← Book details Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 225

Sashe 101

Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

A kn daddumar Amihh ta sameta data idar da sallarh seta koma ta kwanta, a hk Amihh tazo ta sameta. da knta ta tasota zuwa toilet ta kara mata brush suka dawo dakin ta jawota jikinta a hk tayi feeding dinta da superghetti Jlp wadda taji kayan lambu da kifi bushshe da namah, ta danci ba lefi, sbda Amihh ta matsa mata, a karshe ta bata magunguna na zazzabi dade wanda zesa taji dadih a jikinta. Hilwah ta mata godia yana daya daga cikin abubuwan dakesa Amihh karason hilwah komi aka mata seta nuna halin Katsina wa dukda ita ba bakatsiniar bace, wato karamci, bakatsinen mutum be manta alheri, kuma akwai raya alheri da alheri. Komawa hilwah tayi ta kwanta kan daddumar ta kudind'ine da hijjabin jikinta , Amihh tayi juyin dunia kn ta hau bed, hilwah taki hawa ta kara ce mata nan yafi mata ddh, nanko ta ciki na ciki bata da yadda zatayi ne kawai amma ita ason samunta ne ta koma kn bed din sam bata saba da kwancia a kasa ba, ballantana ma ynzu datakejin jikinta duk babu dadih kawai tana manage ne. Badan Amihh taso ba ta batta nan kasan sbda ta kula hkn takeso ta lullubeta da duvet din gadon data gnshi a kasa inda AB'ILAL ya wurgardashi, amihh ta mata sannu kana ta juya ta fice a dakin ta nufa side dinta da trea din a hannunta, dazata wuce falon ko kallon inda yake bata kara yiba tayi ficewarta. Amihh na ficewa ta cire duvet din data lulllube mata jikinta dashi ta jefashi can kasa kusa da bed din, zuciarta cike da tunanin warning din AB'ILAL gareta, sam bata mantaba, tasan har abadan bazata taba mantawa ba, domin ita akwaita da riqon Abubuwan Alheri dana sharri.

Amihh na ficewa a falon ya taso ya isa yayima falon key luck , ya koma ya zauba bisa kushin din daya tashi ya daura kafarsa daya kan daya yanata aikin karkadata kmr dan sarki, jefi jefi seya juya ya kalli kofar dakin yarinyar jira yakeyi yaga fitowarta dan Aiwatar da aiyukan daya bata, amma yaji shiru har kusan mintuna talatin suka shude, mikewa yayi rai a matukar bace, ya nufa bedroom din nata, ya turo kofa ya shigo yana haki, idanuwansa suka sauka a knta tana kwance kan daddumar duk tabi ta kara kudindine knta a cikin hijjabin dake jikinta, idonta biyu sam bata ko rintsesu ba sbda tunanukan dake ranta bata tunanin zasu batta ta rintsa, yana shigowa dakin taji gabanta ya yanke yayi wani irin MUMMUNAR faduwa, seda takai hannu ta dafe kirjinta tana me jin zuciarta kmr zata fashe. Wani irin mugun kallo AB'ILAL yabita dashi wadda yafi na dazu zafi, kallo daya ta masa ta dauke knta tin shigowarsa sbda tsoro da firgicinsa daya dasa mata su ranta. "Ubanwa ya baki izinin kwancia a kn daddumar nan? Damar yin sallah kke dashi a knta itama sallar bana tunanin kinayi dan hk karki kara kunsantar inda aka tanada dan sallah kinajina kou!?'' Ya karshe mgnr hadi da daka mata tsawarsa me firgitata, nan da nan ko ta firgice bugun zuciarta ya karu, ji kkeyi fat! Fat ! Fat! Sbda kawai zallar tsoronshi dake ranta, hkn ke firgitar sa zuciarta. A matukar hasale ya iso daf da ita kmr ze takata yaci gaba da mgna muryarsa cikin matsifa da jaraba "Ina mgna dake still kina kwance, Zaki tashi ko sena Kai ciki duka, in karairayaki, in karairaya banza da hofi!'' Ya karashe mgnr cikin tartsatsi babu alamar wasa a tattare da muryarsa dashi dinma baki daya, daji tasan ze aikata abinda ya fadi. Mikewa tayi jiki na rawa tana me jin wani zazzabin yana neman kara rufeta bacin na dazu daya sauka sbda mgnin da Amihh ta bata, ynzu ga wani sabo ya bayyana sbda firgicin daya haddasa mata, kasancewar bata saba da wannan yanayin ba. Kallon tsana yaci gaba da binta tashi, yayin datayi saurin sauka daga gun sallarh ta dawo kn tiles din ta rakube gu daya , kuka takeso tayi amma hawayenta sunki zuwa, duk tabi ta takure gu daya. Ko kadan AB'ILAL beji tausantaba sema tsanarta daya karaji ta bayyanar masa. "Ke bazaki tashi ba ! ki fito ki fara aikinki ba ko sena shiga jikinki, sannan zaki fi gane yaren nawa! Yar iska kawai!'' Yayi mgnr tasa cikin tsawa, se ynzu hilwah ta tuna da aiyukan daya lissafo mata kuma yace ta farasu yau, gashi bata da lafia, jiki balle ta zucia, jiki babu laka ta fara kokarin mikewa tana ganin jiri a idanuwanta, ta wuceshi tana kokarin barin dakin taje ta fara aiwatar da abubuwan daya satan. Taba kokarin bude handle din dakin ya daka mata tawa, cikin tsana da kiyayya. " ke karuwah!'' Hilwah ta rintse kwayar idonta hadi da jingina bayanta da kofar dakin sbda jirin dataji yana neman kwasarta na zafin kalamarsa wato karuwah dayake kiranta dashi!, wlhy tanajin zafi fiye da tunanin zuciar me imani da mara imanin ma baki daya. Ci gaba yayi da mgna kwayar idonsa na knta, sam baya bari ya kalleta sosai, sede sama sama, sbda tsabar tsananin kiyayyar da yaje mata kuma yau gashi a inuwa daya dashi da karuwah ta gidan karuwai ma. "bari in gaya miki wani abu daya! Ki bude kunnenki kiji ni nan Bana mgn biyu a rayuwata! So ke baki isa ki sani ba in fara a knki ,wlhy daga rana me kmr ta yau na miki mgna daya bakizo kin aiwar da abinda nasaki ba se na lahira ya fiki jin dadih! Stupid!'' Ya karashe kmr ze karasa ya watsa mata mari, jin ya gama mgnrsa ya sata daga masa kai kawai zucia bb ddh ta fice a dakin ganin yana da niyar kmr ze mareta, ta fice da sauri ta nufa saman upstairs din side din nasa, matakala daya ta taka taji ta gaji ta tsaya ta huta tana me ganin jiri, a hk a hk da kyar da kyar harta samu ta gama hayewa, ta iso babban falon dake saman, taganshi tsaf tsaf ba alamar ko da tsinke a kasa, ta nufa aikin zagaye bedrooms din dake saman, duk ta gansu tsaf sbda ba a taba shigarsu ba, duk da kyar take komi, ta dauki tsintsiya ta shiga aikin share falon dukda taga babu ko da tsinke, amma tayi sbda cika umarninsa, tana cikin sharar ya hayo saman upstairs din dan ganin wani iskncin take masa ya riga yayima knsa alqawarin uzzura mata koda ta halin qaqane. Tsayawa yayi ya harde hannusav a kirji ya zuba mata ido, ba tare data dago ta kalleshi ba taci gaba da sharar da hannun hagu Kai dagani kasan bata saba da ko da riqe tsinin tsinken tsintsiyaba balle ta iya sharar. Kallon takaici AB'ILAL ya bita dashi a zucia yace ashe bata iya komi ba sede ta bude kafa ta bawa maza wawakeken gindinta suci su bar bnza inda yake. Daka mata tsawa yayi "a gidan karuwan haka ake shara!!!'' Tsabar firgici da tsoro batasan sadda ta wurgar da tsintsiyar Dake hannunta ba ta mike tsaye jiki na rawa, sbda mgnr tasa. "Baza ki ci gaba ba sena kusa karyaki! yau ko zaki mutu sekin gyara ko ina a gidannan, yanzu ma kk fara ganin whlar rayuwa bade kn yadda an hadaki dani ba, to tabbas ni ne naqasar rayuwarki!'' Ya karashe mgnr ko gezau beji ba a ransa na girman kalmar daya gaya mata. Dago kwayar idonta tayi ta zuba masa, kawai se taji hawaye takai hannu ta share ta tsugunna ta dauki tsintsiyar taci gaba da sharar tana haki, daman ga jiki bb ddh ga zazzabi ga rashin sabo da whla, gashi tanayi yana daga nan yana daka mata tsawar dake gigita mata lissafi. A whlce ta gama share falon, suka nufa daya daga bedrooms din, inda yake tsaf tsaf amma seda ya hargitsashi yace kuma ta gyarashi dole, nan ta hau aikin gyarashi tana haki wani tayi dai-dai wani tayi mistake ya daka mata tsawar dake hargitsa mata lissafi, dole ma ta gyarashi yadda yake sbda tsurewa, koda ta gama gyara dakin ana kiran magrib, a gurguje ya karasa ya b'ata dukkanin sauran dakunan kana ya sauka kasa, domin zuwa masallacin sallarh magrib byn ya buga mata warning kn kada ta yadda ya dawo ya sameta bata gama gyara ko ina ba a gidan. Barinaikin tayi ta nifa toilet tayi alwala tayi sallah a gurguje ta idar, ta koma dayan dakin ta fara gyaransa tanayi tana hutawa, har de ta gama da kyar be dawo ba, ta koma dayan dakin tana cikin gyaransa ya dawo bayan anyi sallarh isha'i harma ya jima a masallacin ya dawo ya ga bata gama ba, aiko nan ya rufeta da balbalin bala'i da matsifa kmr ze daketa, a wannan Karon hkri ta rinka basa amma ina ai kace zugashi akeyi, se kara dagewa yakeyi yana mata tijara dacin zarafi, da hk har suka gama da gyara nan saman tayi mopping lokacin ana neman 10:30am ne, a matukar gajiye take ga matsifarsa ga tijararsa ga uban aikin, wai a hk ma danba datti da ace da datti batasanma yazatayi ba, sam ita bata saba whlr nan ba, yau ce rana ta farko data taba aiki a rayuwarta tin zuwanta dunia, ko tsinke bata taba kaudawa ba se yau, aiko ta whla zakasha ko ita tayi gaf aikin dunia. Yasata gaba suka dawo nan kasan, seda ya hargitsashi sosai kana yace ta gyara, a gajiye ta shiga gyara falon, hatta da kujeru seda yace ta matsar ta share falon, ai duk tijararsa seda ya batta, sbda bazata iya ba, a yadda y fahimta ko ledar pure water akace ta dauka da wuya ta iya dauka, tanayi tana ganin jiri harta gama kimtsa nan falon, suka nufa bedrooms nanma seda ya yamutsasu kana yace ta gyara komi a mazauninsa, ta shiga aikin gyaran tanayi tana haki, harta gama gyara dakuna ukun, suka koma dakinsa nanma tsaf yake amma seda ya hargitsashi yasata gyarashi tana gyarawa yana cewa be masa ba, seya taso mata da matsifa, rnr fa tsaye suka kwana sbda azabar fada da matsifarsa, se 4:30am ta gama gyaran ko ina har kicking da store seda ta gyara, Kana ya barta ta nufa bedroom dinta nan ta tadda trea me dauke da kulolin abinci, nan take zuciarta ta bata Amihh ce ta kawo mata ko salwah, ilai kuwa salwah ce tazo ta ajiye mata Amihh ta aikota tin 7;am taga bata gnta ba se tayi tsammanin ko tana bedroom din AB'ILAL ne, amma kuma batasan meya kaita bedroom din nasa ba, da wannan tunanin ta bar side din koda ta isa seta gayawa Amihh ta kai kawai bata tambayeta komi ba ita ma bata gaya mata kominba. Tana karasowa dakin ta zube kasan tiles tana sauke ajiyar zucia a matukar whlce har numfashin ya ya chnza zuwa na whla, kwanci kawai tayi tanajin wata iriyar matacciyar whla a tattare da duk sassan jikinta, rintse idanuwanta tayi bayan ta kwnta rub da ciki, se ynzu ta tuna batayi isha'i ba ta yunkura zata mike amma ta Gaza mikewa kawai ta koma ta kwanta tanaji ana kiran asubahi amma ta gaza tashi tayi sallarh bayanta ya riqe ya k'age se faman aikin mata ciwo yakeyi infect ma tanajinsa kmr ba nata ba, ba bata lokaci baccin whla yazo ya sureta ya tafi da ita garin whla daman da whlar ya sameta a tattare da ita dan hka ya isar da ita zuwa garin whla, dmn hkn take duk a yanayin da bacci ya sameka a hk ze tafi dakai kuma ya isar dakai ga yanayin da kake.... Goganma be rintsa ba, seda yy sallarh asubahi a masallaci ya dawo side din nasa, yana mejin zuciarsa wasai full da farin cikin abinda yayima hilwah. Karasowa bedroom dinsa yayi, ya zaunawa yayi karatun alqur'ani har 7:am kana ya kwanta yanajin sassaucin damuwar dake tattare dashi, sbda ya fara rageta a kn ita tushen dmwar tasa, a ranshi yace ynzu ma aka fara game din...''yana me aikin kissima irin abubuwan daze ci gaba da mata bacci me mugun nauyi da ddh yazo yayi awon gaba dashi....
Chapter 101 · 0% Book details