← Book details Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 225

Sashe 40

Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

🅿�13 AB'ILAL yayi banza dashi kmr be jishi ba nan ko yana jinsa kawai tsabar wulakanci ne, sannan bayason hayaniya kwata-kwata, Dan guntun tsuki AB'ILAL yaja,. Alhasan be daddara da reation din AB'ILAL ba ya kara tambayarsa meke damunsa. a matukar hasale hadi da harzuqa AB'ILAL ya tasowa Alhasan "karka dameni kaji na gaya maka, ina ruwanka da abinda ke damuna, nifa munafunci ne banaso, in kasan zaka damenine,,se in tashi in bar maka gidanka, tinda ba gidana bane!" Ya karashe mgnr a mugun hasale still kwayar idonshi na kallon saman rufin dakin irin na zamani,kai kace bada Alhasan yake mgnr ba. Ba karamin batawa Alhasan rai mgnr AB'ILAL ta karshe tayi ba Amma seya jure ya shanye ma ranshi kawai ya tashi ya fice ma a dakin, ya nufa dayan dakin da niyar a can ze kwana sbda yasan yau suka kwana a daki daya da AB'ILAL kwana zasuyi suna fitina iri iri. Nan ma daki ne wanda ya amsa sunansa daki yaji kayan furniture mahaukata irin na bugawa a mujallah, daman idanuwanshi cike suke da bacci dan hk ya yada zango a kan dankareriyar katifar data zagaye gadon, ya lumshe idanuwanshi da niyar yy bacci amma baccin ya gagareshi saboda tunanin halin da AB'ILAL yake ciki childhood friend dinsa, tabbas inda amana baze iya bacci ba. mikewa yayi jiki a sanyaye ya sauko daga kn bed din, ya saka slifas dinsa ya nufo dakin da AB'ILAL yake kwance yadda ya barshi hk ya sameshi still idanuwansa a rufe, duba time yy yaga wuraren 1:am mamaki ya cika masa zuciya , inda normal normal ne da ynzu yana sallarh ko kuma yana bacci zuwa 2:am ya tashi amma yau gashinan ya zama kmr bashi ba, kai kace mutum mutumine, duk yabi ya sukurkuce a ciki lokaci kankani ya zama kmr wani gunki. Alhasan be daddaraba ya karaso bakin bed din ya zubawa AB'ILAL ido har wata rama yayi a wannan yan awannin, launin idanuwansa suka rikide zuwa kalar ja amma ba jawur ba. "Frnd Dan Allah ka gayamin meke damunka, ka sani a damuwa wlhy..." Alhasan yayi mgnr kai daji kasan da gaske yana cikin damuwa fiye da wadda ma ya fadi da bakinshi. AB'ILAL yayi shiru kawai a wannan karon ma yana jinsa, kansa yayi masa nauyi azabar ciwo kawai yake masa kmr ze fad'o kasa, amma dukda hkn tunanin yarinyar da tsanarta sun gaza barin zuciyarshi. Gabaki daya Alhasan ya shiga damuwa ya karasa ya zauna gefen bed din , kwayar idonshi ta gaza ko kyaftawa daga kan fuskar AB'ILAL wadda ta dan tasa ma se ynzu alhasan din ya kula da hakan, wato fuskarshi ta dan kumbura. "Dan ALLAH ka gaya min meke damunka plx...." Alhasan yayi mgnar still cikin damuwa yake kmr wanda uwasa da ubansa suka amsa kira. Mgnr da alhasan ke masa a saman kai ba karamin kara masa ciwo yakeyi ba, dan HK ya lumshe idanuwansa daya gaza lumshesu tin tini, sbda beso ya hasko surar hilwah, aiko yana lumshe kwayar idon nasa ta fado yanar gizo gizon idanuwamsa a gigice ya bude idanuwansa kmr wanda fatalwa ta masa gizo ya sauke nannauyar ajiyar zuciya ita kanta ajiyar zuciya inze sauketa, to da isah da izzarta take fitowa kai kace shi din sarki ne, danyafi karfin dan sarki. Alhasan ya kai hannu yana kokarin cirewa AB'ILAL hannun daya rufe fuskarshi dashi AB'ILAL ya kwace hannun a razane dan gani yakeyi kmr hilwah ce ta tabashi da hannunta mara tsarki, a razane ya juyo da kwayar idonshi ya kalli alhasan wanda ya firgita saboda yadda AB'ILAL ya razana daya taba masa hannu. Bude baki Alhasan yayi da niyar yayi mgna, AB'ILAL ya dakatar dashi da yatsun hannunsa guda biyu na hannunsa na hagu, a yadda kawai ya dagowa Alhasan yatsun guda biyu yasan beson ya kara mgna ne, kuma inya kara mgnr yasan zasu samu matsala dan haka yaja bakinsa yayi shiru kawai ya miqe ya fada bathroom din dakin ya dauro alwala, ya fito ya isa ga abin sallah ya hau nafifilin nema wa abokinsa sasaucin abinda ke damunsa zuwa ynzu Alhasan ya fara tunanin kila ko jinnun dake kan AB'ILAL ne zasu bayya kansu daman ya jima yana tunanin anya kuwa ba Aljana bace ta Auri AB'ILAL ashe kuwa hakan ne, aljanar ce, tinda gashinan yau zata bayyana kanta, a cewar alhasan daketa jero nafilfili se zancen zuci kawai yakeyi. Daya kai raka'ah biyu yayi sallahma yy addu'ur'insa, kana ya miqe ya nufa inda ab'ilal din yake yaga yadda ya barshi hkn yake har zuwa yanzu ajiyar zucia ya sauke shima ya kasara side drower ya dauki wata wayarshi kirar i phone me kyau ita anyita ne danjin abubuwa, shi kuma Alhasan ya maidata tajin karatun alqyr'ani me girma. Ya kunnata ya saka karatun alqur'ani me girma cikin suratul bakara nan da nan kira'arh ahamad sulaiman ta fara tashi cikin daddad'an sauti muryarsa, ta karade gaf dakin, alhasan ya saita volume din karatun dai-dai kana ya mayar da wayar ya ajiyeta a inda ya dauketa, still tana karatun alqur'anin. Wani irin sanyi AB'ILAL ya faraji yana sauka a duk sassan jikinsa sanadiyar karatun alqur'anin, seda ya lumshe idanuwansa yana me bin karatun a zuciarsa, Alhasan ya juya ya koma kan daddumar yaci gaba da nafilfilinsa zuciarsa cike da tsoro kada de iskar dake kannasa ta tashi sbda karatun alqur'anin dayasa, a tunninshi in iskar dake kan AB'ILAL din ta tashi, ze figeshi ne yayi sama sama dashi ya dakashi da kasa, dan yasan aljanu karfi garesu, dan haka Alhasan daya kai raka'ah biyu yayi sallahma seya juyo ya kalli AB'ILAL seya ganshi yadda ya barshi still kwayar idonshi a rufe take gam. Alhasan seya juya yaci gaba da sallarhshi a hk har asubahi ta shigo dukkaninsu basuyi bacci ba, a bangaren AB'ILAL sam bejin ddn jikinsa ne, ji yakeyi kmr zazzabi ke neman rufesa tunanin yarinyar ne ya haifar masa da hkn, gashi ya gaza dena tunanin nata. Jefi jefi se aikin saukar ajiyar zucia kawai yakeyi kmr dan damben daya ci duka kuma ya fadi wasa. Jin ana kiran sallarh shiga masallaci sallarh asubah yasa Alhasan dakatawa daga nafilfilin da yakeyi yayi addu'ur'i ya shafa ya mike da counter a hannunshi yana istigfari ya nufo inda AB'ILAL ke kwance jiya eyau, daga dukkanin alamu bemasan an kira sallarh asubahin ba, har zuwa lokacin idanuwansa a rufe suke, se aikin sauke ajiyar zuciya kawai yakeyi, kur alhasan ya kureshi da ido nan take ya gano jikinshi na dan kakkarwa alamar zazzabi. "Subhanallahi!'' Cewar Alhasan ya karasa da hannunshi ya shafi goshin AB'ILAL nan take ya jishi ya dauki zafi rau rau, kmr an hura wuta, da hanzari ya kashe AC din dake dakin, ya dawo kan gadon ya zauna gefen gadon hadi da tambayarsa "Zazzabi ne ke damunka kou? Ka tashi ka daure kayi sallah kasha mgni plx...." Ya karashe mgnr muryarsa cike da rauni hadi da dmwa. AB'ILAL ya sauke ajiyar zucia kawai yana sauraron me Alhasan ke cewa, daman shima yanaso ya tashi kodan yayi sallarh asubahi dukda beji kiran sallarh ba amma jikinsa na basa lokacinta ya karato. A hnkli ya yunkura ya tashi zaune hadi da bude kwayar idonshi tar a kan hannayensa dake zaune bisa cinyoyinsa, ji yayi kaf jikinsa ya masa nauyi musammanma kanshi daya ke jinsa kmr ze fado kasa ya tarwatse, idanuwansa suka masa kmr an sa dank'areren dutse, wato sun masa nauyi. Alhasan ya zuba masa ido tabbas akwai abnda ya faru da abokinsa gagarumi, domin kuwa be taba ganinsa a irin wannan yanayinba , ko ciwo yakeyi baka isa ka gane ba sbda tsabar dauriyarsa amma a lokaci kankani duk yabi ya susuce ya rasa gane kansa. "Bari in temaka maka ka tashi frnd..." Yy mgnr yana kokarin temakawa AB'ILAL dake yunkurin tashi tsaye, dakatar dashi AB'ILAL yayi, Alhasan ya dakata hadi da zuba masa ido kawai, ya yunkura ya tashi jiki babu laka , se tangal tangal yakeyi kai kace faduwa zeyi, wanda be sanshi ba se yasha ko ciwo yasha wato kmr yayi jinyar sati biyunnan haka duk yabi ya saki daga jiya zuwa yau. Slifas din alhasan ya saka a hnkli ya fara takawa harya isa bathroom din dakin yayi tsarki, ya dauro alwala ya fito da kyar, a hnkli yake taka kafafuwansa. yana fitowa alhasan ya fada toilet din ba jimawa ya fito shima, bega AB'ILAL a dakin ba hkn ya bashi tabbacin ya fita ne domin zuwa masallaci dukda kuwa besan inda masallacin yake ba amma masallaci baya taba boyuwa. zuwa lokacin an tada raka'arh farko ta sallarh asubahi. Ficewa shima yayi da slifas a kafarshi ya nufa masallacin dake kusa da gidanshi daman basu da nisa da masallacin. Yana shiga yaga mutuminsa a sahun farko , karasawa yayi yabi sahun baya aka ci gaba da sallarh dashi amma ya rasa raka'arh farko dole seda in an idar shi kar yayi sallahma ya tashi ya kawo wadda ya rasa. Suna idar da sallarh ko adduarh beyi ba sbda azabar sanyi da yakeji ya mike yana ganin hanya na haduwar masa biyu biyu uku uku hudu hudu, ya fice a masallacin se ambaton sunayen ALLAH kawai yakeyi, ya koma gidan Alhasan. A bedroom ya yada zango a daddafe ya lullube da bargon dake kan gadon still se rawar sanyi yakeyi, yayinda haqoransa ke hadewa da junansu, sam shi bame yawan yin ciwo bane, zan iya cewa kafin yayi ciwo da woya, dan haka shi da knshi yy mamakin rikicewar jikn nasa. A haka alhasan ya dawo ya samesa dmn Allah Allah ya rinkayi ya idar sbda yazo yaga a wani hali yake ciki. Cikin hanzari ya karaso bakin bed din ya zauna ya zuba masa ido ta cikin bargon still jikinsa se rawa kawai yakeyi sbda tsabar zazzabi, a hnkli Alhasan ya zame bargom daga kansa yana fadin "subhanallahi! Frnd zazzabi ne me zafi halah ya kamaka... Plx ka daure ka tashi muje asibiti dan Allah...." Alhasan ya karashe mgnr a firgice saboda zafin zazzzabin Jikin AB'ILAL daya dakeshi tin kafin ma ya kaiga kai hannunsa jikinsa, da sauri ya maida hannun nasa baya saboda zafin zazzabin jikinsa yayi yawa. AB'ILAL yayi saurin jan bargon inda Alhasan ya yaye masa ya kara lullube kansa yanajin wani irin
Chapter 40 · 0% Book details