← Book details Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 225

Sashe 60

Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A baya a baya suka bi motar hilwah har suka isa gidan dandi. sukayi packing daga nesa ganin hilwah ta dakata a get din gidan dandin. Suka tsaya ta inda hajiya maryam zata iya hango hilwah, wadda ta tsaya a bakin get din, ta fito ta bude get din kana ta koma motar ta danna kan hancin motar cikin gidan, packing space ta nufa tayi packing kana ta fito ta dawo ta rufe gidan, duk hajiya maryam na hangota, ta gaban glashin motar har matsowa tayi danta ganta sosai. dan ustaz ma zuba mata ido yayi duk ya firgice domin yasan gidan nasu waye ba gidan Arziki bane, har kara lumshe idanuwansa yakeyi yana budesu a kan gidan, shi ga zatonsa ko de mafarkin daya saba ne yake yinsa ido biyu. Nan ya fahimci gaskia ne ba mafarki yakeyi ba reality. "Subhanallah!...Subhanallahi!!..." Shine abinda ya rinka fitowa daga bakin Dan ustaz, tini ya fara zufa sbda tsabar tsoron ALLAH. Hajiya maryam ta dawo da kwayar idonta kan dan Ustaz byn taga hilwah ta dawo ta rufe get din ya zaman bata hangota. "Se faman subhanallahi kakeyi kmr kaga mugun abu..." Hajiya maryam ta fadi a hasale. Dan ustaz ya goge zufar daketa karyo masa daga goshinsa da hannunshi ya goge a jikin baqar jallabiyar dake jikinsa duk yabi ya hade shida jallabiyar, ko za a kasheka baka iya tantance shida jallabiyar wayafi wani baki. "Wato ainifin...subhanallah! Hajiya dole ince subhanallah! Sbda wannan bad'alah da ake aikatawa tayi yawa a doron duniya! Ya subhanallah! Ya khafih! Wayyo adduniya mad'unun! Duniyarnan tsinanniyace, wa'iyazubillahi! Wa'iyazubillahi, ashe de kaga mutum, wayyo! Wayyo, amman de ALLAH wadaran naka ya lalac...." Hajiya maryam ta katseshi cikin tsawa sbda ta gaji da surutan da yake mata marasa kai da gindi. "Da Allah rufemin baki! Shashasha kawai..." Ta karasa mgnr a hasale. Dan uataz ya juyo ya kalli hajiya ya hada hannayensa duka biyu alamar hkri kana tace "latagadab! Wato ainifin hajiya kada kiyi fushi .. Ammm .wato de hajiya ina nufin kada kiyi fushi...affuwan lakhi ya jama'atul madinatul munawwaratul,..." Hajiya maryam se yatsina fuska takeyi sbda Ya dameta da tofe tofen yawu, shi haka yake inde yana mgna kana kusa dashi seya jikaka da yawun bakinsa sharkaf,. "Dan ustaz ka kalli gidan da kyau, inaso ka kawoni zuwa gobe ina da bukatar ganin iyayen yarinyar nan..." Cewar hajiya maryam Dan ustaz ya zabura ya zaro ido fuajarsa dauke da dmwa yace "Fasbir thabran jameelah!! Qala a'uzu billahi an akuna minal fatseequn! '' Ya fadi hhkn da karfi, seda ya firgita hajiya maryan ta kara daka masa tsawa "wai kai meyasa baka da natsuwa ne!'' Dan ustaz yy firgigit ya kara hada hannayensa duka biyun yace "Latagadab! Wato ainifin hajiya dole ne bazan sanu natsuwa ba a halin ynzu ni majnunun ne in har naga inda ake Aikata Zunubi,..." Hajiya maryam tace "Zunubin me?'' Dan uataz ya kara zabura ya zubawa kofar get din da hilwah ta shiga ido yace "wato aibifin Hajiya gidan karuwaih ne nan!" Hajiya maryam ta zaro ido sbda girman kalmar karuwai da Dan ustaz ya fadi, wai gidan karuwa. "Wani irin gidan karuwai kuma? Kai banason hauka..." hajiya maryam Ta karashe mgnr tana tsare gida ta fara tunanin dan ustaz ya fara rainata ne. Dan ustaz yaci gaba da mgna a gigice sbda beyi tsammanin gidan karuwai hilwah take ba. "Wato ainifin Wallahi hajiya ina nufin nan din gidan karuwai ne ..." Dan Ustaz yayi mgnr yana nuna gidan da hilwah ta shiga da yatsa. Hajiya maryam tabi yatsar nashi da kallo, nan ta shiga karewa gidan kallo a karo na uku, dukda bata taba ganin gidan karuwai ba amma de tasan nan beyi kama da gidan masu mutumci, sannan maza se fitowa sukeyi wasu kuma suna shiga. "Gidan karuwai kuma?'' Hajiya maryam ta kara maimaitawa muryarta cike da kid'imewa, still kwayar idonta na kn gidan. Dan ustaz ma idonshi na km gidan yace "Wallahi Mutanen makka nan gidan karuwai ne,..wato ainifin wannan gidan karuwan ya shahara sosai a garin kaduna..duk wacce kk gani a nan to tabbas karuw...." Hajiya maryam dake sauraronsa ta dakatar dashi cike da jin zafin jam'in da yayi. "Rufemin baki ban tambayekaba!'' Dan ustaz yaja bakinshi yayi shiru. Hajiya maryam ta kara zubawa gidan ido, tabbas gidan karuwai ne sbda mazan dake ziryar shiga gidan sunyi yawa, aiko kasuwa se haka. Doubles mamaki ne suka cika zuciyar Hajiya maryam, tana me kara tunano yanayin jikin hilwah data gama karanta a kwanaki biyun da tayi a gidanta, a yadda hasashenta ya bata hilwah virgin ce, babu wata alama data nuna a tattare da ita ta taba sanin namiji, dukda kuwa bataga farjinta ba, amma ta karanci hkn, kasancewar ita likita ce likitanma ta Mata, sannan tanada wata iriyar baiwah, da Allah ya mata, wadda ba kowa keda ita ba, a gaskia taga wasu qualities a tattare da hilwah wadda ke nuni da cewar gaban namiji be taba ratsa gabantaba. Sam Hajiya maryam ta kasa amincewa da gidan na karuwai ne dukda kuwa abinda idanuwanta suka ganar mata, na ziryar shiga gidan da maza suke tayi ko wannan ya isa yasa ta amince amma taki amincewa, ta umarci dan Ustaz daya tada motar su karasa wani shago da take hangowa kusa da gidan karuwan, wanda ya tara cincirundon mutane, maza da mata, amma matan su siyan abu ke kawosu dasun siya suke barin gurin. Zaro ido dan ustaz yayi ganin hajiya na neman jafasa a halaka ya aikata bad'alah yace "Wato ainifin Nace Hajiya me zamuyi a gun shi wancan la'anannan me kwantenar saida kayan maye...." Hajiya maryam tayi jim kana tace "mu karasa de nace..." Dan ustaz be kara musu ba, ya kunna motar ya karasa da ita gun kwantenar din yayi packing ,a saitin kwanternar wadda ta tara maza a kofa, sun ajiye bancina biyu ne, duk cike suke da maza wadanda daka gansu kasan yan shaye shaye ne, duk babu ma me sitirar arziki a jikinsa, zallarh whlr dasuka sa kansu a ciki ta bayyana a tattare dasu. Daga cikinsu wasu na busa sigari wasu kuma na busar wi-wi, ganin tsayuwar motar hajiya maryam a gun yasasu fara watsewa a guje su ga tunaninsu ko jami'an tsaro ne, domin kame akeyi na yan shaye shaye a garin ba arziki. Wani dattijone ya fito daga kwantenar wanda A kalla ze kai 70yrs ya falfala a guje, ya bar kwantener din a bude, shi a zatonsa kame akazo yi, daman ansha kawo masa hari za a kamasa, se kuma barsa sbda yana basu cin hanci ne, agreement maya sukeyi dashi da jami'an tsaro duk karshen wata yake biyansu makudan kudi, shiyasa suke barinsa yana tsula tsiyarsa, abinda yasa ma ynzu ya gudu sbda be gane wadanne jami'an tsaron bane a motar sbda shi be saba ganinsu a irin mota me kyau ba kmr wannan, dan hk yy tunanin governor ne da knshi yazo kamashi, shiyasa ya gudu. Hajiya maryam da batasan dalilin guduwar da sukayiba ta tambayi dan Ustaz Meye dalilin dayasa suke guduwa, nan dan ustaz ya shaida mata sbda sunsha jami'an tsaro ne, Hajiya maryam tayi shiru tayi jim tana me kara bin gidan da hilwah ta shiga da kallo, har zuwa ynzu wani bangare na zuciarta be amince da cewar gidan, Gidan karuwai bane. "Muje gaba..." Hajiya maryam ta umurci dan ustaz, daya tada motar suyi gaba, ya tada suka kara gaba, suna cikin tafiya slow suka ga wani Matashi baki dan siriri, ze wuce ta kofar gidan dandi, hajiya maryam tace Dan Ustaz ya dakata,..dan ustaz yaci burki a gaf da matashin hkn yasa dole yaja ya tsaya ya zubawa dankareriyar motar ido, jikinsa ya fara rawa , ya riga ya gamasa ran yan yankan Kai ne ko kidnappers, dan ynzu ma babu yan yankan kai sede kidnappers din. Hajiya maryam ta sauke glashin sidi dinta, ta zubawa guy din ido, shima itan ya zubawa ido, yana me samun natsuwa ga zuciarsa sbda bega kalar mugaye ba a tattare da matar dukda kuwa mugu beda kammanin ni. Sallahma hajiya Maryam ta masa irin ta addinin musulunci, sbda ta gnshi da tabon sallah. matashin ya amsa yana me jin natsuwa a ransa. Hajiya maryam ta fara mgna cikin tsantsar ilmi da baseera "Ammm..dan Allah in bazaka damu ba zan tambayeka..." Matashin yace to ina sauraronki mama..." Sbda ta haifesa. hajiya maryam ta sauke numfashin kana ta jegowa matashin Tambaya game da gidan da hilwah ta shiga, ba bata lokaci matashin ya bata amsa da cewa gidan karuwai ne. A wannan karon seda hantar cikin hajiya maryam ta kada, kawai tama matashin godia ta umurci dan ustaz dayaja motar ,yaja suka bar gurin, direct hanya gida suka hau, hajiya maryam se juyawa takeyi tana kallon gidan zuciarta na mata k'una, dukda taji gidan na karuwai ne amma kuma soyayyar hilwah a zuciarta bata sake daurin zani ba yada yake a haggun nan hakan yake har zuwa ynzu. har suka isa gida hajiya maryam na tambayar knta shin me Hilwah keyi a gidan karuwai? Tambayar da bata da amsarta kuma bata dame amsa mata ita. Dan ustaz fa jiki yayi sanyi.
Chapter 60 · 0% Book details