Sashe 99
Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
A bangaren Alhajin ALLAH wato goganku be farka a baccinba se wajajen sallarh azahar ya tashi yayi wanka yayi alwala ya fice a gidan sanye da jallabia se zuba kamshi yakeyi ya nufa masallaci dai-dai ana kokarin tada axahar,...dasuka idar da sallarh seda ya jima yana maraji'arh alqur'ani me girma kana yayi addua'ur'insa ya shafa. Da counter dinsa a hannunsa yana lazimi ya fice a masallacin ya dawo cikin gidan, yanajin cikinsa na kiran ciroma, tsit yaji gidan kamar ba kowa se yayi tunanin ko yarinyar ta koma side din Amihh ne tabe baki yayi yace "dakin raba kanki ds izayar dunia..." Juyawa yayi Ya nufa kiching, dan hadawa knsa abinda zesa a bakin salati, tinda yake a side din be taba shiga kiching dinba se yau, ya karasa ya shige kichng din yana me binsa da ido tsarinsa yy kyau harda AC a kiching din, rasa ma ta ina ze fara yayi sbda shi be iya ko kunna gass ba, koda yayi karatu a waje a restaurant sukecin abinci, Dan hk be iya komi ba a fannin girki. tea kawai yake iya hadawa knsa da knsa, Gashi amihh duk tabi ta tsangwanmesa ko abincin nata be samu yaci kmr ba ita ta haifesa da cikintaba. Dawowa falon yayi byn ya hado tea din da bread me yanka yanka ya zauna a kn 2ct ya dansha tea din yana yatsina fuska ko tea dinma be iya hadawa ba ji yy be masa ddh ba, Haka de ya tuttura da bread din yanaci yana tsuki, yau yasawa ranshi insha Allah se yaje side din amihh yaci abincin ko zeji ddh, zuciarshi na cike da kewar abincinta. Bayan ya gama ya dauki cup da bread din ya maidasu kiching ya wanke cup din ya maidasa ma'ajinsa sbda shi mutum ne da beson kazanta, zagaye gidan ya shigayi yana tsukin haushin canza masa tsarin gidanshi da Amihh tayi, hannunshi yakai kan handle din kofar dakinta besanma ko dakin waye ba, be taba shiga dakin ba se yau, dakunan dake side din nasa sunkai 8 a kasa akwai hudu, haka ma a saman akwai dakuna hudu, amma be taba shiga ko daki dayaba a gidan, inba dakinshi ba se yau yaji yanaso yaga dakunan dake gidan.... Tura kofar dakin yayi ya shigo, kwayar idonshi ya sauka a knta, tana kwance har lokacin bacci takeyi batasanma inda knta yake ba, batasanma anyi sallah azahar ba sbda mgnin da salwah ra bata na zazzabin yana dansa bacci. Karasowa yayi cikin dakin ya maida kofar ya rufe yanajin zuciarsa na masa kuna da zafi sbda ganinta da yg kwance, karasowa yy bakin bed din datake kwance kmr gadon gidan ubanta, ko gadon gidan karuwai, ya fadi hkn a ranshi ganin yadda taketa bacci, takaici ya rufeshi wato bacci ma takeyi tsanarta ta kara yawaita a zuciarsa, ji yayi kmr ya rufeta da duka sbda kiyayya, gata de da fari da kyau amma shi ganin bakinta yakeyi, sam ko kyaun nata ma be gani ynzu, jiya zuwa yau ya kara tsanarta sbda kalaman Amihh garesa. Duvet din dake lullube a jikinta ya yayeshi ya jefoshi kasa, cikin kyama ya bita da ido, har lokacin bacci takeyi, batasanma anayi ba, sanye take da riga mara nauyi, red se hijjabin jikinta golden. Wata iriyar uwar wawiyar tsawa ya daka mata. "Keehhhh!!!!''' Ya fadi da karfin tsiya kmr ze fasa dakin, muryarsa cike sa karad'i. A matukar gigice ta farka, batasanma sadda ta diro kasan gadonba jikinta na rawa duk tabi ta firgice ta tsure jin tsawar tasa, har tsakiyar knta... Ido ya bita dashi zuciarsa babu alamar tausanta...dago kwayar idonta tayi ta zuba masa su, jikinta na rawa nan da nan ta fara hawaye ita daman akwai saurin kuka, zuciarta se up up takeyi kmr zata fashe, data diro daga bed din bata ankare dashi ba se ynzu . "Ubanwa ya baki danar yin bacci? Nan gidan ubanki ne, ko an gaya miki gidan karuwai ne, na ...." Ya fadi kwayar idonshi na knta cikin tsantsar tsagwaron tsanar yake mgnr, ko a kwayar ido ya isa ya tabbatar maka da AB'ILAL be kaunar hilwah.