← Book details Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 225

Sashe 54

Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Alhasan be tashiba se 12:20pm ya tashi yayi wanka ya canza kaya daga kayan AB'ILAL domin har sabbin kaya aka zuba a side din nasa. Dawowa falo Alhasan yayi sanye da manyan kaya sun amsheshi Ainun, fitowa falon yayi yanajin cikinsa na kiran ciroma, rarraba ido ya shigayi a falon yaga bega mutuminba, zuciarshi ta bashi ko yana side din Amihh ne, dan haka ya fice a falon ya nufa side Din Amihh bakinshi dauke da sallahma ya shigo, a dining area ya samu Amihh da Mom dinsa suna breakfast dmn basa karyawa da wuri, ya shiga Rarraba ido a falon ko zega AB'ILAL amma babu ko me kama dashi a falon. Karaso wa yayi ya tsugunna ya gaidasu suka amsa cikin jin dadih. "Nan kuka kwana kenan?'' Hajiya maryam ta jefo masa tambayar, daga mata kai yayi hadi dacewa "A, a nan muka kwana Amihh..." "Ina AB'ILAL?'' Hajiya Juwairriyya ta tambayesa . Dago knshi dake kasa yayi yace "Ai nasha ko yana nan ma.. Dana tashi bngnshiba..." Hajiya maryam ta tabe baki tace "Ashe be gaya maka ma ya tafi kano yau ba..dana tashi naga message dinsa Wuraren 7:33pm wai ya tafi kano...ashe kai be gaya maka bama hajiya kinga rashin hnkli irin na yaronnan kou?" Hajiya maryam ta karashe mgnr kwayar idonta na kn hajiya Juwairriyya. Murmushi hajiya Juwairriyya tayi ta fara mgna cikin dattako "Ba rashin hnkli bane hajiya, maybe ko yana baccine sanda ya tafi... Ko kuma uzurine ya kamashi na zuwa kanon uzuran uzuran, plz mu masa adduarh kawai.." Jim hajiya maryam tayi tana juya fake din datakecin Irish me dambun nama dake plt din dake gabanta, . "Allah ya tsare...." Shine abinda ta fadi tana me maida fake din cikin irrish me damubun naman dake gabanta yaji kayan lambu kai bakace wai irrish bane, da dambun nama da kwai ake hadawa a soyashi, se a zagayeshi da ganyayyuka masu amfani ga jikin dan Adam. Hajiya Juwairriyya da Alhasan suka amsa adduarh Amihh da ameen. hajiya maryam ta kalli Alhasan dake tsugunne a kasa har zuwa lokacin tace "Tashi ka zauna mana kayi joining dinmu breakfast...." Toh Alhasan yace daman kamshin duk ya cika masa hanci Yasan abinci Amihh ba baya ba gun dadih ta iya girki sosai. Tashi yayi ya zauna a kn daya daga kujerun dining din, Amihh da kanta ta tashi tayi Serving dinsa da irin abinda sukeci yayi mata godiya ya zage ya fara Kai loma ai nan fa yaji har kunnenshi na rawa.....Ranar nan Alhasan ya wuni suna ta hira tiryan tiryan da Amihh , Hajiya Juwairriyya kam bata bi ta kn hirar tasuba se kiran AB'ILAL takeyi a waya yaki amsawa, hnklinta ya tashi tace Alhasan ya Kira yaji,shima ya Kira gogan yaki amsawa. Hajiya maryam ta tabe baki tace "Daman kun bar whlr da knku a yaronnan dan ba dagawa zeyiba, yana lafia bura uba ce kawai..." Hajiya Juwairriyya tace "Anya kuwa ya isa lafia?'' Hajiya maryam ta amshe da "hmmm lafia lau, ashe hajiya har ynzu bakisan halin yaronnan bane...ai maybe ma yana gani kin amsawa ne kawai yayi..." Alhasan ya amshe da "maybe yana bacci ne Amihh..." Hajiya maryam tace "Ba wani bacci...tsabar bura uba ce kawai..." Hajiya Juwairriyya tayi murmushi tace ''ALLAH yasa bura ubar ce yana cikin koshin lafia...." Hajiya maryam tayi shiru kawai ba tare data kara mgnaba, Alhasan ya amsa da amin.daga hk ya musu sallahma ya fice a gidan ya nufa gidansa, da tunanin hilwah a ranshi, daman da ita ya kwana ya tashi a ranshi yaji kawai yana san halinta rayuwarshi, da ita knta ma yana sonta. Direct ma'aikatarsa ya nufa Wato inda yake business din saida motocinsa , ba business daya sukeyiba shida AB'ILAL sunada hannun jari a kasashen waje, da nan gida nigeria....su yan kasuwa ne...

Washe gari hajiya Juwairriyya ta koma kano, ta bar hajiya maryam da kewarta. Ranar Monday dr maryam ta fara zuwa Aikinta asibitin Nosing home, da asibitin 44, a satin ta farajin dadin Aiki da asibitocin biyu, cikin kwanciar hnkli take gudanar Da ayyukanta , tsantsar jin dadih da kwanciar hnkli ya samu matsugunni a rayuwar hajiya maryam, burinta daya ne a halin ynzu taga Auren AB'ILAL da mace ta kirki.

Tinda yaje garin kanon be fita ko kofar waje ba, Abinci ma se yayi da gaske yake iya ci, a memakon ya samu sassauci game da tunaninta amma ina, Sema abin ya karu a zahirin gaskia yasan tsanarta ce a ransa, to meyasa tunaninta ke addabarsa! Wannan tambayar yakewa knsa kuma ya gaza bawa kan nasa amsa. Yau kimanin kwanansa hudu kenan a garin kano amma Sam be gane komi a rayuwarsa shi de Gashi nan gashi nan ne, abinci ma be shi sede hollandia yoghurt yake iya samu yasha shima sbda Kar yayi mutuwar tsaye ne. 10:pm Kwance yake a kan kayataccen gadonshi duk yabi ya rame se uban haske da yayi, fayau dashi se ya canza daga black ya koma chocolate color. Sanye yake da jallabiya sky blue me mugun kyau an ma wuyan jallabiyar Aiki da dark brown ba karamin kyau ta masa ba. aikin de yakeyi Wato tunaninta dalilin hakan yasa kullum tsanarta ke yawaita a birnin zuciarsa sbda ta manne masa a zucia sam shi kuma beson ya tunata ma a rayuwarsa , da ace Ana fiddo da zucia waje dase ya fito da tasa ya wanke tunaninta a ciki, hatta da kwayar ido, da ana fiddoshi dase ya fiddo da nashi ya wanke tass sbda ya goge surarta daketa masa gizo a kwayar idonsa,..duk duniya be taba tsanar mace ba kmr yadda ya tsani Wannan yarinyar , ya tsaneta! Ya tsaneta!! Ya tsaneta!! Iyakar tsana inda abinda yafi tsana to yayi mata, kwata kwata yana nadamar ma zuwansa kd , wlhy da yasan ze ga ko me kama da ita da beje kdn ba kwata-kwata, dama yayi zaumansa a kano bakin cikin dunia ya kasheshi ya huta. Gashi ynzu yaje ya kara kwaso wa knsa wata muguwar dmwar. a halin ynzu bayajin dadin komi a duniya , shi de kawai yana duniya ne amma baya jin dadinta. sallah ce in yanayi yakejin Sanyi a zuciarsa.
Mikewa yayi a hnkli ya diro daga kan gadon ya nufa bathroom jiki a sanyaye yayin da yaketa ganin jiri, a daddafe Ya dauro alwala ya fito yana tangadi ya nufa dadduma ya tada sallah nan ya fara nafilfili ko ze samu sassaucin abinda yakeji a kasan zuciarsa. Duk a sujjadarsa seya Roki Allah ya yaye masa tunanin yarinyar amma ina! jima yakeyi kmr Ana kara masa tunaninta a kasan narkakkiyar zuciarsa...

Washe gari kankana ya sanar da Alhaji sunusi motar hilwah ta lalace, be tsaya tambayar garin yaya ba kawai Ya kashe wayar, ko awa uku ba ayiba, ya kara kiran kankana ya tambayesu suna ina ne, yace suna gidan dandi, ya kara kashe wayar. Ko 30mnt ba ayiba, wani yazo gidan da sabuwar mota yace alhaji sunusi ne yace a kawowa hilwah. Kankana da Amal da Hilwah duk suka fito nan fa suka tadda mota me kyau da tsaruwa tamafi wadda ta lalace kyau, fara ce sol irin kirar zamani ta matah, ita kanta hilwah motar ta mata kyau, kankana se rangada guda yakeyi, yan gulma nata zuwa suna ganin motar, a gabansu wanda ya kawo motar ya bawa hilwah key da sauran tarkacen motar, sabuwa ce dal ko ledartama ba a gama barewa ba. A ranar kankana ya kwashesu suka hau zagaye gari a motar suna ala san barka hilwah de shiru tayi, ta kira Alhaji sunusi ta masa godiya sosai, abinda yafi kauna a tare da ita kenan komi akayi mata se tayi godiya kullum yanada burin ya mallaki hilwah a matsayin matarsa ta sunnah amincewarta kawai yake jira. Rnr basu suka dawo gidan ba se dare, duk suka zuzzube a kan bed daman a koshe suke, tunanin guy din har ranar gobe be bar zuciyar hilwah ba, wasu lokutan tana mamakin dalilin dayasa tunaninshi ya gaza barin zuciarta kuma data tunashi seta tsinci knta a Tsananin farin ciki , tunaninshi yafi abinci da ruwa muhimmanci a rayuwarta a kullum tunaninsa kara habbaka yakeyi a zuciarta da gangar jikinta komi zatayi yana maqale a ranta, bata taba tsintar kanta a wannan yanayinba a kn dana miji se a knshi wannan shi ake cewa daga kallo daya! Kawai tanaji a jinin jikinta zata kara ganinsa, kuma zuciarta na bata tabbacin hakan. "Hmmmm..." Tayi humming hadi da sakin wani irin shu'umin murmushi around 2:pm tana zaune a kn dadduma tana lazimi bayan ta idar da raka'a biyu na nafifilin da takeyi, shine take wannan tunanin, ci gaba tayi da laziminta tanata aikin murmushi,. Yau kimanin kwanaki hudu kenan da Alhaji sunusi yase mata sabuwar motar. Amal bata nan ta koma hotel gun khamilah, kankana kuma sun tafi bikin wata yar balaja'un qawarsu a garin Katsina shida yan uwanshi D&D. Dan haka se ita Kadai a dakin kmr mayya, se yau tasan ashe mutum rahama ne, kankana ba karamin debe mata kewa yakeyiba, yau da benan se take jinta se a hnkli dakin duk ya mata girma, danma tunanin guy din na debe mata kewa, amma fa a tsorace take sbda tanada tsananin tsoro, ko motsin kirki batayi sosai a dakin.
Chapter 54 · 0% Book details