← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 94

Sashe 26

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ina idar da salla ne na fara kimtsa kayan danaga ya kammala yankawa, sai biyu suka rage bai taɓaba, na tattare ƙyallayen na saka a leda suma na share ɗakin dan ya samu wajen cin abinci.
Ranar dake a tsaye tasaka garin É—aukar wani mugun zafi, da ace ina da dama kayan zan cire nasha iska wlhy.
Haka dai na gama shirya masa abinci a tabarma na É—auki kofi ina zuba ruwa, bisa tsautsayi na É—an zubar, wanda na gama zubawa na É—auka nakai gaban abincin nasa, sannan na dawo ina duba tsumma danna goge wanda na zubar.
Abinka da sabuwar leda, ashe na ɗan ɗisar da mangyaɗa a wajen sanda nake girki, koda na goge wajen kuma ban lura da nanba,, ga ruwa ya zuba, ina ɗora ƙafata da dube-duben inda ruwan ya zuba kawai naji na tafi gaba ɗayana, sai gani ƙasa.
Fashewa nayi da kuka saboda wani azabar zafi daya ratsa ƙashin ƙafata da ƙuguna.
Sosai nake kuka dan na kasa tashi, bansan yaya akai kunnen maman Ama ya jiyoniba, sai gata ta shigo jiki na ɓari tana tambayata lafiya?.
Ganina ina kuka rike da ƙafa da hannu ɗaya, ɗayan kuma na riƙe ƙugu ya sakata faɗin, “Faɗuwa kikayine?�.
Kaina kawai na iya ɗaga mata ina cigaba da kukana, takai hannu zata taimaka min danna miƙe sai ga Yah Ahmad yay sallama ya shigo.
Da mamaki ya kalli maman Ama ɗin sannan ya kalleni fuska babu walwala, “Miya faru?�.
Maman Ama ta buÉ—e baki zata bashi amsa nai saurin katseta....
Kuka na kuma saka masa wanda ni kaina nasan harda taɓara nace, “Faɗuwa nayi�.
Hannuna dake cikin na maman Ama ya kalla, ba tare da ya kalleta ba yace, “Barta kawai zan tada ita�.
Koda ta sakeni a zatona zata fita, sai naga matarka ta gyara tsaiwa tana kallonmu sai kace wasu tv É—inta.
Wannan abu da Maman Ama tayi ya zafi Ahmad a zuciya, dan haka da gayyar cusa mata baƙinciki ya rungumi Umm-Rumana ya ɗagata cak zuwa saman gado, tunda ya fahimci matarnan muguwar ƴar sa ido ce.
Aiko tamkar ya sani, dan tsayawa tai taga yaya za'a kwashe, daga ita har mijinta sun fahimci Ahmad bai taɓa taɓa Rumana ba, har gulma suke akan hakan, wai baya son Rumana hankalinsa nakan Samina har yanzun.
Wani irin zaro idanu tayi na tsagwaron mamaki, maimakon ganin hakan ya sakata fita saita sake maƙalewa.
Rumana kuwa tunda Ahmad ya É—auketa jitai hawayen sun gudu saboda tsabar al'ajabi, sam bata kawo hakan a ranta ba, jitai kawai jikinta na wata irin tsumar tsoro, dan a rayuwarta hakan shine na farko gareta.
Ya kwantar da ita a gadon sai dai rabin jikinta na saman jikinsa, a hankali yace, “A inane kika buge?�.
Hawaye Rumana ta matso da suka cika mata idanu, ta nuna masa ƙafarta, ƙugun kuma kunya takeji shiyyasa ta kasa nuna masa dukda nan yamafi ƙafar buguwa.
A mamakinta sai gani tai ya tura hannunsa cikin rigarta ya shafa ƙugun yana faɗin, “Shinan bakison a taɓane ragguwa?� ya ƙare maganar da matsa wajen.
Jikin Rumana har rawa yake ta ƙankame Ahmad ba tare da ta shirya hakanba, ga wani siririn kuka data sakar masa na jin zafi, bai bartaba yanata matsa wajen yanda ƙashin zai saki.
Ita ko ta ruƙunƙumesa tamkar zata koma masa ciki. Dauriya kawai Ahmad yakeyi, amma gaba ɗaya jinin jikinsa yamutsawa yakeyi ta kowacce kafa, tsigar jikinsa yanda ta tashi ya saka kowanne gashin jikinsa fitowa ta ɓularsa. Karo na farko a rayuwarsa da ƴamace ke a jikinsa kwance, abinda ya jima yana kissimawa da Samina kawai, a yau sai ga saɓanintace kwance a jikin nasa. Kasancewarsa gwanin kamewa yasa baka fahimtar yana a mawuyacin hali koda a fuskane, saima kalmar Sorry da yaketa ambatama Umm-Ruman a hankali yana cigaba da murza ƙugun�.
Saɗaf-saɗaf maman Ama ta fice a ɗakin wani abu na tokare mata maƙoshi, dan ita gani tai soyayya suke a gabanta kawai.
Duk yanda Ahmad yaso daurewa ya kasa, hakan yasashi zamewa ya kwanta yana saka Rumana sosai a jikinsa, wai shinan duk azuwan gyarane, taƙi tsayawa ya matseta, wannan damar Rumana da azabar matsa gurin ciwo ya isheta ta kuma mannema Ahmad sosai tana kuka da roƙonsa dan ALLAH ya bari hakanan, akwai zafi sosai.
Sam shi baima san tanaiba kam a yanzu, dan É—iff kunnensa ya toshe, salon yanda yake matsa mata wajenma kawai zai baka tabbacin ya fara canja tasha ne.

Har maman Ama taje ɗakinta sai ta kasa daurewa, tsabar hassada nacin ranta ta kasa zaune ta kasa tsaye, maganin zafi ta ɗauka ta dawo ɗakinsu Umm-Rumana, tunda ta ɗaga labule taga yanda suke mai makon ta koma da baya sai catai “Yauwa ga maganin zafi kozata shafa a wajen insha ALLAHU zai saki�.
Yanda tayi maganar da ƙarfine ya dawo da Ahmad hayyacinsa, ya buɗe idanun da suka canja launi da ƙyar, kafin ya yunƙura ya tashi zaune da Umm-Ruman a jikinsa, ita tanata shashshekar kukane, shiko sai ajiyar zuciya yake saki a jere kamar jaririn dake neman abinci bai samuba.
Fuskarsa mugun tamke yakai dubansa ga maman Ama, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa saboda yasan muryarsa zata iya fallasa tsantsar buƙatar dake a tare dashi a halin yanzu.
Maman Ama ta ajiye musu maganin zafin gefen gadon ta fice kamar gaske, amma saita maƙale a bakin ƙofa.
Umm-Ruman ta raba jikinta da nashi tana share guntun hawayenta, murya a matuƙar shaƙe yace, “Sannu, kawo ƙafar muga itama�.
Rumana ta marairaice idonta na sake cika da ƙwalla, “Yaya dan ALLAH ka bari na huta sannan, ALLAH akwai zafi�.
Kansa ya girgiza yana kamo ƙafar, “Waya ce miki idan aka barshi anjima bazakiji zafinba, saima kinfiji fiye da yanzu� ya ƙara maganar yana matsa ƙafar itama.
Nanma ta ɗanyi kuka tana rirriƙe masa hannu saboda ƙafarma ta ɗan bugu, sai da ya tabbatar ta matsu sosai ne ya sauka a gadon, jakkarsa ta kaya ya buɗe ya fiddo maganin zafi, dan ko kallon wanda maman Ama ta ajiye baiyiba, a ƙafar ya fara shafawa kafin ya kalli Rumana cikin ɗan ɗaure fuska yace, “Juyo bayan ki ɗaga rigan�.
Cike da jin kunya Rumana tabi umarninsa, shiko yay mursisi yana shafa mata a wajen. Bayan ya kammala ya miƙe tsaya yana cewa, “Kwanta kiɗan huta na minti biyar maganin ya shiga wajen sosai�.
Babu musu ta kwanta tana gyara rigarta, shiko ya ajiye man zafin saman mirror ya koma saman tabarmar ya zauna.
Yunƙurawa tai zata tashi tana faɗin, “Bara na saka maka abincin�.
“Barshi zan zuba kawai�.
Yay maganar yana buÉ—e kular abincin.
Dole Rumana ta koma ta kwanta, Ahmad kuma ya zubama kansa a binci a filet É—in da Umm-Ruman ta ajiye.
Sai ya samu kansa da yawan kallonta, kaɗan-ƙadan idonsa sai ya kai gareta.
Rumana kuwa barcin wahala ne yay gaba da ita ba tare da ta shiryama hakanba.
Maman Ama dataji shiru sai ta kama gyaran murya, da faɗin, “Sannu amarya kinji� Ahmad duk yana jinta, amma sai yay kunnen uwar shegu da ita, jin anƙi bata amsa taja ƙafafunta ta koma ɗaki.

★★★★★★�

Koda na farka bayan la'asar kaina kawai na gani a ɗakin, babu kayan da ya yanka, sai kular da abinci kawai ke ciki da kofin ruwa, filet da ƙaramin kofi da yay amfani dasu ma can na hangosu ya saka a robar da nake tara wanke-wanke.
Sakkowa nai daga gadon, dukda har yanzu ina ɗanjin zafin amma ba kamar ɗazunba, takarda dana gani saƙale a hannun kofin ruwan na zare ina warwarewa.

_Idan kin tashi kici abinci, ga maganinan kisha kuma._
Chapter 26 · 0% Book details