← Book details Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 225

Sashe 97

Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau kimanin 4days kenan da zuwan Hajiya karama gidn, ta bar hajiya maryam da nazarin shawarar data bata na ta hada hilwah da mijinta gu daya. Hajiya maryam ta kira hajiya Juwairriyya kan ta kara bata shawara a kn shawarar da hajiya karama ta bata, nan ita ma tace mata ta hadasun zasufi shakuwa. Hajiya maryam taji ddhn hkan, sede tana zullumi kan kada gogan yayita zalintar hilwah, hakade tace bari tayi kasada in taga da zalinci seta dawo da ita side dinta. Ba tare datayi shawara da hilwah ba balle AB'ILAL, ta kira masu gyara gida, daga companyn turawa tasa aka canza kaf kayayyakin furniture din Side din AB'ILAL hatta da tsarin komi seda aka canza. da TV seda aka chanza aka zuba azababbu masu azabar kudi da kyau. Ranar Gogan benan ya fita zuwa office dinsa dake nan kd, zesa hannu a wata takadda daza a kaita zuwa kasar American, a can uban gidansa yake. be dawo gida da wuri ba,har seda yaga tafiyar takaddar kana ya dawo gidan 9:3pm, ya shigo falonshi a gajiye, se faman jan tsuki yakeyi, inda ace a kano ne bazeyi whlr nan ba. da yayi ba yau....tunaninshi ya tsaya cak yayin daya shiga karewa falon kallo yana me shakar kamshin dadin dake falon, Nan take ya fahimci an canza komi ne na falon, yasan Aikin Amihh ne, to meyasa tasa aka chnza masa kaya bayan shi bece a canza masa ba....yana nan tsaye yana wannan tunanin Amihh tayi sallahma ta shigo falon, ya amsa hadi da juyawa ya zuba ma AMIHH ido , tana gama shigowa falon hilwah ma ta shigo sanye da riga iya guiwa mara nauyi, sede fa ta amsheta ainun, komi ya fito ya bayyana real Aini, kallo daya AB'ILAL ya mata ya dauke knsa daga knta nan take yaji duk wani sauran annuri dake kn fuskarshi ya gushi. "Amihh meyasa aka chnza min furniture din falo?'' AB'ILAL yayi mgnr da Hajiya Maryam murya cike da jaraba. Ba tare da Amihh tabi ta knsa ba, ta karasa ta zauna kan kujerar 3ct. hilwah ta tsaya cak knta na kasa, se aikin sharar kwallah takeyi tinda Amihh tace mata zata dawo side din take kuka har ynzu amma kukan nata besa amihh fasa abinda tayi niya ba, shine ynzu ta taso ta gaba dataji shigowar AB'ILAL gidan, can suka bar salwah a falo itama tana kuka, sam bataso komawar hilwah side din AB'ILAL ba. "Taho nan ki zauna...."cewar Amihh datayi mgnr da hilwah tana me nuna mata kusa da ita, hilwah ta gaza motsi tanaji gabanta nata tsananta bugu.. AB'ILAL dake tsaye Yanaji kamar zuciarsa zata fashe dan takaicin ganin hilwah a side dinsa me tsarki. Dadin dadawa kuma yaji amihh tace wai ta zauna masa a kn kujera, cikin sanyin jiki yaga hilwah na kokarin karasawa ta zauna kmr yadda Amihh ta umarceta, ranshi ya harzuka cikin tsawa yace "Karki kuskura ki zauna min a kan kujera! Nan ba gidan karuwai bane!" ya fadi a matukar harzuke. Nan take hilwah taja ta tsaya tana mejin hantar cikinta na kad'awa jikinta ya hau kakkarwa ta gigice sbda tsawar daya mata ta firgitata Ainun, zata iya cewa tinda uwarta ta haifeta ba a taba mata irintaba, nan take hawayen dake kn fuskarta suka kara yawaitar gudu, hadda shashsheka.

*Ya Allahu ka yadda na sauke nauyin jama'arh lafia😍.....*
08/01/2022 à 18:24 - SAADATU BINTU ABDULLAHI: 30***
Amihh dake zaune ta zuba ma AB'ILAL ido, tana mejin zafin kalamansa ji takeyi kmr ta tashi ta rufeshi da duka sbda takaicin zafin ya kira hilwah karuwah, idanuwanta takai ga hilwah wadda keta kuka, hkn se ya karawa Amihh zafi a ranta harma ta gaza mgna sbda takai karshen bacin rai. "Get out of my side pls! Banason ganin marasa tsarki '' AB'ILAL ya dakawa hilwah tsawa, cikin tsanah, da kiyayyah , ko ganinta besonyi a side dinsa, ko yace ma a duniarshi. Jiki na rawa Hilwah ta juya tana kuka da niyar tabar falon Amihh tace "karki sake ki fita a falon nan, tinda shima kasar bata ubanshi bace!'' Amihh ta fadi cikin kunar zucia, mgnr tata ta karawa Ab'ilal takaici, da kunar rai. hilwah taja ta tsaya ba tare data juyo ba se faman sharar kwallah kawai takeyi, tana shashsheka. Yayinda shashshekar tata ke kara batawa Amihh rai, dawo da dubanta tayi kn AB'ILAL daketa faman huci kmr ze fashe. "Idan ka kara kiran yarinyarnan da karuwa Allah ya isa tsakanina dakai!'' Amihh ta fadi cikin matsifa murya babu alamar wasa, sbda tsabar takaici har idanuwanta sun kankance, matsifa na cinta. Jin kalaman Amihh AB'ILAL yayi kmr saukar aradu a cikin zuciarsa, wai yau a kn wata karuwah ne uwarsa ke masa ALLAH ya isa. "Amihh ni kikayi ma Allah ya isa?'' AB'ILAL ya maimaita zuciarsa cike da tsanar hilwah. Hajiya Maryam ta daura kafa kan daya irin na tijarar nan, ta kankance idanuwanta ta fara mgna tana numfashi sbda jaraba, ji takeyi a ranta AB'ILAL be taba bata Mata rai ba irin na yau, ashe duk iskncin baqsnta matan, daya rinkayi a baya ne. "Nan gaba tsine maka zanyi kuma duk a kan Dan hakin daka raina din!" Ab'ilal ya zaro ido zucia na kuna yana me maimajta kalaman amihh a zuciarsa Takaicinsa daya daya zamana sbda karuwah mara tushe Amihh ke neman tsine masa albarka, nan ya dankare a tsaye. Hilwah se aikin shashshekar kuka kawai takeyi zucia bb ddh, bata tabajin zafin kalami ba kmr yadda taji zafin kalamin AB'ILAL gareta a yau, tabbas ya bar tarihi a rayuwarta , kalmar karuwa daya jefeta dashi ita tafi komi bata mata rai ita ta sata kuka, ji takeyi kmr zuciarta zata fashe. Amihh taci gaba da mgna a harzuqe"Idan har bazaka zauna lafia da yarinyarnanba, nidakai bazamu zauna lafia ba har abadan! In kanaso kasan wacece ni dan ubanka kayi abinda kaga dama ga yarinyarnan! Baka sanni bane, bakasan wacece niba, se in har ka kuskureni a kan yarinyarnan a nan ne zaka gane wacece ni! Gatanan ta dawo nan side din naka har Abadan, dan ALLAH Muhammad ka kwad'ata ka cinye! Kaga in zaman nigeria zeyu gareka!'' Amihh na gama fadar hkn ta mike ta fice a falon cikin zafin zucia. Ajiyar zucia ya sauke rai babu dadih, ya zubawa bayan hilwah ido, wadda ke tsaye har lokacin kmr mutum mutumi, kallonta yakeyi amma tsanarta na yawaita a zuciarshi. kwata kwata hilwah bata yima Ab'ilal ba, se ynzu yake kara tabbatar da cewa ita din karuwa ce, duba da yanayin kayan jikinta, riga iya guiwa se mayafi data yane knta dashi, wai a hk ne take yawoh kuma Amihh na gani Amma a hk ace me Tarbiya ce, kuma wai matarsa, shi bega ma abinda yaja hnklin Amihh ba gareta ta makala masa ita, in tarbia ce bega alamar taba a tattare da yarinyar, dauke kwayar idonshi yayi a kn jikinta dmn ba itan yake kallo ba, tsinanniyar rigar dake jikinta yake kallo, tsanarta ta kara yawaita a zuciarsa, juyawa yayi jiki babu laka zucia na juyayi, yayinda sbda bacin rai ko ganin gabansa ba yayi sosai...a hk har ya isa bedroom dinsa, a kn tamfatsetsen bed dinsa ya kwanta, yana me dafe knsa dake masa wani irin azababben ciwo, harga Allah yasan Amihh ta shiga hakkinsa , ta hadashi da abinda ranshi beso, Ta shiga hakkinsa ta kuma ta shiga hakkinsa, abin dunia ya hadu ya masa yawa, Gashi beda katafus tinda yaji mgnr tsinuwa jikinsa ya kara masa sanyi! Can cikin zuciarsa da ransa da jinin jikinsa ji yakeyi kmr ze maceh, zuciarsa se kuna takeyi yayinda yaketa maimaita kalaman Amihh a ransa wai wai yau shi take ikirarin zata tsine mawa a kn tsintacciyar mage, mara tsarki wadda ta rayu a cikin sab'on ubangiji! Takaici ya rufesa! Inside ji yakeyi kmr ya hadiye zucia ya mutu, ko ya samu sassaucin bala'in dake ransa.

Tanajin sadda ya bar falon har lokacin se hawaye takeyi tana shashsheka. Nan kasan tiles din falon ta zube ta fashe da wani matsanancin kukan da batasan dalilin dayata yinsa ba, ji takeyi kmr ranta ze fita, kukan takeyi hadda majina tasan de halin da take ciki beci ace tana wannan kukan ba kmr ranar fitar ranta, zata iya cewa bata tabayin kuka me cin zucia ba kmr na yau. Nan kasan tiles din dakin ta kwana tana kwallah sam bata rintsaba, ga sanyin kasan tiles din na ratsata ga sanyin AC amma sam hkn be dametaba... Kmr yadda ta kwana bata rintsaba hk ya kwana be rintsaba, kwana yy yana nafilfili, da asubahi ya fice zuwa masallaci ya gnta kwance a kn tiles din falon amma be bi ta knta ba ya fice a falon, zucia babu dadih, Da ace yanada yadda zeyi ya bar ganin yarinyarnan da yayi, ko ya samu farin cikinsa ya dawo rayuwarsa.. Tanaji yazo ya fice a falon, yana fita ta tashi zaune da kyar kmr me ciki zucia babu ddh, yayinda takejin knta ya mata mugun nauyi Kmr ze fashe, a daddafe ta iya tashi tsaye, idanuwanta sun kumbure, fuskarta fara sol seda tayi ja jawur, ji tayi jikinta ya mata nauyi sbda sanyin data kwasa a kasan tiles din falon. Da dafe bango ta karasa cikin dakin daya zama mallakinta, komi nata nan amihh tasa aka kawo mata, dakin ya hadu iya haduwa, bathroom ta fada ta hada ruwan dumi tayi wanka a,daddafe ta fito tayi alwala kana ta dawo dakin, tanajin jikinta ya mata dama dama sede dan zazzabi datakeji a jikinta, shiryawa tayi cikin doguwar riga irin ta yan hutu mara nauyi, tasa hijjabi ta nufa inda aka tanada danyin sallah, ta tada sallarh asubahi, ta idar ta jima tana lazimi da addu'ur'inta, bayan ta shafa nan kasan daddumar ta silale tanajin zazzabi na neman kamata sosai, rintse idonta tayi tana tunano kalmar da AB'ILAL ya jefeta dashi Na karuwah! Taji wani siririn hawaye na zirarowa daga kwayar idonta, se aikim sauke ajiyar zucia takeyi na kwanan da tayi tana kuka,,,tana nan kwance baccin whla yazo ya tafi da ita, baccin takeyi amma kuma bame dadih ba, again kuma ga zazzabi na nukurkusarta, se kudindine jikinta takeyi da hijjabin jikinta, datayi sallarh dashi bata cire ba.
Chapter 97 · 0% Book details