← Book details Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 178 OF 225

Sashe 178

Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Suna cin abncin daren suna hira suna raha, har suka kammala,,AB'ILAL be wani ci ba sosai, se juya spoon din hannunsa kawai yakeyi yayinda hoton bayanta daya gani yaketa masa yawo a cikin kwakwalwar kai, gabaki daya ya hanashi sukuni. 10;30pm ya musu sallama ze tafi gida. Alhaji bashir yace "Aah alaji ka kwana a nan mna, mu Ai munsha kwana zakayi ..." Hjya karama ma ta amshe da "nima Nasha kwana zeyi, har inasa dan ladidi ya gyara side dincan .." AB'ILAL ya girgiza musu kai kawai alamar Ah'a. hjya karama da alhaji bashir suka sashi gaba kn ya kwana, su Son samunsu ne ma yy 1week, AB'ILAL daketa duba agogon hannunsa yaki amincewa da hkn badan sun so ba, suka rakoshi har motarsa hjya karama na shirin bude baki tace masa bari a kira maka m..." Ya katseta ta hnyar shigewa motarsa sam beson ta kara ma masa magiya kn ya kwana a gidan, danshi a zatonsa cewa zatayi bari a kira mahaifiyarsa, nan ko so takeyi tace bari a kira masa matarsa suyi sallahma, sam AB'ILAL be jira ta kara mgna ba, ya kunna motarsa, ya sauke glashin motarsa, ya kara musu sallahma,,suka masa fatan sauka lafia, ya fice da motar a gidan, se kallon side din hjya kadama yakeyi ji yakeyi a ransa kmr akwai wani abu na fannin rayuwarsa a side din nata.. Hjya karama da alaji bashir suka nufa side din Alhajin bayan ficewar AB'ILAL a gidan.

Tinda suka shiga dakin dazasuyi sallar magrib, basu fito falon ba a dakinsu suka ci gaba da kallon series dasukebi a Zee World din. Haka kawai hilwah taji yanayin jikinta ya sauya ta rasa dalilin hkn, ga bugun zuciarta dake tsananta time to time, se jan numfashinta takeyi sbda kamshinsa datakeji a hancinta, ta rasa daga ina kamshin nasa yake zuwa gareta, se tayi tunanin ko kamshin nasa ne ke mata gizo kmr yadda shidin yake mata gizon. A daddafe tayi sallar isha'i salwah na ankare da ita, da canzawar mood dinta, byn sun idar da isha'i salwah ta tasata da tambaya kn meya sameta, meyasa mood dinta ya canza, hilwah tace mata ciwon kaine kadan, ta fadi hkn ne sbda t huta da tambayoyin salwah, tasan inba hkn ta fada mata ba, bazata barta ba. Sannu salwah ta mata, itama ta shiga dmwa ta hada musu goldenmoon sukasha lokuta da dama shi suke sha basu cika cin abncin ba da daddare. Bayan sunsha goldenmoon din Salwah ta bawa hilwah magunguna na ciwon kai, ta amsa tasha sbda tabbas kn nata na mata ciwo, bayan tasha mgnin ba jimawa bacci me nauyi ya sureta, itama salwah ba jimawa bacci me nauyi ya sureta, nan kasan carpet ita ta kwanta, yayinda hilwah ke kn bed ta kudindine cikin duvet. 12:am ta farka a nannauyan baccin daya sureta, ta tashi da matsanancin k'ishi, ta sauko daga kn bed din, ta nufa frij ta duba taga ruwansu ya kare se uban drinks a cikin frij din, ta fice a dakin ta nufa falon gidan, wani irin mummunar faduwar gaba ta tsinci knta a ciki, sbda kamshin jikinsa daya cikata Ainun, Ji tayi kafafuwanta suna neman gagarar daukarta ta lumshe kwayar idonta ta zubawa kujerar 3ct ido, hk kawai take ganinsa a zaune kmr yanai mata gizo, jingina bynta tayi da bango mafi kusanci da ita, ta rintse kwayoyin idanuwanta hadi da sauke gwauron ajiyar zucia me dauke da numfashi,,,,tafi karfin 30mnt a wannan yanayin , kana ta iya jan kafafuwanta da kyar ta isa ga frij din falon ta budeshi ta dauko ruwa na gora, ta juya zata koma bedroom dinsu ta juyo ta kalli kn kujerar 3ct din, tabbas kamshin nasa dake falon yana neman zautar da ita, duk a tunaninta kamshin nasa ma gizau yake mata a hancinanta guda biyu, jiki a sanyaye ta nufa dakinsu ta isa ga gefen bed ta zauna ta bude ruwan ta kafa bakinsa a kn bakinta ta fara kwalkwala yayinda har zuwa ynzu kamshin jikinsa be bar hancinta ba, tasha ruwan kusan rabin gora kana ta mayar da murfin gorar tana rufewa tana tunaninnika a zuciarta, ji tayi ciwon kn dake knta ya dawo sabo dal, har wata juwwa taji tanaji, ta koma ta kwanta tana mejin kaf idanuwanta ma babu bacci a ciki, kawai ta kwanta ne ta lumshe kwayoyin idanuwanta har wani kara jawo numfashinta takeyi sbda kamshinsa dake cikin hacinayensa har zuwa ynzu,,,wad'ansu tunaninnika suka shiga zirya a cikin kwakwalwa me aykin dake cikin knta, ta kai hannunta na hagu ta dafe knta tana jero salatuttuka ga shugaba Annabi muhammadu S.A.W, kana daga bisani ta daura da istigfari, ta rufe da hailala, hk kawai taji wani irin dadih a ranta, zuciarta ta mata wasai da wasu tunaninnikan sede har ynzu babu bacci a kwayoyin idaniarta , amma zuciarta ta watsake,,ada ta cushe da abubuwa da dama, ta gyara kwanciarta, ta koma ga hannunta na dama, kawai surar guy din keta yawo a duniar tunaninta, "Handsome!'' Ta fadi hkn a bayyane tana wani sakin shu'umin murmushi, da surarsa tazo tunaninta seta tsinci knta a faffad'an murmushi... Mikewa tayi still tana sakin murmushi me tattare da Annuri ta nufa bathroom, ruwa me dumi ta hada tayi wanka da abubuwanta na kamshi, ta gama wankan ta dauro alwala ta fito sanye da bathrobe, dai-dai salwah tazo juyi idanuwanta suka sauka a knta, tarr ta bude idanuwanta a knta masu cike da bacci, duba tamfatsetsen agogon dake ajiye a bed side tayi, taga ya nuna 1:39am, ta dawo da kwayoyin idaniarta kn hilwah dan kara tabbatar da wankan ta fito kmr yadda taga tana d'iga. "Me rabin suna wanka kkyi?'' Hilwah data karasa ga drawer din kayansu ta juyo ta kalli salwah dmn ta kula ta tashi a baccin tin fitowarta daga toilet. "Yeah wanka nyi .." Hilwah ta bata amsa tana kokarin zumbula doguwar riga ta bacci me mugun kyau, kalar milk me ratsin peach. "Meya sameki na wanka by this time.?" salwah tayi tambayar se faman zabgo hamma takeyi. Hilwah ta gama saka rigar ta dauko hijjabi ta saka tana fuskantar Salwa tace " Au se abu ya sameka kake wanka da daddare....'' Cewar hilwah. Salwah tace "A mana, ko yah AB'ILAL yazo ne..." Hilwah ta gallara mata harara tana mejin wani kala a jikinta, har alwalarta ma na kokarin karyewa, amma tayi control tace "bani da time dinki..." Ta karasa kn dadduma ta tayar da sallarh nafilah, salwah ta bita da ido hadi dayin daria tace "Ni inada naki time din Ai..." Ta fadi hkn hadi da yunkurawa ta tashi ta nufa toilet tana fadin. "Nima bari in dauro Alwala inzo mu kwashi ladar nan tare karki barni da baccin asara....'' Ta karasa shigewa toilet din ba jimawa ta dawo daure da alwala ta nufa ma'ajin hijjabansu na sallah ta dauko ta saka, ta isa ga hilwah daf da ita ta shimfida daddumarta itama ta fara jero tata kiyamul lail din.
Chapter 178 · 0% Book details