Sashe 119
Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ranar dasu hilwah suka dawo daga scul Amihh ke sanar da hilwah mijinta ya koma kano, ba karamin jin dadin hkn hilwah tayi ba, ta dawo side din amihh da kwana zuwa kafin AB'ILAL din ya dawo a cewar Amihh. Sosai amihh ta matsa gun koyawa hilwah girki a kiching kullum tare suke shiga kiching abincin dare ko weekend haka to rnr daga safe har dare basa zama, musammanma a yan kwanakinnan dasuke yawanyin baki, daga gidan Alhaji babba harshi alhaji babban ma yazo yaga hilwah ya yaba da kyaunta, se sakin zance yakeyi a gabanta, hilwah ta Tashi ta bar falon a kunyace. Hajia maryam ta girgiza kai kawai tasan Halin nasu alhajin a jini yake. A yau hajiya juwairiyya tazo garin kaduna, amihh ta mata tarba ta alheri abinci kusan kaloli biyar suka shiryawa hajiya Juwairriyya taci tasha, hirar yaushe gamo ta tsinke tsakaninsu da Aminiarta Hajiya maryam. Hilwah da salwah sukazo suka gaidata sbda dataso basunan 12:am suka bar gidan zuwa mkrntarsu amma dasu aka shirya mata abinci. nan Hajiya Juwairriyya taga hilwah aiko ta yaba da kyanta, bayan sun gaidata har sun koma cikin dakin salwah hajiya Juwairriyya ta juyo ta kalli aminiarta hajiya maryan wadda keta faman sakar mata murmushi tace "kai Aminiata, wannan shimfidediyya haka, ah dole fa ki gigice ki hada Auren nan, wannan ai kyakyawan iri ce yarinya ga kyau ga ladabi da biyayya gata kyakyawa ALLAH sarki..." Hajiya maryam tayi Murmushi zucia fal jin dadin yadda hajiya juwairiyya ke yabon hilwah taji dadin hakan sosai. "Kede bari hajiya gata nan fa tubar kallah....''cewar Amihh. Hajiya juwairiyya ta amshe da ''gaskia kam masha Allah komi yaji tako ina fam fam...." Hajiya maryam ta dan jefe hajiya da kallon kunya tace "kai hajiya wai fam fam....'' Hajiya juwairiyya tace "E mna kiga yarinya tako ina ya cika,....ko cikine da ita?'' Hajiya Maryam tayi yar Dariya tana tunawa da haka hajiya karama ma tace datazo waiko ciki ne da ita. "Hajiya wai baku gane me ciki ne? Wannan ma yaushe dannaku ya kusanceta balle tayi cikin..." Fuska dauke da rashin fahimta Hajiya Juwairriyya tace "kmrya be kusanceta ba? Kina nufin basu tare tarayyar Aure ba?'' Hajiya maryam ta daga mata kai alamar tabbatarwa. Hajiya Juwairriyya tace "kai haba de! Hajiya ke ina zaki sani, tinda de abu ne na sirri ba ganewa zakiyi ba, kila sunyi abunsu baki sani ba, ALLAH na tuba Yaushe zega wannan abubuwan ya gyale se kace ba namiji ba.... " Hajiya maryam dake sauraren hajiya juwairiyya ta amshe da "to inajin de ba namijin bane, domin kuwwa xan iya rantsewa be kusanci yarinyarnan ba, abinda ma dakunansu daban daban suke kwana, mutumin da duk yabi ya tsangwameta ya takura mata, Hajiya ta ina za ayi tarayyar Aure, wai sekace kin mnta halin yaronnan na taurin kai..." Hajiya Juwairriyya tayi jim kana tace "Haka ne hajiya, Amma ni naga yarinyar ai bata da makusa ,,,gaskia made da lefinki anfa juma dayin auren nan, to ki maidata dakinsa mna tinda de Matarsa ce halalinsa ce hajiya ba amfanin kwanan da sukeyi a rarrabe...'' Hajiya maryam tayi shiru tana me nazarin maganganun hajiya juwairiyya, tabbas mgnrta tayi kuma ta dace. "To shikenan hajiya aiko kn kawo shawara hkn za ayi,,,," hajiya juwairiyya tace "ai hkn yafi hajiya, wata rana ko ba aso dole za a kusanci juna....'' Hajiya maryam tace "gaskia ne kam Hajiya, Allah de ya tabbatar mna da Alheri,.." Hajiya Juwairriyya ta amsa da "ameen de hajia,... Gaskia AB'ILAL wani irin mutum ne, Allah na tuba da irin yaran nan ne Alhasan inajin da tin ranar da kika kai masa yarinyar nan side dinsa ze daddanne yar mutane..." Hajiya maryam ta zaro ido tace "kai hajiya karkiwa dana sharri..." Hajiya Juwairriyya tace "wlhy knji mgnr gaskia nake gaya miki, yarannan na yanzu girtsatstsune hjya, kmr suna jira a kai musu mace su far mata da sukuwa...." Hajiya maryam tayi yar daria tace "hkne kam hajiya, a week dinnan abubuwan da muke cin karo dasu kenan a asibiti yaran mata sede kiga an kawosu ranga ranga wlhy hajiya sabbin aure mazansu sun musu kaca kaca, kai yarannan namu ALLAH ya shiryasu hajiya,..." Hajiya Juwairriyya ta amsa da Ameen...ai hajiya yaran yanzu sha'awah ta musu yawa wlhy wasu kmr sayi yawo tsirara baga matanba baga mazanba..." Hajiya maryam tace "hk ne kam, matan kmr suna jira a aurar dasu hk mazanma, inma anyi sa'arh sun riqe knsu kenan, se kiga da anyi aurrn washe gari anyi barna mara kyaun gani hajiya ke kyace ko mahaukata suka zama...." Hajiya Juwairriyya ta kwashe da daria jin mngr hajia maryam na karshe tace "Hajiya haukacewa ce mna sukeyi, ba a hayyaci .." Hajiya maryam tayi kwafa tace "amma ko ALLAH wadaran lalacewar nan Hajiya mu da ai ba ayin irin wannan girtsuwwar..." Hajiya Juwairriyya tace "Ai da kikace hajiya knsan komi yana tafia ne da zamani....'' Hajiya maryam tace "Hkne Allah ya shirya mu baki daya ya tseratar damu daga fad'awa halakar zamani...." Hajiya juwairiyya ta amsa da Ameen daga hk suka ci gaba da hirarsu har zuwa sallarh magriba kana suka nufa dakin Amihh danyin sallarh. Washe gari alhasan yazo gidan, sbda maifiyyarsa data sanar dashi zuwanta shine ya iso ya kwashe gaisuwwa, a nan yaga Hilwah ya kureta da ido ita ma ta kuresa da ido dukkaninsu suna nazari ne da tunanin inda suka taba ganin dan'uwansu, se daga bisani alhasan ya tuna da inda ya gnta, ya shiga tambayar kansa me takeyi a nan gidan? Da wannan tambayar a ransa har sukaci abincin rana tare a kn dining alhasan se faman kallon hilwah yakeyi daman kwanakin baya seda ya koma gidan dandi ko ze samu ganinta amma be gnta ba, nanfa alhasan ya kwallafa rai shi a dole yagani yanaso, ba ruwanshi da inda ya ganta shide kawai allah ya jarabceshi da sonta.. Bayan sun gama cin Abincin suka dawo falo suka ci gaba da hirar su ukun alhasan dasu salwah da hilwah amihh da hajiya maryam sun shige bedroom dinsu suna tasu hirar a can. Alhasan ya samu damar kallon hilwah yadda yakeso ya rasa ta ina ze fara isar da abinda ke ransa. Harde ya kasa jurewa ya maida dibansa kn salwah yace "Sis salwah nace ita sister bata da waya ne?'' Fuska dauke da rashin fahimta Salwah tace "wa kake nufi yah alhasan?'' Alhasan yace "qawarki nake nufi, yama sunanta?'' Ya karashe mgnr kwayar idonsa na kn hilwah wadda knta ke kasa, duk hirar da akeyi ita bata cewa komi. "Hilwah kake nufi ?'' Cewar salwah. Alhasan yace ''yauwa ita sunanta kenan ashe..." Fuska dauke mamaki Salwah tace "Eh..." Alhasan ya basar kawai ganin wani yanayi a kn fuskar salwah, suka ci gaba da hira kwayar idonsa na kn hilwah, salwah na ankare dashi, mamaki ne ya rufeta ganin irin kallon da alhasan ke jifar hilwah dashi koda de ita batasan komi ba a fannin so tasan de akwai ayar tambaya a kallon da alhasan kewa hilwah, se mamaki ya kara rufe salwah ita a zatonta yah alhasan ai yasan hilwah matar yah AB'ILAL ce tasan ko yah AB'ILAL be fada masa ba, to amihh zata fada masa cewar hilwah matar yah AB'ILAL ce, sbda duk wanda yazo gidan se amihh ta gaya masa hilwah matar AB'ILAL ce, bata sanar da alhasan ba ga tunaninta ko AB'ILAL ya sanar dashi kuma ya nuna masa hilwah, shiyasa Amihh bata nunawa alhasan ita ba.rnr har dare alhasan be bar gidnba sbda Hilwah, se 10:pm ya bar gidan, koda yaje gida gaza bacci yy sbda tunanin hilwah, tin ganin farko ALLAH ya jarabcesh da son hilwah, yade dannewa ransa ne kawai sbda yasan da bame yuwwa bce, kasancewarta daga gidan karuwai, ynzu daya gnta a gidansu AB'ILAL se yasha ko sunada dangantaka ne, shi fa sam yama mnta da wani Aure da akawa AB'ILAL din balle ya kawo a ransa ko matarshi ce. washe gari da sassafe Alhasan yazo gidan se akayi rashin sa'arh 8:pm su hilwah da Salwah suka nufa makaranta, alhasan beji ddhn hkn ba, seda ya zauna gidan har after asri suka dawo daya gnta se yaji sanyi a ransa, inya zauna ita kawai yake kallo ko ana hira baya fahimtar meke gudana, sbda kallonta da yakeyi,,su kuma iyayen nasa wato Amihh da hajiya Juwairriyya sam basu fahimci meke tafia ba, harkar gabansu kawai sukeyi. Rnr ma se 10:30pm alhasan ya bar gidan da karin dumbin tunanin hilwah a ranshi. Washe gari hajiya juwairiyya ta bar garin kaduna zuwa kano dmn daza tazo fly tabi hk ma dazata koma fly din tabi zuwa kano. Rnr ma nan gidan alhasan ya wuni se yammaci ya tafi. Washe gari bezo ba se wuraren yammaci sbda aiyuka dasuka sha masa kai. Wasa wssa fa Gidan fa ya zama gidan zuwan alhasan kullum da kullum ko duk bayan kwana daya, duk Dan hilwah yake zuwa, Amma sam Amihh bata ankare ba, sbda inyazo basu cika zama gu daya ba, Alhasan nason ya isar da bukatarsa amma ya rasa ta ina ze fara, se ya bar abin a ransa kawai yana ci masa zucia, yana nan de yana adduarh ranar daze bayyana abin da ke ransa.