Sashe 116
Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Dayake already Amihh ta kira salwah tace ta gayawa hilwah ta shirya AB'ILAL ze kawota asibiti ta masa allura Salwah tace to kawai amma bataji ddh ba dataji ance AB'ILAL ze kai hilwah asibitin, ita de bata da yadda zatayi ne. Salwah ta gayawa hilwah itama bataji dadin hknba, tinda tayi ciwonnan, nan take kwana. Salwah tace tayi maza ta shirya sbda gudun tijarar gogan, hilwah ta shirya cikin jallabia kalar peach pure, irin me kyaunnan wanda daka kalla zakasan peach color ne, abinka da farin mutum ta dora peach se sukaso su saje kalar ta amsheta ainun, ta yane knta da mayafin jallabiar shi kuma dark peach ne ya amsheta iya amsa sumarnan ta fuskarta ta kwanta luf luf tayi matsifar kyau dukda ba makeup a fuskarta ko mai ma bata shafa ba kasancewar ana dan zafi zafi, ban tabbatar da cewa me kyau me kyau bane se a knta dukda ba make up amma ita me kyau ce tama fi kyau ta hadu iya haduwa rigar ta amsheta tako ina, saman rigar aikine da hannun rigar aikine haka kasan rigar ma duk aikinne, dark pink, tayi kyau kmr asa kudi a siyeta, tako ina cas cas, das das. Salwah se kodata takeyi na kyaun da tayi, se santinta takeyi hilwah harga Allah bata taba ganin me kyau da Qualifies irin na hilwah na. Godia Hilwah ta mata na yadda taketa yabon kyaun nata, ta feshe jikinta tako ina da perfume dinta me mugun ddh. Dawowa falo sukayi suka zauna suna jiran shigowar gogan dukda de salwah tasan be zama lallai yazo ba. Suka zauna suna dan taba hira salwah taga time ya Dan tafi tace "hilwah mutuminnan fa ko ya shirya ba mgna zeyiba, yaushe ma girman kai ze bari yayi mgna, se kace dan qaruna..." Hilwah ta bita da ido kawai, itama tasan hkn bame yuwwa bane yazo yayi mgnar. Salwah ta daga waya ta kira Amihh ta gaya mata har ynzu fa AB'ILAL bezo ba,.." Amihh ta katse wayar ta danna dealing din number dinsa, tini ya koma falonsa se faman tsuki yakeyi, 10mnt din da yayi ko 1snd be kara ba ya dawo falonsa, shine Amihh ta kirashi , kin dagawa yayi har seda wayar ta kara ringing na biyu kana ya daga ya kara a kunne. "Duk bura ubar da kakeyi kaci gaba dayi Dan ubanka ni de uwarka ce ni kk wulakntawa ...da saake a tarbiarka!'' Amihh ta fadi a hasale. AB'ILAL ya sauke ajiyar zucia yace "Amihh nifa Ba wulakntaki nakeyi ba, tin dazu ina tsaye waje inata jiranta kince in kawota nabi umarni , kuma se inyita tsayuwwa waje bata zoba gaskia kuma ni ynzu na koma ma falona, kaina ke ciwo...." Ya karashe mgnr cike da gajiawa. Amihh ta amshe da ''ko ciwon ajali kakeyi ka taso ka kawota ynzu nan kaji na gaya maka!'' Tana gama fadar hkn ta katse wayar ta kiran.