Sashe 43
Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
A daren Ranar kwata kwata hilwah bata rintsaba, hatta da sallarh daren gazawa tayi, kwana tayi tana shaye shaye, cocaine taci ubanta, ta shaqa iya shaqawa har seda ta fara hawa mata kai, Kankana da knshi ya dauke cocaine din ganin tana neman kashe knta bayan kwalebanin codeine datasha sunkai roba biyar,,amma ina ita a lokacin ma kari take, nema tablet dinta na rage sha'awah kam tasha kusan balli hudu a tashi daya amma sam bata ji sassauci ba se uban zuba kawai takeyi kmr an bude karshen fanfo, tsuliya ta kawo ruwa iya ruwah,, yadda ta kwana bata rintsaba hk kankana Ya kwana be rintsaba, ita ta kwana dashi a rnta, kankana kuma ya kwana da tunanin meke damunta a ransa,...kafin zuwa asubahi jikinta yy laushi knta kuwa se qoqarin barazanar tarwatse mata yakeyi. Da asubahi duk yadda taso ta tashi taje tayi sallarh asubahin gazawa tayi, jikinta duk yabi ya saki, sam bata jinma zata iya mikewa ta tsaya da kafafuwanta amma dukda hkn tunaninsa da kyakyawar surarsa basu iya ficewa a bangon zuciartaba, tini surarsa ta manne a bangon zuciarta ba tare data mata iso ba, sam ko shawara ma bata nema ba. Bayan asubahin zazzabi me zafi ya rufeta nan da nan ta hau rawar sanyi, kankana ya kula da hkn se hnklinsa ya tashi, ya nufa bedroom ya dauko bargo ya dawo ya lullubeta, still bata bar rawar sanyin ba, budeta yy ya taba jikinta yaji yy mugun zafi, nan hnklinsa ya tashi, ya lalubo Wayarshi ya kira Amal , kira uku kana ta iya dagawa a make take, tana rungume cikin jikin Khamilah a tamfatsetsen dakin hotel din. ta kara wayar a kunne byn ta daga, ba tare da kankana ya jira tace komi ba ya shaida mata halin da hilwah ke ciki, aiko gama fadi beyiba ta diro daga kan bed din da wayar a kunnenta ta zura slifas dinta, da wata iriyar kafurar rigar bacci a jikinta, ta dauki bag dinta da car key dinta, khamila ta zuba mata ido ganin tana kokarin ficewa a dakin, dmn duk tanajin me kankana ke cewa ta wayar, adduarh ta shigayi ALLAH yasa hilwah ta mutu kowa ya huta. A gigice amal ta figi motarta kirar zamani me mugun kyau me, new design, kalar motar maroon ce. A hnya ta kira kankana ta tambayesa suna gidan DANDI ne yace mata suna gidan hilwah ba tare datace komi ba ta katse wayar.ta juya kan motarta zuwa gidan hilwah din, a cikin tsananin tashin hnkli take tukin harta isa gidan, tayi hon me gadi ya bude mata ta shigo ko packing din arziki batayi ba, ta fito daga motar hannunta riqe da wayarta key din motar ma a ciki ta barshi. Tana shigowa falon ta samu hilwah a kwance a carpet se kankana dake zaune saman knta, Amal na ganinta lullube da bargo ta kara gigicewa tana fadin "Meya same ta plx..." Ta karashe mgnr hadi da karasowa inda hilwah take ta zauna ta bude fuskarta tin kn ta kai hannu tiririn zazzabin dake jikinta ya doketa, hnklinta ya kara tashi ta kara tambayar kankana meya sameta ne...Kankana da duk ya shiga dmwa uwar daki ba lafia ya kwashi lbrin yada yazo ya sameta jiya ya sanar da Amal, Tausan Hilwah ya cika zuciar Amal bata ma fahimci me kankama ke cewa ba, tace ma kankana "Mu kaita asibiti kawai..." Kankana yace "okay..." Daga hk ya tashi ya ciccibi bargon da hilwah wadda ta fara ficewa a hayyacinta sbda zafin zazzabi bata masan zuwan Amal ba, ya fice da ita daga gidan Amal na biye dasu a baya, da hnzari ta karaso ta bude Musu gidan baya a motar ya sakata kana ya shiga ya rungumota jikinsa. amal ta shiga dreva seat taja motar a gigice suka fice a gidan, me gadi kam se kallon ikon ALLAH yakeyi a ranshi yana tambayar knshi ko waye ba lafia oho.... Asibitin kudi mafi kusa Amal ta nufa hnklinta a tashe sbda ciwon na hilwah ya matukar gigitata, ..suna isa asibitin aka amshesu hannu biyu biyu ba wani bata lokaci aka shiga bawa hilwah taimakon gaggawa, Kankana da Amal se aikin zagaye suke a kofar dakin da hilwah da doctor suke ciki kai kace me naquda suka kawo...cikin lokaci kankani aka bawa hilwah taimakon gaggawa akasa mata drib kana aka bata daki, kankana da Amal kam iyakar damuwa seda suka shiga. Amal ta tsaya bakin bed din da hilwah ke kwance har wata rama tayi kmr Wadda tayi ciwon sati biyu, dukda hkn kyaun fuskarta be ragu ba har ynzu yana nn 100% sema kyau data kara, tayi haske hasken rashin lafia, kankana dake zaune kan kujera ya rafka uban tagumi hannu biyu biyu ya zubawa hilwah ido wadda keta sauke numfarfashi, shi Tsoronshi Allah tsoronshi kada hilwah ta mutu a kamashi a kaishi maqarqama domin kuwa cewa za ayi shi ya kasheta musammanma in case din ya fada hannun police....kwanansu biyu a asibitin aka sallamesu hilwah ta samu sauki sosai amma tunanin wannan guy din be bar taba, sosai dr ta mata natsiha kan ta rage shaye shaye da tunani, duk binciken dr din ya tabbatr mata da hilwah na shaye shaye, kuma damuwa ce ta sata a wannan ciwon datayi, hadi da taimakon shaye shayen. Alhaji buluwasi yazo tin kafin a sallameta a asibitin shi ya biya komi kana suka dawo gida da Amal wadda keta bata kulawa a kwanaki biyun, khamilah ko gaidata batazo tayiba..kwanan buluwasi daya a garin kaduna ya juya ya bar kasar byn ya cika hilwah da mahaukatan kudade, domin a wannan tafiyar ze jima sosai. Amal da kankana suka ci gaba da bawa hilwah kulawa domin har zuwa ynzu bata koma normal ba, shaye shaye kuwa se abnda yayi gaba, kmr yadda tunanin guy din kullum keta kara habbaka a ranta, tunani guy din ya zamar mata abinci kuma abin sha, kawai taji a rnta tanaso ta kara ganinsa a rayuwarta koda sau daya ne...