← Book details Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 225

Sashe 130

Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

8:20am amihh ta nufa side din hannunta rike da tray wanda ke dauke da abinci da kuma magunguna ta turo kofar dakin hilwah ta shigo , dai-dai ta fito daga toilet daure da bathrobe dagani wanka tayi. Amihh ta shiga kare mata kallo tana fadin "Masha Allah kafa tayi sauki tinda gashi har knyi wankan, knyi sallah kou?'' Hilwah ta daga mata kai alamar eh tinda ta mata allurar ta bata maganin taji dadin kafar ta rage mata radadi , harma ta iya takata shine ta tashi tayi sallarh isha'i , harma tayi wankan ynzu,. Amihh ta karasa ta ajiye tray din hannunta a kn bedside ta juyo ta kalli hilwah tana fadin "alhmdllh raguwar Amihh me tsoron allura, taho kici abinci kisha mgni knji, seki tafi dakin Mijinki ..." Hilwah ta canza fuska ba tare datasan tayi hakan ba jin amihh tace taje dakin mijinta tasan dakin AB'ILAL Amihh ke nufi. Amihh ta fahimci canzawar fuskar hilwah a lokaci kn kani amma ta basar kmr bata fahimta ba. "Knji kou sweetheart?" Cewar Amihh. Hilwah tace to cikin sanyin muryarta seda ta bawa amihh tausai, ta bita da ido ta nufa drawer din kayan baccinta ta bude ta dauko wasu riga da wando masu laushi kalar mint green me digo digon white ba karamin amsarta riga da wandon sukayi ba, dukda ba matsatstsu bane amma sun matseta daf, ita jikinta ne hkn komi tasa seya bayyana zallar surar jikinta koda bataso, sumar nan tata ta zubo har kan gadon bayanta, ta karaso ta zauna gegen Amihh, amihh ta bude plate din dake kn tray din wanda ke dauke da kaza se tiriri takeyi dagani ynzu aka fiddota daga oven duk ganyayyaki sunbi sun baibaye jikin kazar rabinta ma duk ganye ne, hilwah ta kalli kazar dake plate da Amihh ke miko mata, kana ta dago ta kalli amihh, a dunia tanason dahuwar kazarnan irin ta larabawa ce Se tayi mamakin yadda Amihh tasan tanaso kuma ta yaya ta iya dafawa? Duk wanda ya iya dafa kazarnan to tabbas ya jibance larabawa ne, bawai haye ba. Amihh da knta ta shiga bata kazar a baki taci sosai a nan take amihh ta fahimci hilwah nason dahuwar kazar ko ba a fada mata ba, tanada ayar tambaya a kn yarinyar amma sam batason matsa mata ne sbda ta fuskanci inta tambayeta a kn wacece ita tana shiga wani hali. Magungunan amihh ta balla bata ta hadi da ruwa ta kora da mgnin, bata cika kin mgni ba tafi kiyayyar allura amma mgni in aka bata tanasha, sede in ita ce zatasha shi da knta bazata sha ba. "Feshe jikinki da perfume ki muje in rajaki dakin mijinki, nima zan kaiki da kaina sweet..." Cewar Amihh. Hilwah ta zubawa Amihh ido kana ta maida kwayar idonta kasa, harga Allah sam batasom zuwa dakin AB'ILAL amma bata iyawa amihh musu a kn hakan. Amihh ta kureta da ido tana karanto reaction dinta nan take ta fahimci bataso kawai de bata iya mata musu ne. "Nasan ina shiga rayuwarki Hilwah, kuma nasan ke me biyayya ce gareni , insha ALLAH kuma Allah baze barki hk ba, ki hkri da rayuwar Aurenki kowacce mace da irin qalubalenta a rayuwa, kowa kike gani a duniarnan akwai abinda ke damunsa, kuma akwai qalubalen dayake fuskanta Allah baya taba barin musulmi mumini hka nan Sakaka ba tare da jarabawa ba, kiyi hkri ALLAH subhanallahu yana tare da masu hakuri albarkacin biyayyar da kikemin insha Allah se Allah ya dubeki da idon rahama ya miki sakayya ta inda bakiyi zato ba...Allah ya miki albarka tashi kije ki fesa peefume dinki kizo muje .." Hilwah da jikinta yy sanyi sbda sansanyar kalaman amihh gareta ta mike a hnkli ta isa ga dressing mirror ta feshe jikinta da sansanyar perfume dinta, ta karasa ta dauki hijjabinta na sallah ta sakashi yakai mata rabin guiwa, , amihh ta tasata gaba suka fice a dakin, suka isa bakin kofar dakinsa, hilwah taja ta tsaya ta gaza bude handle din kofar dakin, amihh ta kula da tsoronshi hilwah keyi hkn ya bata tabbacin AB'ILAL na mata wani mugun abun ne. Karasawa amihh tayi hilwah ta matsa mata ta bude handle din dakin ita ta fara sako kai cikin dakin kana hilwah ta biyo bynta kwayar idonsa ya sauka a knshi yana kwance bisa bed dinsa har lokacin kwayar idonsa na kallon saman rufin dakin yayin da zuciarsa ke kan tunani tunani,. Kamshin perfume dinta ya cika dakin, already kamshinta me ddh ya riga ya gama shigar masa cikin kai shi ya bashi tabbacin ta shigo dakin, takun mutun biyu yakeji a dakin sbda dukkaninsu akwai takalma a kafafuwansu. Ba tare daya juyo ya kallesu ba amma ya fahimci su biyu ne suka shigo dakin Amihh da ita yarinyar. Amihh ta kamo hannun hilwah ta karasa da ita gefen AB'ILAL, tace ta kwanta da kmr zata mata musu se kuma ta kwanta ba tare data kalli inda yake ba, tayi facing hanyar shigowa, amihh taja duvet din bed din ta lullubeta, ta mata adduarh ta tofeta, AB'ILAL na kallo ko a hk yasan amihh nason yarinyarnan sosai, hakan ya bashi tabbacin inya rabu da itan tabbas zata tsine masa kmr yadda ta fadi, takaici da haushi ya cikawa AB'ILAL zucia hadi da kyamar yadda yarinyar tazo ta wani haye masa kn bed a matsayinsa name tsarki amma yau gashi karuwa ta kwanta masa a kan gadonsa, be taba jin abinda yayi hurting dinsa ba a rayuwarsa kmr abinda amihh ta masa na kawo yarinyar kan gadonsa,na bacci me tsarki me tsarkakewa. "Sweet dreams my love....." Amihh ta fadi hadi da bata deep kiss a kn goshinta hilwah tace "thank you amihh ..." Cikin sanyin muryarta tayi mgnr, AB'ILAL dake ji haushi ya kara rufesa se yakara tabbatarwa ransa hilwar ce takeso ta kwana dakinsa, sbda ya kusanceta, a thank you din datace wa Amihh ya fahimci hkn... Hajiya maryam ta sakar Mata murmushi kana ta juya ta bar dakin, ko kallon inda AB'ILAL yake batayi ba. Tana fita hilwah ta sauke ajiyar zucia ta gaza ko numfashin kirki se raba ido takeyi a dakin duk a tsorace take, sbda sunyi kusa kusa hatta da saukar numfashinsa tana iya juyowa shima yana jiyi nata kadan kadan. Juyowa yayi ya zubawa bayanta ido ya wani tasa ya cika fam dashi se yaji a ransa daman nononta ne yake kallo hk ba bom-bom ba, sosai ya kure duwawuknta da ido, kasancewar akwai yalwar haske a dakin, duk da hijjabin dake jikinta be hanasa ganin hips dinta ba me uban cika kmr ze fashe, daurewa yy ya hadiye wani irin yawu a hnkli rashin mutunci na cinsa inside."ke!!'' Ya fadi cikin tsawa. Seda jikin hilwah da gangar jikinta suka amsa, saura kiris ta fado kasan bed din sbda firgici da tsoro, ta riqe jikinta gam gam zuciarta kmr zata kama da wuta sbda tsantsar tsabaragen tsoronsa da takeji... "Ki saukarmin a kn bed dina tinda ba gadon gidan karuwai bane! nan ba a taba isknci ba a knsa,...." Yy mgnr muryarsa na sarkewa da jaraba, ga tsawa a cikin mngnr tasa. Hilwah jiki ya jara daukar rawa, ta sauka a kn bed din ta koma kasan tiles ta kwanta gudun karma ta kwanta masa a kn carpet ya mata cin mutumci. A wulaknce ya bita da ido ya juya fuskarsa daga kallonta sam be damu ba, data kwanta a kasan tiles din shi gaba daya haushi take basa, kuma kishi ne ke dawainia dashi ba tare daya sani ba.
Chapter 130 · 0% Book details