← Book details Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 225

Sashe 69

Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hajiya maryam bata tsaya da motarta a ko ina ba se a packing space din gidan Alhaji murtala wato alhaji babba. Fitowa tayi daga motar dai-dai 10:47am ma'aikatan gidan suka hau jero mata gaisuwa wasu sun santa wasu kuma basu santaba tsoffin ma'aimatan gidan duk sun santa wato wadanda ke musu aiki tin suna katsina,. Amsawa tayi ba yabo ba fallasa ta fara takawa a cikin gidan da jagoran daya daga ma'aikatan da suka santa zuwa bangaren hajiya babbah, wato matar Alhaji ta farko. Tini ta tashi a falo ta sameta suka gaisa a mutumce, sauran matan ma dasukaji zuwanta duk sukaxo suka miko gaisuwa aka cika mata gabanta da kayan motsa baki sam Hajiya maryam ta gaza sa komi a bakinta, abinda ke zuciarta shi kawai takeso ta aiwatar ko zata samu salama. "Alhaji ya tashi kuwa?'' Hajiya maryam tayi tambayar da hajiya babba. Dattijuwar matar tace "Bansani ba de..bari a tambayi zainab muji.." Ta karashe mgnr kwayar idonta na kn Hajiya zee wadda keta faman taunar ciwgum, kmr zata taune haqoranta Sbda hajiya Maryam ta iya amsawa da mutumci. " ya tashi, yanata shirin zuwa masallaci ne..." Hajiya maryam ta zubawa zee ido wadda ke mgna tana yatsinar baki, a hkma wai a mutumce ta amsa. Hajiya babba ta kalli hajiya maryam tace "To knji ummu AB'ILAL ya tashi, na manta ma yau Friday knsan 12:30pm yake zuwa masallacin jumna'arh..." Hajiya maryam tace "okay toh bari in ganshi..." Tayi mgnr hadi da mikewa. "Toh a fito lafia..." Cewar hajiya babbah. hajiya zee ta tashi itama tabi bayan hajiya Maryam ita ta mata iso zuwa falon Alhaji babbah dayake bata taba zuwa gidanba se yau. Da sallahma ta shigo falon...Alhaji babbah na zaune kan kujerar zallar royal din dake falon 3ct sanye yake da danyar gezner me mugu mugun kyau, kalarta kalar blue ce light me kyau, hadda babbar riga, hannunshi riqe da counter yanata lazimi yayinda zallar hular zanna bukar take gefensa, karatun alqur'ani ne ke tashi a falon kasa kasa cikin natsuwa. "Wa'alaykumussalam..." Ya amsa sallahmar hajiya Maryam domin zee batayi ma sallamar ba. Ya dago ya zubawa maryam ido, zuciarsa ta cika da mamakin wai yau maryam ce a gidansa, ko gizau take masa, " tabbas yau take jumma'ah ga maryama a gidana..." Cewar Alhaji babba da mamakinsa ya gaza boyuwa. Karasowa hajiya maryam tayi ta zauna a kan kujerar dake kusa da alhaji 1ct zee ta karasa ta zauna gefen Alhajin. "Barkanku da safiya alhaji babba..." Cewar Hajiya maryam data dan rissina. Fara'arh dake kan fuskar Alhaji ta kara bayyana, farin ciki fal ranshi ya amsa da "Barka ka de maryamu matar muhammadu kuma uwar muhammad..." Murmushi kawai Hajiya maryam tayi. Alhaji babba shima yy murmushi yana me gyara siririn glashin dake kwayar idonsa ya zubawa Hajiya maryam , wadda ke sanye da siririn glashinta itama, shi dij take kallo. "Kai yau ba banzaba hajiya kikaxo gidana ... Da walakin wai goro cikin miya..." Wani irin shimfidadden kayataccen Murmushi hajiya maryam ta sakarwa alhaji babba wanda be taba ganin irinsa ba se yau, dan hk ya kara tabbatar da cewa da walakin din goro cikin miya. A natse ta fara mgna "Haka ne kam Alhaji...akwai muhimmiyar mgna da nake tafe da ita, insha ALLAH...kuma alheri ce..." Alhaji babba ya washe baki yana me gyara babbar rigar dake jikinsa yace "Alhamdulillahi ! To bismillah ina jinki..." Hajiya maryam ta kalli zee da tayi kasak'e tanaso taji gulma. Hajiya maryam ta hade rai tace ''ke dan bamu guri..." Mikewa hajiya zee tayi ta fice a falon alhaji babba ya kalli hajiya maryam yace "Ai dakin batta karamar yarinya ce batasan komi ba..." A zucia hajiya maryam tace "amma tasan namiji kou..." Amma a fili tace "A gaskia Alhaji abinda kakeyi baka kyautawa wlhy baxan fasa gaya maka ba, yaza ayi ka auro yarinya karama sa'arh kananan yaranka, ai dole ma ta raina sauran matanka..." A hasale Amihh tayi mgnr. Alhaji babbah ya washe baki yace "maryama, maryama kenan, Ai addinina be hanani auren taba..." Hajiya maryam ta amshe da ''dukda hk amma ai ana barin halak dan kunya ...." Alhaji yayi yar daria yace "Well, bazaki ganeba...ynzu de meke tafe dake..." Fara'arh Hajiya maryam data gushe ta dawo sabuwa a kn fuskarta, ta zuge bag dinta ta ciro kudade kimanin 500k yan dubu dubu ta ajiye a gaban table din Alhaji murtala, yabi kudin da kallo yan 1k 1k ne bandir bandir biyar wato dubu dari biyar, ya kalli kudin ya kalli maryam fuakatshi dauke da neman karin bayani yace " Wannan kudin na menene maryamu?"kara gyara glashin dake idanuwanta tayi ta gyara zamanta sosai fara'arh dake kn fuskarta ta yawaita tamkar gonar audiga ta kalli kudin kana ta dawo ta kalli Alhaji babbah tace "So nakeyi yau bayan an sallami sallarh jumma'arh a daura Auren Muhammad AB'ILAL da hilwah Muhammad AB'ILAL......"

*for more information...08136349646*

Gumbar madara 😋
Gumbar kankana
Gumbar Alkama
Gumbar gero
Gumbar ridi
Gumbar hatsi
Gumbar gyada
Gumbar Ayah
Gumbar me rubutun mallaka.

Tsumin tabaje
Tsumin baure
Tsumin kankana
Tsumin kwakwa
Tsumin zam-zam
Tsumin rubutu
Tsumin al'ajabu

Ingantaccen maganin infection sadidan insha ALLAH.

Ingantaccen matsi, mesa dadin gaba ga me gida, da maganin gyaran nono, maganin sa kiba, da maganin rage tumbi, maganin kara hips available.

Turaren mallala E.T.C humrar mallaka...

Masu bukatar hadin *yar gatah* komi da komi za asa a ciki na NA MALLAKA dana mgnin infection 20K 30K 40k 50k 70k 80k 90k 100k iya kudinki iya yadda zakiyi shagalinki . MATA KU TASHI KUYI GYARA SABODA MASU GIDA MAGUNGUNANMU masu inganci ne Da kyau sayen na gari maida kudi gida . 08136349646.pls karki dauki lmbata ki dameni in baki shiryaba plx.
08/01/2022 à 18:24 - SAADATU BINTU ABDULLAHI: *YAR DANDI CEH...* 🅿�20
SAADATU BINTU ABDULLAHI✍�

Alhaji babba kanshi ya kara kullewa, jin tace hilwah Muhammad AB'ILAL, to ina kuma suka samu hilwah a danginsu? Gaf Hajiya maryam ta kara kwance masa tunani, ya kureta da ido, yayinda take kara tabbatar masa da abnda ta fada a kan fuskarta. "Me kike nufi? Waye kuma hilwah ko gilwah AB'ILAL Muhammad?" "Ita ce wadda nkeso a daura Auren nata da AB'ILAL a yau..." Hajiya maryam ta fadi fuska babu alamar wasa. Alhaji murtala ya bita da ido, yasan halin maryam kaifi daya ce, sannan bata taba zuwa masa da mgna me girma ba kmr ta yau. "Da amincewar shi na ta'alah za ayi auren ko yayane?'' Alhaji murtala ya jefowa hajiya maryam tambayar. "Dukkaninsu ban nemi amincewarsu ba, ni naga hakan ya dace, kuma na bukata dan ALLAH Alhaji karka zurfafa bincike, ni nasan me na hango kawai a daura auren..." A wannan karon da sanyin murya tayi mgnar. Alhaji babba ya sauke ajiyar zucia shi be taba ganin inda akayi haka ba. "Kina nufin ita ma macen bata amince ba? Ta yaya hkn ze yu, aure babu amincewar mace balle amincewar namiji?'' Cewar alhaji murtala. Hajiya maryam tace "Wannan duk ba dmwa bane, zasu amincewa junansu daga baya, dan Allah alhaji karka kara cewa komi plx! Ni nasan insha ALLAH akwai alheri..." Alhaji murtala ya sauke ajiyar zucia beda yadda zeyi da maryam in taso abu kawai ayi shine kwanciar hnkli. "Shikenan Allah yasa hkn ne Alheri..." Cewar Alhaji murtala, hajiya Maryam taji wani irin mugun dadih ya ratsata seda tayi yar Dariya tace "Ameen...alhaji kai nakeso ka zama waliyinta in yaso se a nad'a wani a matsayin waliyin Shi yaron naku..." Alhaji murtala ya jinjina kai yana me nazarin maganganun hajiya maryam. Knshi ya kara kullewa a karo na biyu yace "ita yarinyar bata da iyaye ne?" hajiya maryam tace "tana dasu .." Alhaji murtala yace ''suna ina ?'' Hajiya Maryam ta amshe da "gani nan ni ce uwarta ni ce ubanta..." Alhaji murtala ya zaro ido zucia fal mamaki, gani yakeyi kmr de hajiya maryam bata hayyacinta a yau. Ya bude baki zeyi mgna,ta katseshi "Dan ALLAH alhaji kar kace komi plx, kasan bazan kawo abinda ze cuci danku ba, a wannan fannin zamu hada sunnah ne kuma zamu samu lada insha Allah...plx kar kayi musu dan ALLAH..." Alhaji murtala yayi shiru kawai dukda bakinshi na cike da maganganu, Amma ya danne. "ALLAH ya sa muce kwara da Akayi..." Cewar alhaji murtala. "Ameen..." Amihh ta amsa da farin ciki a ranta. "Wannan kudi naki ki kwashe su, hajiya maryam, ai mune mukeda alhakin biyawa yaronnam sadaki bake ba ..." Cewar Alhaji murtala. Sosai hajiya maryam taji ddh, ta masa godia ta kwashe kudinta tasa a bag, alhaji Murtala ya mike ganin lokaci ya tafi yama hajiya maryam sallahma ya fice a gidan ya nufa masallaci, hajiya maryam ta dawo side din hajiya babba dan tace baxata tafi ba harse alhaji ya dawo taji meke tafita, nan ta zauna sunata hira da hajiya babba...
Chapter 69 · 0% Book details