← Book details Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 225

Sashe 103

Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Amihh ta shigo bakinta dauke da sallahma, idanuwanta suka sauka a knsa yana kan dinning din ya gama cin sakwarar kenan yana korawa da kunun aya me sanyi, idonuwansa na rashin kunya ya zubo mata, kana yace "sannu da zuwa hubb...'' Ta amsa da yawwah ba yabo ba fallasa, ta daura da cewa ''ina iyalin taka?'' AB'ILAL yayi kmr ma bejita ba, ya kauda knsa gefe, tasan kuma ya jita, ta girgiza kai kawai tace "badakai nake mgnaba!'' Ta fadi cikin tsawa, ido ya zuba mata kana yayi kasa da knsa yace "ni mgnr me kkyi min? me kkce min?'' Amihh ta hade rai tace "dangin ubanka nace!'' AB'ILAL ya kara dagowa ya kalleta ya dauke kwayar idonsa, kwafa taja kana tace "dan dangin ubanka nace ina iyalinka?'' Cikin tsiwa ta kara tambaya. Dago fuskarsa yayi yana kallon gefe ya hade rai yace "Gaskia ni Amihh a rayuwata bnsan wani iyali ba..." Hajiya maryam ta kalleshi kawai taji a ranta kmr taje ta daukesa da mari, tasan tsabar iskncine ke dawainia dashi. "Zaka sani, idan watan dazan ci maka mutumci a kn yarinyar Nan ya kama, ynzu duk ina daga maka kafa ne, Amma ina rokon ALLAH yasa ka kuskureni...a lokacik xakasan meye iyali a rayuwarka.." Tana gama fadar hkn ta nufa bedroom din salwah tana kwalo mata kira. "salwah! Xoki hadomin abinci.." Ta fadi hkn tana turo kofar bedroom din ta shigo, kicibus sukayi da Salwah wadda taji me take cewa shine ta taso cikin hanzari, dan aiwatar da abinda ta umurceta, Ja baya tayi ganin Amihh ta shigo dakin, idanuwan Amihh suka sauka a kn hilwah dake kwance kn bed din. "Sannuu da zuwa .." Ita ce kalmar data fito daga bakin hilwah cikin ladabi hadi da tashi zaune. Amihh ta amsa da yawwah fuska dauke da fara'arh. "Ashe kina nan, ya jikin?'' Cewar Amihh, da tayi mgnr cikin kulawa, tana karewa hilwah kallo har zuwa kafafuwanta. "Da sauki..." Hilwah ta amsa knta kasa. "Eh naga Alama ga kumburin fuskarma ya sabe, da kafafuwan ma Allah kara sauki.. " amihh tayi fadi cike da kulawa. hilwah ta amsa da Ameen... "Ina wuni Amihh?'' Salwah ta gaidata hadi da Rissinawa Amsawa amihh tayi babu yabo babu fallasa, ta dawo da dibanta kn Salwah, wadda ke sanye da doguwar rigar Atamfa play ce amma ta kamata ta saman nonuwanta sbda akwai nonuwan masha Allah, sede ba irin na hilwah ba ita nata irin manyannan ne masu shape din mango, na hilwah kuma masu gindin tasa ne. "Ke ina kk samo wannan rigar?'' Amihh tayi tambayar da salwah, fuska bb alamar wasa. Salwah dake tsaye knta kasa seda taji gabanta ya fadi, daman seda ta gayawa me dinkin kada ya mata matsatstsiya amma seda yayi mata, kuma ba wani kamata tayi sosai ba kawai de tasan in Amihh ta gani se ta mata mgna. "Na ce ina kk samo wannan tambad'ad'd'iyar rigar ta jikinki?'' Amihh ta kara fadi cikin tsawa. Seda Salwah ta Dan zabura kana tace "itace Wadda me dinki ya Kawo min shekaran jiya, daya daga kala takwas dinnan da kika bada a dinkamin.." Hajiya maryam ta yatsina fuska tana me kara karewa Salwah kallo kana tace "ita wannan rigar yan iskan? Ke kkce ya miki dinkin nan haka? Danni bnce ma a miki breast cup ba.." Salwah tayi saurin girgiza mata kai alamar ah'a, Hajiya maryam ta daka mata tsawa ''karya kkeyi ke kikace ya miki irinta, aike take takenki dole se an tashi tsaye a knki sam baki da alamar kunya a rayuwarki, ...last warning kar in kara ganinki da wannan rigar a cikin gidannan, inba hk ba daga ke har rigar sena yaga muku rigar tsiyah knji na gaya miki.." Amihh ta karashe mgnr tana motsa yatsunta alamar gargadi, da sauri salwah tace toh, Amihh kiyi hkri..." Bnzan kallo amihh ta watsa mata kana tace "dallah can! ki kawomin abinci daki Ynzu.." Ba tare data jira amsartaba ta fice a dakin. Salwah ta sauke ajiyar zucia, ta juyo ta nufa drower din kayanta Dan canza rigar, hilwah ta bita da ido tinda Amihh ke ma salwah fadan ta dago tanata kallonta tana kallon Salwah ita bataga aibun rigar ba, amma amihh keta wannan fadan, se yau hilwah ta fahimci AB'ILAL amihh ya biyo a fada, Amma shi ya fita. A gurguje Salwah ta cire rigar ta saka wata free ko breast cup babu, ta daura dankwali ta fice a dakin, duk ta barbaza kaya a kasa wanda ta fiddo da tana neman rigar daxata chanza , hilwah ta taso ta nufa inda kayan ke barbaje a kasa ta tsugunna kasan ta shiga aikin ninnninke mata su, ko ninkin bata iya sosai ba, sbda bata saba ba.
Chapter 103 · 0% Book details