← Book details Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 225

Sashe 109

Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Koda salwah ta karasa dakin kwance ta samu hilwah a kasan carpet din tini ma bacci ya dauketa, se sauke ajiyar zucia takeyi dagani a wahalce take ajiyar zuciar. ajiye mata mgnin salwah tayi ta dauko duvet din dake kan bed din, ta lullubeta dashi, ajiyar zucia hilwah ta sauke ta kara kudindinewa a cikin duvet din tana me kara sauke ajiyar zucia, hadi da shashsheka. Salwah ta tsaya ta zuba ma fuskar hilwah ido, kasancewar bata lullube fuskar tata ba. Zucia cike da tausan hilwah salwah ta ta tsugunna ta dauki trea din data kawowa hilwah breakfast din ta juya ta fice a dakin, ta nufa side din Amihh, direct kiching ta nufa dan hada abincin rana sbda yau zataje scul tanada lecture 2:am, kiching din ta isa ita da Ma'aikatan gidan suka shiga hidimar abincin ranar....

A bangaren AB'ILAL Be samu bacci ba kwata kwata sede ya gaji da juyi ya tashi dan knsa wuraren 10:30am ya sauko daga kn bed din , yana me jin knsa na juya masa na rashin baccin da beyi ba, fadawa bathroom yayi, seda ya kwashe 1h a bathroom yana wanka, kana ya fito bayan ya dauro alwala, ya goge jikinsa sosai, kana ya shafa kyakyawan lotion dinsa ya shirya cikin danyar shadda mint color dinkin kaftani, dinkin ya matukar amarshi ainun, kasancewar yau juma'arh ce shirin zuwa masallacin yakeyi. ya feshe ko ina da ko ina na jikinsa da perfume , ya dauki hula ya kafa wadda ta dace da tsarin shaddar dake jikinsa, fuskarnan tasa ta fito das, sajensa ya kwanta luf se shining yakeyi yana walwali, ya hadu iya haduwa! Nan take ya fito a zallar asalinsa na me kyau, kallo daya zaka masa ka fahimci cewa shi din ruwa biyu ne Wato de ba zallar nigeria bane shi, sbda kyaun nasa ya shahara, ya fito sosai zanensa ya zanu tako ina cif cif das das, shu'umin kyau garesa hadi da makirin kyau tako ina ya cika taf, yanada cikar haiba, kyaunshi na bugawa ne a mujallah , ya hadu iya haduwa, ko a indian film ban taba ganin me kyaunshi ba. dauko makirin watch dinsa yayi ya daura a tsintsiyar hannunsa, ya kara fashe jikinsa da turarensa, ya zira takalminsa me mugun tsada, ya kara fashe jikinsa da perfume dinsa, again and again sbda shi din ma'abocin kamshi blne, baya gajia da kamshi. ya dauki counter dinsa dake kn mirorr da car key ya fito falon se zuba kamshi yakeyi, dai dai agogon bangon falon ya buga karfe shabiyun rana dai-dai. tsayawa yayi ya zubawa inda ya bar yarinyar dazu tana kuka da ido , kawai se yaji jikinsa ya masa wani iri se hasko yarinyar yakeyi a durkushe a gun, rintse kwayar idonsa yayi na wasu yan daqiqu kana ya budesu jiki a sanyaye ya juya ya fice a Falon, fitowa compound yayi, yana takunsa na isa tamkar dawisu ma'aikatan gidan nata miko masa gaisuwa amma sam be bi ta knsu ba, tafiyarsa kawai yaci gaba dayi, shaddar nan tasa se faman walwali takeyi tana daukar kwayar idon me kallo. Direct ya nufa packing space karasawa yayi cikin gareji ya fito da motar daya sewa hilwah daman key dinta ne a hannunsa, yasa me wankin mota ya wanke masa ita yana daga nan zaune a kn wata kyakyawar kujera ta hutawa dan Ustaz ne ya dauko masa kujerar ganin da yana tsaye. yana daga zaunen yana danna wayarsa har aka gama wanke motar aka gogeta dmn batayi wani datti ba sbda ko a garejin an lullubeta da rigar mota. shiga motar AB'ILAL yayi ya figeta ya fice a gidan ya nufa babban masallacin santan bello, daman a nan yake juma'arh inhar yana nan kaduna....bayan sun idar da sallarh ya fito suka hadu da Alhaji babba, kasancewar shima a nan masallacin yake sallarh juma'arh. Karasawa AB'ILAL yayi ya gaidashi dukda haushinshi yakeji sbda yasan hadda sa hannunshi a auren da Amihh ta masa, bayan sun gaisa Alhaji Murtala ke tambayar AB'ILAL ya iyalin tasa, AB'ILAL yayi kmr be gane me yake cewa ba, ya canza akalar hirar zuwa ga tambayarshi yaushe ze koma kasar USA sbda a can ake duba masa lafiar jikinsa..'' Alhaji babba yace yana tunanin se Nan da 2 month ab'ilal ya jinjina kai kawai dmn ya kawo mgnr ne dan ya canza akalar bnzar tambayar da alhaji babba ya masa. Daga bisani yama Alhajin sallamah ya nufa motarshi ya shiga yaja ya bar masallacin , shima Alhaji babba ya shiga tashi motar dreva yajashii subaka bar masallacin. Ab'ilal na isowa gidan direct side din Amihh ya nufa dan samawa knsa abinda zeci, yana shiga dai-dai salwah na riqe da trea tana shirin barin side din zuwa side din AB'ILAL din domin ta kaiwa hilwah abincin rana. AB'ILAL Yayi kmr ma be gnta ba. ta gaidashi yaki amsawa kawai ya nufa dinning ya zauna, salwah na nan tsaye tsakiyar falon kmr an dasata, ta daga kafa da kyar ta fara tafiya da niyar ta fice a falon, ta tsinkayi muryar AB'ILAL na cewa "Ke zo kiyi serving dina...'' Jiki na rawa Salwah tace to ta dawo ta ajiye trea din dake dauke da abincin hilwah a kn dinning table din, ta fara bubbudewa AB'ILAL kulolin dake kan table din, abinci Kala biyar ne amma AB'ILAL yace duk basu masa ba. Ya umurce salwah data shiga kiching ynzu ta dafa masa tuwan shinkafa miyar kubewa danya. Takaici kmr ze kashe salwah gashi tanaso ta kaiwa hilwah abincinta a hk ma tasan ta batta da yunwa, gashi tanaso taje scul tanada lecture 2:am gashi ynzu ma 2:am din ta kusa befi 15mnt ba 2:am din tayi. Zucia babu ddh kuma ba damar ta nuna ta juya da niyar ta shiga kiching yace ta fara hado masa coffee tace toh kawai ta juya ta nufa kiching din, a gaggauce salwah ta hado masa coffee din ta kawo masa yanata aikin shafar wayarsa kirar Samsung, ta ajiye masa ta shiga kiching din ta fara kokarin daura masa tuwan xucia babu dadih, tasan de yau tayi missn lecture dinta. Se faman jin haushi takeyi tana aikin tuwon ma'aikatan gidan suka temaka mata gun hada masa tuwon, ta samu ta gama takai masa taga ko coffee dinma besha ba, se faman shafar wayarsa yake har lokacin, ta zauna tana jiran sadda ze gama yace tayi serving dinsa tasan bata isa ba ta bar falon batayi serving dinsa ba. Seda ya mula ya mulmule kana yace tayi serving dinsa, tana gama serving din nasa AB'ILAL ya fara cin tuwon a yangance Salwah nata satar kallonsa se yatsina fuska yakeyi, ya dauki cup din coffee din ya Kai bakinsa yaji ba ddh sbda sanyin da yy, ya kalli salwah yace taje ta kara hado masa wani, Jiki na rawa Salwah ta juya ta koma kiching din ta kara hado masa wani coffee din, ya amsa ya fara sha, ya kalleta yace taje ta masa farfesun kayan ciki yanzunnan..a zucia salwah tace ta shiga uku, kana ta juya ta nufa kiching ta shiga aikin hada masa farfesun Hilwah ce kawai a ranta tasan yunwa nacan tana kwakularta, mkrntarta ta yau kam tini ta hkra da ita...
Chapter 109 · 0% Book details