Sashe 106
Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ina zatasa rayuwarta taji dadih, ta fara tunanin ta gudu ta bar gidan, se dayar zuciarta ta kwabeta kan karta kuskura kodan darajar hajiya maryam,...kukan tasha har kusan 8:am kana ta iya mikewa ta nufa bathroom tayi wanka da ruwa me zafi kmr me jego da towel ta gargasa jikinta tana wankan tana kukan takaicin abinda ya mata marin da yayi mata yafi komi tsaya mata a rai, ya bar tarihi a rayuwarta, shine mutum na farko daya fara wulakntata a dunia kuma shine mutum na farko daya fara kai hannunsa kn kuncinta da sunan mari. Wasu hawaye masu zafi suka shiga aikin bin kuncinta, tayi shashsheka a yadda take kukan kawai ya isa a tausaya mata ita din abar tausai ce tamkar marainia ce sbda bata da uwa bata da uban dazata gaya musu dmwarta,,, da kyar ta iya bambare dankunnen daya fasa ya shiga bayan kunnenta ta bambareshi tana kuka, ta cireshi ma baki daya, nan take jini ya balle, da kyar ta samu ya tsaya, gasa gurin ita ga zatonta ma kunnenta ze yage se ko akaci sa'arh be yagenba, ta dauro alwala ta fito domin gabar da asubahi, har lokacin bata bar kukanta ba, ta fito ta shirya cikin riga da wando amma ba matsatstsuba irin na indians dinnan free basu kwancia a jiki sosai kalarsu kalar green ne ce sun matukar amsarta, hijjabi ta zumbula ta nufa inda aka tanada dan sallah ta tayar da asubahin da kyar take sallarh har ta idar se aikin shashshek'ar kuka takeyi Hadi da ajiyar zucia. Har ta idar da sallarh ta mike ta cire hijjabinta duk a tsorace take gani takeyi kmr ze banko kofar dakin ya shigo da zullumin a zuciarta har ta idar da sallarh. Maida hijjabin data cire tayi ma'ajinsa a daddafe ta karsso bakin mirror ta zubawa fuskarta ido, gani takeyi kmr ba ita bace, duk tabi ta canza fuska ta kumbure again ga kuraje jajaye a fuskar tata, kara matsawa tayi gaban mirror ta zubawa fuskarta ta ido sosai zuwa wuyanta ,da hannayenta ma inda duk jajayen kurajen suke, seda ta dan tsorata sbda bata saba ganin hkn a jikinta ba, ta fashe da wani sabon kukan ita batasan meyasa abun ya fito mata ba, batasan cewa sauro suka cijeta ba, sbda be saba cizon taba balle ta bambamce yadda reaction dinsa yake a jikin mutum. Ta kurewa gefen fuskata ido inda ya mareta shadin Hannunsa radau ta zubawa ido, ta kara fashewa da kuka, ba zafin marin bane yafi addabarta a ynzu zafinshine ke cinta inside, Ta kusa 30mnt a tsaye gaban mirror din tana kukan kana ta fara jiyo ana knocking din kofar dakin jikinta ya hau kakkarwa, ta karasa can lungun dakin ta rakub'e tana hawaye jikinta na rawa, tasan shine, wannan karon kuma sede ya kasheta, ya riga ya firgitata ya dandana mata izayarsa.... Ci gaba akayi da buga kofar, hilwah tayi shiru jikinta nata kara daukar kakkarwa, .."hilwah kina bacci ne!'' Cewar salwah dake daga waje tana knocking din kofar dakin hannunta riqe da trea me dauke da breakfast din hilwah. Jin shirun yasa salwah zatonta ko bacci hilwah takeyi. Ajiyar zucia hilwah ta sauke jin Muryar salwah, ta sauke numfashi me dauke da whla da gajiyawa, ta goge kwallarta ss, ta fara qoqarin saita knta, dan kada Salwah ta fahimci, halin da take ciki, ta isa ga madubin ta kara gyagyara fuskarta duk dan kada salwah ta fahimta ne, Amma tasan da wuya in bata fahimta ba kodan kurajen jikinta tasan su zasu tona mata asiri, da hnzari ta dauko hijjabin data cire ta saka tana jiyo salwah nata kwalo mata kira, karasawa tayi ta bude kofar bayan ta saka hijjabim se faman rurrufe gefen kuncinta daya kumbura takeyi. Tinda ta bude mata kofar ta zuba mata ido, hilwah tayi kasa da knta, a kallo daya salwah ta fahimci abubuwa da dama na matsala suna tattare da ita, kama daga kn kurajen daje fuskarta har zuwa dan kumburar da fuskar tata tayi, zuwa saman kwayar idonta ."meya sameki?'' Itace tambayar data fito daga bakin salwah, hilwah ta koma ciki ba tare data ce komi ba , Salwah ta sako kai cikin dakin kwayar idonta na kn Hilwah wadda ta zauna a kasan dakin, se faman rurrufe gefen fuskarta takeyi, Salwah ta karasa ta ajiye trea din dake hannunta a kasn carpet din, still kwayar idonta da hnklinta suna kan hilwah, wadda knta ke kasa kmr munafuka, salwah ta karaso inda take ta zauna tana facing dinta ta kure fuskarta da ido dukda se faman rufe fuskar hilwah keyi amma hkn be hana Salwah fahimtar kuraje yan ficil ficil jajayen dasuka fito mata a kn fuskar tataba. "Dea meye wannan a fuskarki?'' Salwah ta tambaya fuska dauke da mamaki sbda ita de tasan lafia lau suka rabu jiya fuskarta smul dukda ba mai take shafawa ba, tinda tazo gidanma se versilin take shadawa. Salwah ta kara kureta da kallon kurillah, kurajen nata bata mamaki. Hilwah ta kara rufe gefen fuskar tata ba tare data bawa salwah amsa ba, salwah se aikin binta takeyi da ido gefen fuskar tata datake boye mata ita takeso ta gani, dan hk takai hannu ta juyo da fuskar tata ba tare da hilwah ta ankare ba, Dan hk ta saki hannunta da hijabin dataketa rufe gun dashi, nan Salwah taga shadin hannu seda ta firgita ta zaro kwayar ido waje, tausan hilwah ya rufeta dagani ko ba a gaya mata ba tasan shadin hannu ne. "Meya sameki dea? Meye wannan? Waya mareki?'' Salwah ta jero mata tambayoyin duk a gigice take, ta zubawa shadin yatsun dake kwance kn fuskar hilwah ido, Salwah tayi saurin maida hijjabinta a gurin ta lullube, tayi kasa da knta hadi da cema Salwah "ba komi..." Salwah ta kara zubawa fuskar tata ido, ko ba a gaya mata ba tasan be wuce yah AB'ILAL ne ya daketa ba sbda mugune azzalumi ne ba imani bane a ransa, nan da nan zuciarta ta hasala, tausan hilwah ya kara lullubeta,taji kmr ta mata kuka, duk tabi ta gigice, dagani ba karamin wuya taci ba daga jiya zuwa yau. "Yazakice ba komi plx,,bayan ga shaidar hannu nan a kn kuncinki again ga wasu kuraje, plx ki gayamin gaskia bnaso kice min ba komi Dan Allah... Ki bar zurfin ciki kawai ni ki gayamin gaskia, yah AB'ILAL ne ya dakeki kou?'' Salwah ta karashe mgnr a hasale, bata tabajin haushin yayan nata kuma jinintaba se yau, sbda tasan wannan Aikin nasa ne. Hilwah tayi kasa da knta hadi da fashewa da kukan da batasan dalilin sa ba, daman kmr tana jira. Salwah ta matsa jikinta ta jawota t rungumota jikinta itama ta fashe da kukan tana fadin "Amma bross be kyautaba, Wlhy ni shiyasa banso kk dawo side dinnan ba sbda nasan cutarki zetayi Allah kadai yasanma me yake miki, wlhy sena gayawa Amihh inta dawo Daga Aiki (kasancewar yau 7:am ma bata cika ba ta fice a gidan, sbda aikin gaggawa daya sameta, shiyasa batazo taga hilwah ba sbda yayi sassafe dayawa ita ga zatonta ma basu tashi ba)" salwah ta kara rungumo hilwah jikinta, salwah taji jikin hilwah nata kakkarwa Ga uban zafi daya dauka , se faman kuka sukeyi kmr wadanda iyayensu suka mutu, zuciar salwah cike da tausan hilwah...seda suka kwashi 15mnt a hk suna kukan kana salwah ta dago fuskarta daga jikinta ta tallabota da dukkanin hannayenta biyu ta zuba mata ido har lokacin se kuka takeyi tausanta suka kara cika Salwah, cikin muryar kuka Salwah tace "dea AB'ILAL ne ya dakeki kou? Ki gayamin Nasanma shine ko baki fad'iba..." Hilwah ta girgiza mata kai alamar ah'a salwah tace "plx ki gayamin, wlhy sena gayawa Amihh koda hkm zesa ya kasheni, ai ba kawoki akayi ba yayita cutarki ba, ni nasan yana cutarki kawai kinki fad'i ne...." Cikin muryar me cike da gajiyawa da kuka Hilwah tace "ni...be...min...ko...mi...ba..." Ta fadi muryarta na sarqewa sbda kukan dake cinta har lokacin, kmr numfashinta ze dauke. Salwah ta hade rai takaici ya rufeta ga abu tana gani ganin idonta amma kuma hilwah na karyatata. "Why zaki cemin ah'a, bayan ga shadin yatsu nan a kn fuskarki, Wlhy dukanki yayi, su wad'annan kurajen ina kk samosu Plx?'' Salwah ta karashe mgnr hadi da kara dago face din hilwah ta zubawa kurajen ido ss, nan take ta fahimci na cizon sauro ne abunka da farar fata irin ta jarirai. fuska dauke da mamaki salwah tace "kmr cizon sauro? Ta yaya sauro ya shigo ya cijeki?' Ina aka samu sauro har haka?' Salwah ta karashe mgnr tana karewa dakin kallo, sam babu wata kafa da sauro ze shigo to ta ina ya shigo ya mata wannan cizon, Hilwah tayi shiru hadi da kara kasa da knta, hilwah ta bita da ido ganin bata da niyar bata amsa yasata ci gaba da mgna itana hawaye . "Ki gayamin meye ya hadaki da AB'ILAL ya miki duka, kuma ya akayi sauro ya cijeki plx ki gayin plx? " hilwah ta goge hawayen dake zubo mata itana, ta sassauta kukanta ganin Salwah duk tabi ta damu har lokacin se kuka takeyi tace "ni be min komi ba,..." Ta fadi da muryarta ta kuka, hadi da karyayyen harshenta. Salwah taji takaicinta ya rufeta zurfin cikinta haushi yake bata "to wannan kurajen sauron ina kk samesu? Tinda kinki gayamin meya hadaki da yah AB'ILAL ya dakeki dan wlhy nasan dukanki yayi ga mari nanma a kn fuskarki, inna gayawa amihh ita tazo ta tambayeki zaki gaya mata gaskia Tinda ni baxaki gayamimba..." Hilwah ta tsagaita da kukanta jin Salwah tace zata gayawa Amihh kuma dagani da gaske take bada wasa take ba, ta kara goge hawayenta dake kn fuskarta kwayar idonta na kn salwah ta fara mgna ''plx karki gayawa Amihh, ni be min komi ba.." Salwah ta hade rai tace "in kina cewa be miki komi ba bnjin ddh, infect ma haushi kk bani sbda ga abu ina gani a zahiri... Kawai ki gayamin gaskia tinda bakiso in gayawa Amihh dan Allah ki gayamin?'' Salwah ta karashe mgnr da sigar roko, hilwah ta tsaya a kn bakarta kan be mata komi ba, salwah tayi juyin dunia Amma hilwah tace mata ba komi, aiko tace seta gayawa Amihh nan