← Book details Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 225

Sashe 41

Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

azababben sanyi, inda ze samu ma a kara masa barguna guda uku so yakeyi, se ynzu AB'ILAL ya fara tunanin anya kuwa hilwah ba Aljana bace ,ko kuma mayya masu lashe ma mutum kurwa, domin kuwa silar ganintane ya haifar masa da wannan mummynan yanayin a jikinsa. Alhasan da duk yabi ya damu best friend ba lafiya se cewa yakeyi "Ka tashi muje asibiti plx...." AB'ILAL yayi bnza dashi domin kuwa bejinma ze iya tashi vitamin A dinsa ya fara sauka. Hnklin Alhasan ya soma tashi domin be saba ganinsa a wannan halinba, gashi yy juyin duniya kan ya tashi su tafi asibiti amma ya masa bnza, karshema alhasan cewa yayi ze temaka masa ya tashin ko ya daukeshi amma ina AB'ILAL yaki amincewa,,jiki bb laka alhasan ya dauko wayarsa domin kiran doctor dinsa doctor Eesha, har yayi dealing number dinta ta shiga ta dauka ma yayi saurin katse wayar, tunawa da yayi da halin mutuminsa, dukda yana cikin Wannan halin amma be zama lallai in yaga doctor mace ba ya yadda ta dubashi. Dole ya chanza akalar kiran zuwa ga kiran abikinsa kuma likitansa doctor kabeer , bugu daya biyu dr kabeer ya dauka. Alhasan ya masa bayani kan cewa yazo gidansa yanada mara lafiya ya dubasa abokinsa ne ba lafiya, zazzabi me zafi,'' ba bata lokaci dr kabeer ya ce Gashi nan zuwa.." Kana ya katse kiran. Alhasan ya ajiye wayar a side drower din ya nufa kiching domin ya hadowa AB'ILAL koda ruwan tea ne ko coffee yasha kafin dr ya karaso, dukda de yasan halin kayansa da wuya yasha din. A gaggauce ya hado masa coffee kawai ya nufo dakin hannunsa riqe da dan karamin plt me dauke da glass cup me mugun kyau da tsaruwa, ya karaso bakin bed din ya zauna hadi da ajiye plt din dake dauke da cup din a gefensa, idonshi na kan AB'ILAL dake cikin bargo har zuwa lokacin jikinsa be bar kakkarwa ba. Nan Alhasan ya shiga lallaminsa kan ya tashi yasha coffe din, Amma AB'ILAL ma yaki tanka masa, kuma idonshi biyu yana jinsa, kawai de beda ra'ayin amsa masa ne kuma beda ra'ayin shan coffee din, se faman lumsar idanuwa yake tayi a cikin bargon ya juya ya koma ya kwanta rubda ciki, yana kara lumshe kwayar idonshi yana budewa a hnkli a hnkli duk sun kara masa nauyi sbda be rintsaba tin jia har zuwa yau, rabonshi da bacci tin shekaran jiya da daddare shima ba wani baccin kirki yayiba sbda ibadar dare da yakeyi. A haka dr kabeer yazo ya sameshi da kayan aikinsa, shi knshi dr kabeer din ya girgiza da ganin yadda zazzabin yy ma AB'ILAL mugun kamu, seda ya tambaya wai kwananshi nawa a wannan yanayin, Alhasan ya shaida masa daga jiya ne zuwa yau kawai. Dr kabeer da idanuwansa ke manne da glass yace "what! Jiya zuwa yau shine yayi laga laga haka?" Ya karashe mgnr da mamaki a ransa, Alhasan ya daga masa kai alamar tabbatarwa. Dr kabeer ya jinjina kai kawai shi da kanshi ya tausayawa AB'ILAL sbda yana jin jiki, "yaci abinci?" Dr kabeer ya tambayi Alhasan, jinjina masa kai Alhasan yy alamar ah'a ya nuna masa inda ya ajiye plt din dake dauke da cup me Coffee din daya hada masa yace "Ga coffee ma na hada masa be sha ba...'' dr kabeer yace "Okay ba damuwa..." Daga hk ya fara kokarin duba ab'ilal ba wani bata lokaci ya duba BP dinsa yaga yy kasa kuma damuwa ce tasa hkn, cikin hnzari ya bashi taimakon gaggawa yasa masa drib byn ya debi jininsa domin yaje ya masa gwaje gwaje, domin kuwa already yazo da komi nasa na bukatuwa, cikin drib din ya narka masa allurorin bacci domin alhasan ya sanar dashi beyi bacci ba jiya. Wasu magunnguna dr kabeer ya rubutawa Alhasan ya bashi yace ya nemo ynxu a ciki a bawa AB'ILAL guda daya in yayi bacci ya tashi. Alhasan yace to jiki na rawa suka fice daga dakin shida dr kabeer din , suka fito compound tare kowa ya hau motarsa suka fice a gidan bayan dr yace ze dawo bada jimawa ba. Direct Alhasan pharmacy ya nufa domin siyan magungunan, driving yakeyi amma tunanin AB'ILAL da halin daya barshi yana ranshi.A gaggauce ya isa dialogue pharmacy a nan ya siya magungunan ya juya ya koma gidansa. Yana yin packing ya fito cikin sassarfa hannunsa riqe da ledar magungunan daya siyo, ya karasa cikin Gidan nasa hannunsa riqe da ledar magungunan daya siyo. Koda ya shigo dakin yana tunanin zega AB'ILAL na bacci, nan fa ya ganshi idonshi tar a bude ya zubowa kofar dakin ido, ba karamin mamaki abin ya bashi ba, sbda an masa alluran bacci, shi ga tunaninsa tini ma yayi nisa a baccin, karasowa yayi bakin bed din ya tsaya tsaye ya zubo masa ido, yana fadin "kayi bacci ne ka tashi frnd? Ko bakayi baccin bane?'' Yayi masa tambayar fuskarshi dauke da mamaki, shuru AB'ILAL yayi ba tare daya ce masa komi ba, alhasan ya zuba masa ido yanada tabbacin be rintsaba sbda ga idanuwansa nan jajur kmr garwashin wuta, a bangaren AB'ILAL kuwa gaza baccin yayi, kwata kwata dukda ga baccin yanaji a idanuwansa amma ya gaza yinsa saboda tunaninta, ya gaza ficewa a kahon zuciyarsa. Rabawa Alhasan yayi ya zauna gefen bed din ta wurin kanshi, har ynzu cike yake da mamaki, ya ajiye ledar hannunsa a side drower ya cire wayarsa a aljihu ya danna wa dr kabeer kira, bugu daya ya daga, nan alhasan ya Roqeshi kan ya dawo da wuri, dr kabeer yace insha Allah nan da 30mnt ze dawo, alhasan yace okay daga hkn sukayi sallahma. Alhasan ya dawo da kwayar idonsa kan AB'ILAL byn ya gama wayar. Ya fara tunanin wani abu ne ke damun AB'ILAL abun ma gagarumi domin kuwa ruwa baya tsami banza, nan da nan Alhasan shima ya kara shiga dmwa. "Frnd Dan Allah meke damunka plx?'' Alhasan yy tambyar muryarsa cike da zaquwar yaji meke damun abokinsa. AB'ILAL ya lumshe idanuwansa kawai ya budesu ba tare daya ce komiba, kwata kwata ko mgna baya so a masa, saboda knshi kamar ze fashe yake jinsa, juyar da fuskarshi yy gefe guda, ji ykeyi kmr ana buga masa kacau kacau a tsakiyar Kansa, har wani dil-dil gefen da kwakwalwarsa take yakeyi masa, dafe kn nashi yayi zucia cike da damuwa, ya rintse idanuwansa. Sannu Alhasan ya bishi dashi domin kuwa ko ba a gaya masa ba yasan yana mugun jin jiki. Maganin da dr yace a bashi Alhasan ya dauko ya shiga kokarin bashi, amma fir Ab'ilal yaki amsa, karshe ma yace baze shaba, alhasan yy juyin duniya amma yakisha, gashi yaki cin komi, se abin ya kara damun Alhasan ya shiga dmwa Ainun, yace "Bari kawai in kira Alhaji babba in gaya masa bka da lafiya, ni ciwon nan naka tsoro yake bani, an baka mgni kaki sha again kaki cin abnci, an maka allurar bacci kakiyin baccin, ko tantama babu wani abu ke damunka a ranka, kwara in kira Auwal hubb, ko Alhaji babba in gaya musu kawai..." Yy mgnr cikin dmwa, idanuwansa na kan AB'ILAL , wanda yy shiru yana sauraronsa, harya dauka ya dire, cikin muryarsa ta marasa lafiar dake jin jiki ya fara mgna "Plx karka kirasu frnd.. , na fara jin sauki..." A hasale Alhasan ya amshe da "Sauki? a ina ? Kaki cin abinci, kakishan ruwa, kaki shan mgni, ta ina zaka samu sauki? Zakace kar in gaya musu? Ah'a kwara in gaya musu gaskia karkazo ka mutum min a gida, ka barni da gwaramar katsinawa da larabawa..." Ya karashe mgnr yana latsa karamar wayarsa dake hannunsa. AB'ILAL ya juyo da fuskarshi garesa ya zuba masa ido, cikin dakiya yace "plx wazaka kira?" Alhasan ya bashi amsa a takaice. "Alhaji babba..." Ab'ilal ya girgiza masa kai cikin karfin hali, yace " karka kirashi pls,..." Alhasan yace "why?" AB'ILAL ya cije lefe kansa na kara masa nauyi, kasa kasa ya fara mgna. "Karka kirashi plx ynzu inka kirashi, hnklinshi ze dawo nan ne, Kaga kuma gobe zeje kano, a kn maganar dawowar Auwal hubb nan garin..." Ya karashe mgnr da kyar, seda alhasan ya matso da Kunnenshi kusa dashi kana ya iya jin me yake ce masa. Jim alhasan yy kana yace "to shikenan, ynzu me kkeso kaci kasha mgni plx, kasan de banason ganinka a wannan yanayin wlhy? Ciwonka kafiya ba wanda ya isa ya saka kayi, a haka zaka samu sauki plx?" AB'ILAL yayi shiru hadi da maida fuskarshi gefe guda kawai, se ganin surar hilwah yakeyi a jikin bangon. "Na tsaneki..'' AB'ILAL ya fadi a bayyane cikin fitar hayyaci,sam be ankare da cewar mgnr da yayi ta fito fili ba, Alhasan dake saurarensa ya zubo masa ido Fuskarshi ta cika da mamaki, hadi da dumbin tambayoyi a zuciarsa , tunani yakeyi shin menene AB'ILAL ya tsana?" Wato kmr de yadda tunaninsa ya basa akwai wata a kasa. "Wacece ka tsana frnd?'' Alhasan Ya jefowa AB'ILAL tambaya. Ajiyar zucia AB'ILAL ya sauke me mugun ddh, yaja gwauron numfashi, yayi jim jim, ya sauke ajiyar zucia ya lumshe idanuwansa. Alhasan ya kara jefo masa tambayar daya masa a baya,cewa wacece ya tsana, shiru AB'ILAL ya masa danshi a zahirin gaskia besanma mgnr tasa ta fito ba. Alhasan yaja bakinshi yayi shiru kawai, yana nazarin rayuwar AB'ILAL daga jiya zuwa yau, kunna krtun alqur'ani yayi, shi har ynzu tunani yakeyi iskokaine. Da kyar ya samu ya lallaba AB'ILAL ya dansha tea kadan shima seda yace ze gayawa Alhaji babba, sannan ya samu yasha dan kadan, wanda ko yaron goye baze isheshi ba, alhasan ya bashi mgnin da dr yace a bashi ya koma ya kwanta ynajin jikinsa kmr ba nasa ba. Alhasan ya jona burner din turaren wuta domin yasan mutumin da mugun son kamshi kmr jinnu, lumshe ido AB'ILAL yayi ba karamin jin ddn kamshin yayi ba, hadda hkn yasa yake Nacewa gidan auwal hubb, a ko da yaushe kamshi yakeyi kmr gidan shuwa arab, koda yake shuwa su biyu bayan indians da larabawa a son kamshi da bakatsinen mutum. Kimtsa dakin Alhasan ya shigayi saboda mutumin uban yan son tsafta ne, karya ne kaga ko tsinke a bedroom dinsa ko bathroom dinsa, shi
Chapter 41 · 0% Book details