← Book details Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 174 OF 225

Sashe 174

Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rnr nan bakin kofar Amihh ya kwana sauraye sukayi watanda dashi sam be wani rintsaba se gyangyad'i daya rinka yi, ma'aikatan gidan km rnr gulmarsa suka kasa a fai-fai. Da asubahi ya tashi jikinsa yy rad'o rad'o da cizon sauro ga wani azababben ciwon kai dayayi masa dirar mikiya ga uban jiri yana gani ya nufa side dinsa ya kama ruwa yayi alwala ya fito a daddafe cikin dauria da dakia ya nufa masallavi,,,byn sun idar da sallarh asubahin be tsaya maraji'ar ba ya dawo gidan ya koma bakin kofar Amihh inda ya kwana ya zauna zaman nade kafafuwa biyu biyu wato kmr zaman cin tuwo, ya rafka uban tagumi ba abnda yake yawo a zuciarsa se tunanin yarinyar...... 8:30am A haka Amihh ta fito ta sameshi, yana ganinta yayi zumbur ya mike tsaye, ya zuba mata ido cikin shirinta na tafia office dinta take, ita ma Amihh ta bishi da ido yadda taga jikinsa rudu rudu fuskarsa ta kumbura ya bata tabbacin a wajen ya kwana, tausansa ya ratsata sosai fiye da kullum, seta tuna da hkn fa ya bar yar mutane itama da kwana a waje, sannan kuma yayan mutane, daya wulaknta sunfi dubu, da mari da duka daga amihh ta hadasa da mace seya nemo cin mutumci ya mata, shiyasa ALLAH ya kamasa dayawa, wai a hk danma beda bakin iyaye... Amihh bata bi ta knsa ba tayi wucewarta ta nufa motarta ya biyota yana gaidata cikin ladabi da kaskantar da kai, ta amsa a takaice, yana biye da ita har suka iso bakin motar Amihhn, tana shirin shigewa motar ya rike murfin yana cewa "Auwal hubb baki gayamin ba ko kn duba kayayyakin abnda beyi ba ki fadi se a siyo wasu..." Amihh ta kwace murfin motarta a hannunsa tace "ban duba ba, kuma bazan duba ba ynzu..." Ta fadi tana me shigewa cikin motarta zata mayar ta kulle murfin ya rike murfin harma tana datse masa yatsarsa da jikin motar ba tare data ankare ba, sam beji zafin hkn ba, dukda kuwa ta datsesan sosai. "Pls auwal hubb dakin Temaka kin duba...." Ya fadi cikin marairaita..amihh datakeji kmr zuciarta zata fashe sbda tausansa amma ta hade rai tace "In kana takuramin dinnan ne ze hanani in duba wlhy ka barni in sarara mna..." AB'ILAL ya kara narkewa kalar tausai sosai cikin marairaita kmr karamin yaro yace "Shikenan Auwal hubb, kiyi hkri na bar takura mikin inkin samu lokacin kya duba...amma zuwa yaushe zaki samu lokacin?''amihh tace "se inna samun zan gaya maka...sakarmin murfin mota..." Ba musu ya sakar mata murfin motar taja ta kulle ta tada motar tayi ficewarta ya koma side dinsa cikin dmwa yy wanka, ya shirya cikin danyan yadi butter milk, ya fito hannunsa rike da car key dinsa, yana tafia kmr ze fadi sbda yunwar cikinsa, ya nufa motarsa ya shiga yajata ya fice a gidan...da kyar yake driving din, ya nufa tamfatsetsen kantin da yayi siyayyar akwatunan da kayyakin dake cikin akwatin jiya,, yaje ya kara hado wasu akwatunan dozing biyu, duk aka cikasu da atamfofi na zamani, da laces da shaddoji mnya, Masu mugun tsada da gold again da kayyaki de na alfarma, ciki hadda kananun kayan dakarin wasu panties, da bra, duk da knsa ya zabesu aka cika akwatunan 24 din da kayyaki tantsam. Ya biya kudaden kayayyakin ta hannyar tansper, company din suka masa kyautar wani tamfatsetsen gold sbda shi yafi kowa siyayya a satin. Akasa masa akwatunan A bayan motar bote, da cikin motar tasa saman kujerun baya,, ya zagaya ya shiga mazaunin driva ya fice a kantin. Ya nufo gida zuwa lokacin anata kiraye kirayen sallar magrib, byn yy paking ya kira ma'aikatan gidan suka shiga daukar akwatunan kalar mint color da silver ash, suka nufa falon Amihh dasu, ab'ilal a tunaninsa ko ta raina wadanda yasiyo ne shiyasa bata kulashi ba, shiyasa ya karo ko allah zesa a dace ta tankashi ta gaya masa inda yarnyar take, da knshi zeje ya daukkota ya dawo da ita gidansa, har gida na musamman yasa a gina masa a wani filinsa dake cikin steeving shekhari area. Aka gama kwashe akwatunan tas aka kaii Side din Amihhn wadda ta fito daga daki byn ta gama sallar magrib kawai taga akwatuna mnya mnya zuwa lokacinnan gama kwaso su daga wajen. Amihh ta tsaya ta saki baki, tana kallon akwatunan, tasan Aikin ab'ilal ne, "notikan kai sun kwance ..'' Amihh ta fadi hadi da rike haba tana kallon akwatunan, dai-dai gogan ya shigo bakinsa dauke da sallahma, amihh ta bishi da ido duk yabi ya kara rikicewa ya gigice. Ba tare daya gaidata ba ya fara mgna. "Yauwwa amihh gasunan kn gani kou?ki duba in basuyi ba a karo wasu..." Amihh ta bar mamakin lamarin nasa, ta fara tsammanin akwai rashin hnkli da rashin Lissafi a lamarin nasa. "Allah ya kyauta .." Ta fadi hadi da juyawa ta nufa kiching ta tsinkayi muryarsa yana tambayarta yaushe zata duba kayayyakin..." Ta masa bnza ta karasa shigewa kiching din. Ya juya ya fice a falon sbda beyi sallarh magrib ba ya nufa side dinsa.... Bayan isha'i ya dawo side din Amihhn ya jita rufe ya koma side dinsa ya dauko wayarsa ya kirata tana gani taki dubawa yy typing message ya tura mata kn inta ga kayan ta masa mgna, yana zaune kofar waje yana jiranta, amihh na ganin message din nasa jikinta ya mata sanyi, abin ma ya wuce tunaninta, sam bataso ya kara kwana a kofar wajen gudun kada sauraye su kara cizonsa kar su kaisa ga ciwo, Amihh tayi typing message kmr hk *Ka tafi side dinka ka kwanta inna duba zan kiraka ...* har zata tura masa se kuma ta fasa ta ci gaba da duba kayyakin akwatunan da aka kawo yau din, a Zuciarta sam ba ddh ta cushe da kunci harga ALLAH AMIHH nason ab'ilal kmr ranta, amma tafiso ta dasa masa tarbia a wannan datsin,sbda ya sakankance dayawa kwara ya koyi darasi.

Ranar ma nan bakin lofar ya kwana zaune kmr dan maraya, washe gari amihh ta kara fitowa zuwa office ta gnshi taki kallonsa sosai gudun kada ta gaza sukuni tayi wucewarta ya biyota yau ma har bakin motar, yana tmbyrta ko ta diba kayyyakin, abnda beyi ba ta fadi ya kara siyowa..." se a lokacin amihh ta dago ta kalleshi taga jikinsa rudu rudu da cizon sauro wani irin zafi amihh taji tin daga kasan zuciarta zuwa gangar jikinta, ji tayi kmr saurayen jikinta suka ciza, abnka da uwa komi ya samu danta jinsa takeyi kmr ita ya sama,,,Amihh ta kasa dannewa ta shige motarta ta fice a gidan ta barshi nan tsaye ya nufa side dinsa jiki ba owab'i. yy wanka a daddafe ya dawo bakin kofar side din nata ya zauna a zuciarsa se adduarh yakeyi Allah Yasa yarinyar tashigo da babu makawa seya tashi ya rungumeta ko ze samu sassaucin soyayyarta dake addabarsa a ransa...a hk yauma amih ta dawo ta samesa a bakin kofar side dinta tana dawowa ya tareta da ta duba kyn...amihh ta fara masa kallon mahaukaci ta shige cikin side dinta tana masa fatan samun sassauci ya biyota sbda batama dakin luck ba,, har bedroom dinta ya bita yana tambayarta ina yarinyar nan, wannan tambayar baya gajiya dayi mata ita, amihh ta masa bnza, ta ajiye bag dinta ta cire mayafinta ta fice a Dakin zuwa kiching nanma seda ya biyota yana meci gaba da tambayar tata ina matarsa, Amihh bata tangasa ba, Harya gaji ya fice zuwa masallacin sallar magrib. daya dawo daga masallacin yaci gaba da addabarta ta shige dakinta ta kulle nan falon ya koma ya zauna yana tsammanin zata fito amma bata fiton ba har akayi isha'i ya fice zuwa masallacin sallar isha'in ya dawo falon, ya zauna bisa kujerar 3st se yaji k'ishi ya ciyishi ya tashi ya dauko ruwa a frij falon ya dauko da fresh milk ya dawo ya zauna yadansha fresh milk din, kadan ganin yana neman mutuwa. Rnr nan falon ya kwana a zaune be rintsaba, har asubahi yayi alwala ya fice zuwa masallaci knsa ya masa nauyi sosai ga ciwon kai.. Hk ya rinka addabar Amihh ya koma har binta office ta tsawatar masa ta, da kyar ta samu ya bar binta har zuwa office dinta, sede kullum cikin yo akwatuna yake, kmr bada kudi yake siya ba, amihh taga haukar tasa ta wuce mizanin lissafinsa, dan hk tace ya barsu hk nan,,yace shi baxe bari ba, inde har taga ya bari to ta dawo masa da matarsa ne..." Amihh taga hauka iya hauka, ma'aikatan gidan ma sun fara tsammanin ya zare ne, dan hk dasun gansa sesu gusa, suma tsoro yake basu duk yabi ya kara figewa...yau da Amihh ta gaji ta tasashi gaba tace dole se yaci abnci, yace baze ciba shi se yaga matarsa, Amihh tayi juyin duniar nan yace baze ciba, dole hk ta barshi, sbda bazecin ba a halin ynzu ko ruwa yanasha ne kawai amma bayayi masa ddh, ayko jikinsa duk ya gama zabgewa ya koma kmr bashi ba, kullum labbansa a bushe, kmr mara lafia, side din Amihh nan yake kwana ya tashi ya wuni , wata rana a waje wata rana a falo,,sbda shi Amihh ta bar rufe kofa, gudun kada ya kwana a waje kwanan nasa wajen yana sata a tashij hnkli, da dmwa.
Chapter 174 · 0% Book details