Sashe 107
Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
hilwah ta shiga rokonta tana mata magiya, kan karta gayawa Amihh, salwah tace seta gaya tinda bata gaya mata me yah ab'ilal ta mata ba, hilwah ta fashe da kuka tana rokon Salwah kn karta gayawa Amihh, Salwah tace to kawai sbda hilwah ta tsagaita daga kukan nata, da kyar kuwa ta samu ta tsagaita daga kukan nata, zuwa lokacin ta fara jin axababben ciwon kai na gefe da gefe biyu na knta, dan hk ta amshi hakurin da Salwah ta bata tayi shiru ta dau na annabawa, Salwah ta zuba ma hilwah kunun gyada da kosai ta tura mata gabanta, zuba musu ido hilwah tayi bata taba cin kosai ba gaskia kwara ma kunun gyad'a ta taba sha da tana gidan dandi wata rana kankana ya taba siyo musu. Mikewa tayi da niyar taje toilet tayi brushi salwah tace ina zata je ta bata amsa da brushi zatayi, salwah tace okay, ta bita da ido harta shige bathroom din jiki babu kwab'i, se tausanta ya kara ratsata salwah, ta rafka uban tagumi a zucia tana me adduarh Allah ya sakawa hilwah ga AB'ILAL tama mnta cewar shidin wai dan uwanta ne. Hilwah ta fito tazo ta zauna ta fara shan kunun gyad'an Amma sam bata kai hannu ga kosan ba sbda bata iya cinsa, ko tace ma bata taba ganinsa ba se yau, ita inbama datazo gidanba bata cin Abincin ire ire hkn, nata fa ban kankana ke dafa mata amma a gidan Amihh ta koyi cin Abincin iri irin wad'annan..Salwah ta tambayeta meyasa bazataci kosanba, hilwah tace bata taba ma ganinsa ba balle taci. Salwah ta bita da ido da mamaki a ranta tace "baki taba ganin kosai ba? kosai ne fa? ko de baki taba ciba?'' Salwah ta tambaya hilwah. "Ban taba ganinshi ba se yau..." Mamaki ya kara cika salwah jin hilwah tace bata taba ganinsa ba, ita de bata taba ganin dan nigerian dayace be taba ganin kosaiba se hilwah. "Kici kinji dea akwai ddh...'' Hilwah ta girgizawa Salwah kai kawai alamar ah'a, salwah ta bita da ido har lokacin se mamaki takeyi a ranta. Hilwah ta dansha kunun gyad'an da salwah ta zuba mata Rabi ta ajiye cup din tace ta koshi salwah tace ta dan kara mna ta girgiza mata kai, Salwah ta mike hadi da cewa bari inje in kawo miki magani naga alamar kinada zazzabi na maleria ne da ciwon kai, duk fuskarki tayi wani kubul kubul, bnsan ina kk samu sauro ba ya cijeki ba..., bari in kawo miki magunguna, har na ciwon jiki ma..." Hilwah ta daga mata kai alamar to, salwah ta fice a dakin hilwah na kallonta harta fice ta koma ta kwanta, nan kn carpet din jiki a sanyaye, ko ina nata ciwo yake mata,...abubuwan da AB'ILAL ya mata tin zuwanta gidan har zuwa ynzu suka shiga tariyowa a cikin kwakwalwar kanta, hk kawai takeji a zuciarta ta tsaneshi kmr yadda ta tsani mutuwarta, tasan itama ya tsaneta dan hk ta kara tsanarsa bisa kn tsana, bata taba tsanar wata halittaba a rayuwarta kmr yadda ta tsani AB'ILAL.