← Book details Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 225

Sashe 71

Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

zucia, fiye da yadda kukan uwa ke taba zuciar uwa. Saukowa kasa amih tayi ta rungomo hilwah jikinta tana me tsananin jin kaunarta har cikin kasan zuciarta. Nan ta shiga bubbuga mata baya da sigar rarrashi... Seda ta kwashi 30mnt tana jikinta tanata shashekar kukan da batasan dalilinsa ba, amihh nata aikin rarrashinta, da kyar ta samu ta sassauta kukan nata, ta hau aikin sauke ajiyar zucia, salwah dake tsaye ta gaza zama dmwarta taci uban ta hilwah ita ya dace tayi kuka sbda ita tasan waye AB'ILAL kwata kwata babu alamar sauki a lamarinsa.... hilwah da Salwah rnr wuni Sukayi jiki a sanyaye zucia babu dadih, musamman ma Salwah harga Allah tafi Hilwah shiga tsananin damuwa, hajiya maryam kam zuciarta wasai se tarairaya ta musamman take ta bawa hilwah tana kwantar mata da hnkli da cewar bazata bata abinda ze cucetaba..hkn yasa hilwah jin ddh a ranta ta barwa Allah lmrinta, da daddare kwana sukayi suna ibada, hilwah da Salwah a dakinsu, hk ma Hajiya maryam dake dakinta, kwana tayi tana gayawa ubangiji hadi da masa godiya. Taji dadih sosai na yadda Hilwah ta amince da zabin Nata, ta zama sirikarta, mafarkin hajiya maryan ya zama gaske, na son ganin AB'ILAL yayi Aure....duk seda sukayi sallar asubahi kana suka samu suka rintsa, har zuwa lokacin hilwah bata bar tunani tunani ba a ranta, Sede bacci barawo, a yau tana missn cocaine dinta sosai, tasan da ace akwaita ko ita ta shaqa taji ddh.. Washegari 12:pm amihh ta tashi da adduarh a bakinta, wayarta dake bedside drower ta dauko tayi dealing number din AB'ILAL.... tashin shi daga bacci kenan shima sbda be samu ya kwantaba seda yayi sallarh asubahi, jiyannan duk se a hnkli yake jinsa, ko office ma beje ba, sbda yadda zuciarsa keta beating da karfi , be taba jin irin hkn ba se a jiyan. Wayarshi dake bedside drwer ta dauki rurin neman agaji, zumbur yashi zaune jin yanayin ringing din na Auwal hubb ne, jiki na rawa ya jawo wayar tashi ya tsurawa screen din wayar ido, Sunan Auwal hubb ya bayyana a kn fuskar wayar, wani irin ddh yaji hadi da mamaki, ya manta yaushe rabon da Auwal hubb ta kirashi a rayuwarshi, har kiran ya tsinke be iya dagawa ba saboda mamaki hadi da farin ciki, shi a zatonshi ynzu ta sauko ne gabaki daya, tana missn dinsa shiyasa ta kirasa. Kara daukar ringing wayar tayi, ya amsa ya kara a kunne "Auwal hubb...hayaty..." Wadannan kalaman guda biyu suka fito daga bakinsa, murya dauke da mamaki. "Ina so in ganka a kd yau...." Ita ce kalmar data fito daga bakin hajiya maryam daga cikin wayar. Gaban AB'ILAL ya yanke ya fadi jin yadda tayi mgnr cikin tsare gida. "Lafiya?'' Ita ce kalmar data fito daga bakin AB'ILAL. Daga cikin wayar Amihh tace "Ni kake tambaya lafiya, dan dangin ubanka? Kai a ko da yaushe seka nuna zallar rashin tarbiya,... Ynzu Zaka zo dinne ko kuma seka gama wulakntani kmr yadda ka saba" cikin tsiwa hadi da bala'i tayi mgnr. "Allah ya baku hakuri...zanzo yanzu ma insha ALLAH.." Ya fadi murya cikin ladabi, can kasan zuciarsa yana me adduarh Allah de yasa lafiya. Murmushi me sauti amihh ta fitar, seda murmushi ya daki zuciarsa ya manta rabon dayaga murmishinta a rayuwarshi. "Allah ya kawowa lafia...." Ta masa adduarh, ba karamin ddh yaji ba ya amsa da ameen ta katse wayar yabi kan wayar da ido yana me tunani tunani ga ransa. "Anya kuwa lafia?'' Ya tambayi knsa, tambayar da babu amsa. Haka kawai ya tsinci knsa da son ya gagauta ya shirya yaje kd din danjin dalilin kiran, kawai de jikinsa ya basa ba banza ba. Saukowa yayi daga kan bed jiki a sanyaye, ya kara wani irin fresh sede ya dan fada. Direct bathroom nufa, 50mnt ya dauka yana wanka, kana ya fito ya shirya cikin manyan kaya, wadanda suka amshi jikinsa, ya feshe jikinsa da perfume dinsa, me mugun dadih, dai-dai lokacin daya gama shiryawar anata kiran sallar azahar dmn already yayi alwala ya nufa masallaci aka gabatar da azahar din dashi, ya dawo ya dauki wayoyinsa da car key dinsa ya fice a dakin, ya sanar da ma'aikatan gidan zeyi tafiya ne, ya rufe gidan ya bawa me gyara gidan key din gidan. , se adduarh fatan alheri hadi da dawowa lafia ma'aikatan gidan suke ta masa har ya Shiga motarshi ya fice a gidan, ya hau hanyar zuwa kaduna, zuciarta na masa wani iri, sam baya wani jin dadin knsa kawai yana driving dinne sannan yanata adduarh ALLAH yasa lafiya de Amihh ta doko masa wannan kiran, can kasan zuciarsa yasanma ba alheri bane.
Chapter 71 · 0% Book details