mama gaje yini tai haɗiyar zuciya, gashi ta kira Number Samina a rufe, da yamma kuma tace zataje gidan inna mari baba ya hanata.
Washe garin zuwan Ahmad aka sanya ranar su Fa'iza, dama akan hakan ne baba ya kirasa, sai kuma ga dalilin zuwan nasa akan tafiya karatunsa.
Wata É—aya aka saka kacal, saboda Ahmad ne zaiyi komai, gashi kuma watan gobe idan ALLAH ya kaimu zai wuce idan yakai tsakkiya, nanda kwanaki 45 kenan kacal.
Bai bar kano ba saida ya tabbatar ya rage kaso mafi yawa na abubuwan buƙatar hidimar bikin ƙannen nasa guda biyu, kwanansa shida ya dawo akan sai biki kuma, zai ringa turoma Mudan kuɗi a hankali ana cigaba da rage hidimomi.
Ya tafi iyayensa na sanya masa albarka, tare da tsarabar da aka shiryama su Rumana.
Kasancewar tasan yau zai dawo da wuri tai gyaran gidan komai yay ƙal, dama ta wanko kanta a wani saloon dake nan kusa dasu, Haysam ma an masa aski daya ƙara fiddo ƙyawunsa, dan shima akwai suma ya gada uwa da uba.
Zainab dama tayi kitso kwanaki biyu da suka wuce saboda makaranta.
Alala tai masa mai daɗi, dan tasan shine abinda yafi so a rayuwarsa sai kuma tuwo, tai kwalliyarta cikin shadda siket da riga, inda shima Haysam akai masa gayunsa, zainab kam bata dawo makarantaba, dan lokacin ƙarfe sha biyu da kusan rabi.
Saboda tafiyar yamma yayo jiya sai gasu sun iso da wuri, a gajiye ya shigo gidan saboda zaman mota.
Yay sallama shiru babu amsa, sai idanunsa daya sauke akan Haysam dake barci a falo, yay murmushi yana ƙarasowa ga yaron, gaban kujerar ya durƙusa tare da ranƙwafawa ya sumbaci kumatunsa da goshinsa, yayinda hancinsa ke shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren da yaron keyi.
Umm-Ruman dake bayansa tsaye bai saniba tai murmushi, sai da ya miƙe ta matso jikinsa ta rungumeshi ta baya tana ɗora kanta a bayansa, a tare duk suka sauke ajiyar zuciya, Ahmad ya ɗora hannunsa akan nata data zagaye cikinsa yana firzo iskar bakinsa, zagayo da ita yay gabansa yana ƙarema kwalliyar tata kallo.
“Gwal ɗina kinsan kuwa ke sarauniyace ko a cikin matanma?� yay maganar yana ɗora goshinsa akan nata.
Murmushi tayi tare da dora laɓɓanta akan nashi ta sumbata kaɗan ba tare da tace komaiba.
Yana ƙoƙarin maida laɓɓansa akan nata zainab ta shigo da sallama, dukansu baya sukaja kowa yabar jikin ɗan uwansa.
Zainab dama bata lura da yanda sukeba tahau ɗokin ganin yayanta ya dawo, sannu da zuwa tai masa kafin ta ƙaraso ta duƙa tana gaisheshi da tambayarsa jama'ar gida.
Fuskarsa da ɗan murmushi ya amsa mata yana zama cikin kujera, ya tambayeta karatu tace Alhmdllh, saƙon gaishe-gaishen da duk aka aiko mata ya shiga lissafa mata, dai-dai nan Rumana ta dawo ɗauke da ruwa a kofi.
Gefensa ta zauna kaÉ—an ta tsiyaya masa ta bashi.
Amsa yay yana wani narke mata fuska cike da salo, ita dai ta kauda kanta tana murmushi, saima ta tashi zuwa É—aki domin haÉ—a masa ruwa, harta gama ta dawo suna wajen shi da Zainab, Haysam dai bai tashiba yanata barci.
Kusan mintuna uku sannan ya miƙe zuwa ɗaki, Zainab ma ta nufi ɗakinta tana faɗin bara tazo taci abinci yunwa takeji, Rumana tai dariya cikin tsokana take bata amsa da, “Ai yau keda ɗanki banyi girki da kuba, iya yaya kawai zaici abincin gidannan�.
Zainab taja birki cikin shagwaɓa take fadin, “Mi mukayi aunty?�.
“Ku kuka sani, idan ya tashi ki tambayesa tsiyar da yaymin yau a gidannan, bugu yaci kafin nai masa wanka yay barcinnan�.
Saurin dawowa Zainab tayi, ta duƙa gaban Haysam tana tattaɓashi da faɗin, “Kai aunty Rumana, dan ALLAH da gaske bugunsa kikayi?�.
“Oh kin ɗauka wasa nake kenan?�. Rumana ta faɗa tana shigewa ɗaki.
Zainab kamar zatai kuka taketa shafa kan Haysam dake barci lokaci-lokaci yana sauke ajiyar zuciya, yayinda haushin auntyn tata ya kamata.