Sashe 21
Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har magriba ruwan bai ƙareba, saboda a hankali suka sakashi, alwala tayo tazo tai salla, bayan ta idarne ta tashi ta saka masa ɗayan ruwan kamar yanda suka nuna mata, duk da dai a tsorace tayi komai, lokacinne kuma Maman Ama.. Ta sake shigowa danta dubashi.
Maman Ama na fita Abu ya shigo gidan da sallama, maman Ama dake ƙoƙarin fita ta amsa masa tana bashi hanya ya shigo,
“To, abun ya kai harda ƙarin ruwa kenan?�. Abu ya faɗa yana ajiye kwanikan hannunsa
Rumana ta share hawaye tana faɗin wlhy kuwa Yah Abu, ni tsoroma nakeji kar wani abune ke damunsa ba'a saniba, garama akaisa asibiti tunda dai wannan ba likita bane babba�.
“Karki damu Umm-Ruman, zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu akaga jikin yaƙi daɗi ai gara aje asibitin, ga tuwo nan inji Ayyah, bara naje na sanar musu dan basusan an saka masa ƙarin ruwa ba�.
Kai kawai Rumana ta iya É—aga masa.
Ya fice da hanzarinsa, ita kuma ta koma ta zauna ta zuba tagumi.
Koda aka kira sallar isha'i da ƙyar ta iya tashi tayi, tana ƙoƙarin ninke abin sallar tajiyo sallamar matan gidansu, da sauri ta amsa tana ɗaga labule, ganin da gaske sune sai daɗi ya kamata, sai da suka gaisa da maman Ama sannan suka shigo ɗakin.
Ayyah ce da matan baba Iliyasu, Gwaggo da mama gaje da Ammin ta ne basu zoba.
Tabarma ta saka musu suka zauna, ta durƙusa ta gaishesu, suka tambayeta mai jiki tace da sauƙi.
Ta miƙe ta zubo ruwa a kofi ta kawo musu, Ayyah tace, “Rumana waye ya saka masa ruwan?�.
“Ayyah tare da yaya Sufyan daya kawosa sukazo, leda biyune, da ɗayan ya ƙare shine na saka ɗayan kamar yanda suka nunamin�.
“ALLAH ya ƙara afuwa� suka faɗa kusan a tare.
Sun daɗe a gidan sunata jajanta abun, har Mudanseer ya shigo da baƙar leda a hannu, shima har cikin ɗakin ya shigo suka gaisa da Rumana, ya tambayeta jikin Ahmad ɗin yana ajiye ledar hannunsa.
“Ga wannan kananzir ne tun ɗazun yace na kawo shaf na manta wlhy, saboda ɗinki ya ɗauke hankalina, kawo risho ɗin a haɗa�.
Miƙewa Rumana tayi ta ɗakko kwalin ƙaramin risho da su Fa'iza suka kawo ta ajiye gabansa, buɗewa yay ya fiddoshi daga ciki, ƙaramine amma yanada ɗan ƙyawunsa, suna nan zaune harya gama zira lagwanin ya haɗa komai yasa kananzir ɗin, sai da yaga tankin ya cika ya miƙa mata sauran yana faɗin, “Sai ki adana wannan ko�.
Amsa tayi cikin girmamawa kamar yanda aka koyar dasu ga dukkan yayyensu.
Su Ayyah suka miƙe suna faɗin bara su wuce kar dare yayi, idan ya tashi tai masa sannu.
Tamkar Rumana zatai kuka haka taji, ta rakasu har soro tana share guntun hawayen da suka cika mata ido.
Umma tace, “Haba Rumana miye abin kuka anan, kowa da haka ya fara kinji, ALLAH ya baku zaman lafiya dai da haƙuri da juna�.
“Amin� Ayyah ta amsa, Umma babba kam baki taɗan taɓe tana wani mosan mugunta, kusan dai ƙawar mama gaje ce.
Ayyah na kallonta amma tai kamar bata ganiba suka fice, Rumana ta koma cikin gida tana share sauran hawayenta.
Zama tai suna É—an hira da Mudanseer, dan dama can shi yana sake musu ba kamar Ahmad ba, sannan mutum ne mai yawan barkwanci ga kowa. Shine ya sakata dole taci tuwon da Abu ya kawo, sannan yace ta bashi tukunya da ruwa ya dafa musu ruwan zafi, idan Ahmad ya tashi sai kawai ta juye masa yay wanka tunda ALLAH yasa akwai filas.
Tashi tai ta ciro tukunya daga kayanta, ta ɗauraye ta zubo ruwa ciki ta kawo masa ƙofar ɗaki inda ya maida risho ɗin yana ƙoƙarin kunnawa, ta ɗauko filas ɗin shima ta wanke dan su Fa'iza duk suka kawoshi tare da risho.
“Bara naje na dawo kafin ruwan yayi� Mudan ya faɗa yana ƙoƙarin fita.
To ta amsa masa, shikuma ya fice.
Bai jimaba sosai ya dawo da leda a hannu, ya miƙa mata tare da buɗe tukunyar, ruwan nata ƙoƙarin tafasa ne, dan haka ya buɗe murafan filas ɗin ya matso dashi kusa. Yana tafasowa kuwa ya kwashe sa, sai da ya cika sannan ya miƙa mata bayan ya rufe, ya kashe risho ɗin ya ɗako da kansa ya maido mata ɗaki.
“To Umm-Rumana bara naje gida dare ya farayi, idan ya tashi ki tabbatar dai yasha magani, amma ki haɗa masa tea yasha zaiji daɗin jikinsa, ALLAH ya ƙara afuwa, da safe idan ALLAH ya kaimu zan dawo naga yaya ya tashi, idan munga babu wani canji sai aje asibiti ALLAH ya rufa asiri�.
Kanta ta ɗaga masa, ji take kamar tace ya tsaya karya wuce shima, amma bata da ikon hakan, tana kallo ya fice ya barta ita kaɗai sai Ahmad daketa barcinsa dan Mudanseer ya cire masa ƙarin ruwan tun ɗazun saboda ya ƙare.
Tun tana kallonsa harta fara gyan gyaɗi, ahaka Ahmad ya farka kusan ɗayan dare ya ganta, ɗakinsu buɗe ga hasken fitila ƙau saboda sabon batiri dake a ciki, idanunsa yaɗan lumshe ya buɗe a kanta, sai ta bashi tausayi, an haɗata da aikin da sam bai dace da itaba.
Bargon ya janye ya sakko daga gadon, yaɗanji ƙarfin jikinsa saboda ƙarin ruwan da aka saka masa.
Motsin saukarsa ya saka Rumana buÉ—e idanunta, cikin É—an rikicewa take masa sannu, ya amsa murya a dushe.
Buta ya ɗauka ya fita, itama saita miƙe ta fara zuba ruwan sanyi a botiki kafin ya fito taji idan zaiyi wankan, a haka ya fito ya sameta, kanta a ƙasa tace, “Yaya Ko zakayi wanka?�.
Kamar bazai amsa ba sai kuma yace, “Inason yi amma akwai sanyi�.
“Ruwan ɗumine ai�
Kallonta yayi sosai, ganin haka yasata saurin cewa, “Eh ai Yah Mudan ya kawo kananzir ɗin, shine ya dafa maka�.
Janye idonsa yay akanta yana jin ƙaunar ƙanin nasa, da hannu yay mata nuni data haɗa masa, ya miƙe ya hau cire kaya.
Da sauri ta fita da ruwan takai masa bayi, a tsakar gida suka haÉ—u yana sanye da jallabiya, ta wuto shikuma ya shiga bayin,
Tea ɗin ta haɗa masa kamar yanda Mudan yace tayi, ta shimfiɗa abin salla ta ajiye shayin a gefe da biredi, sai ƙwai da Mudan yasa aka soya masa shima ta juye a filet ta rufe.
Ahaka ya shigo ya sameta, ya ɗauki buta ya sake fita, babu jimawa ya dawo, sai da ya kulle ɗakin sannan ya ƙaraso, Rumana na gefe zaune kanta a ƙasa ya tada salla.
Kafin ya ƙarasa ramuwan sallar magriba da isha'in har Barci ya fara kwasar Rumana a wajen, ta riga da ta saba da barcin wuri.
“Ki tashi kije ki kwanta� nutsatstsiyar muryarsa ta daki kunnenta.
Buɗe ido tayi da sauri tana gyara mayafinta, ta ɗaga masa kai tana ɗan matsowa gabansa, buɗe shayin tai da ƙwan ta matsar gabansa sosai,
“Su Ayyah sunzo dubaka da Umma ƙarama da Umma babba, hakama yah Sufyan yazo sake dubaka baka tashiba�.
“Na gode� ya faɗa a hankali.
Shayin ya ɗauka ya fara sha saboda yunwa yakeji dama, Rumana ta miƙe ta ɗakko ledar magungunansa ta ajiye gabansa, tabarmar data kwanta jiya ta ɗauka zata shimfiɗa a ɗayan lungun gadon tunda Ahmad na zaune inda ta kwana jiya sai ya dakatar da ita.
“Ki hau gadon ki kwanta�.
Yanda yay maganar a dake tasan babu zancen musu, sai dai jikinta har rawa yake kaÉ—an, taya zata iya kwana dashi bisa gado É—aya?.
Kamar mai tsoron a saceta haka ta É—ofana a bakin gadon ta cure jikinta waje É—aya.
Ahmad na kallonta baice mata komaiba, ya gama shan shayinsa yasha magani da ƙyar, Rumana dayake ta juya masa baya batasan hidimar da yakeba.
Ya daɗe zaune a wajen har barci ɓarawo ya sace Rumana dake kwance a ɗofane.
Jin barci na neman sake ɗaukarsa saiya miƙe ya ɗakko filo daga gadon da bargo, jallabiyarsa ya cire ya kwanta akan abin sallar yana rufa da bargon duk da kuwa garin akwai sirkin shigowar zafi.
★★★★�
Yau dai kam duk yanda yaso fita a gidan bayan sun gama karyawa hakan ya gagara, dan sosai ciwo ya kaishi ƙasa, daga ƙarshe dai sai da Rumana ta amsa wayarsa ta kira Mudanseer.
Babu ɓata lokaci yana zuwa suka wuce asibiti.
Sai ga zance kamar wasa ya zama babba, dan kuwa dai gado aka bama Ahmad.
Kowa ya tausaya masa, dan kuwa dai ansan ciwon abinda Samina tai masane ya kasa barinsa.
Samina ko koda taji labari ko a jikinta, dan ko sau ɗaya bata taɓa leƙa Ahmad asibiti ba har yagama kwanakinsa shida aka sallamesa ya koma gida.
Duk ya rame choco color É—in fatarsa ta sake wani irin fayau, sai hancinsa da ya sake fitowa raÉ—au da manyan idanuwa.
Bayan yayi wanka da ruwan da Rumana ta dafa masa ya fito jiki duk babu ƙwari, su Ayyah duk suna daga waje zaune ya shiga ɗaki ya shirya, itama dai Rumana wajen ta fito ta zauna zaman jiransa.
Bayan ya kammala saka kayan ya kira Mudanseer daga cikin É—akin.
Shiga yay, mintuna kaɗan shima Mudan ɗin ya leƙo ya kira Ayyah da Rumana.
Shiga sukayi, Rumana ta zuba masa abincin da Yaya Maryam ta kawo masa, duk da bayajin daɗinsa haka Ayyah ta takura masa tana basa a baki, sai da yaci fin rabi sannan ta ƙyesa, aka koma dagamar shan magani, dan kuwa da ƙyar yasha sa hardasu yunƙurin amai.
Ranar dai duk anan suka yini sunata tarairayarsa, sai gab da magriba duk suka tafi aka barsa shida Rumana kawai.........âœðŸ?
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*
: *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*ðŸ™ðŸ½
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuoeSgXuo
*(14)*