← Book details Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 179 OF 225

Sashe 179

Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda ya bar gidan be nufa ko ina ba se babban club din garin, sbda dazu ance masa se zuwa dare suke taruwa su yan shagakin duniar, a zuciarsa yakejin tana kusantosa sede matsalar besan a ina take ba, kawai de a jikinsa yakejin tana kusa dashi, Sbda zuciarsa dake tsananta bugu. Bayan ya isa clube din yaga yammata iri daban daban, lungo da sako seda ya duba be gnta ba, ya fice a Club din zuwa ga hotel din dasuka fara haduwa shida ita, nanma zagayensa ya shigayi tako ina lungu da sako, amma sam be gnta ba, yafi karfin 2h a hotel din sbda a nan yakesa ran ze gnta amma be gnta ba, ya juya ya fice a hotel din, ya nufa zuwa wani club din nanma be sameta ba, dukda dare ya tsala amma sam shi ba hkn bane ke damunsa, babbar damuwarsa ya samu ya gnta ko a ina ne, ko a wani hali ne, shide yanasonta ko yaya ta zama, ko ita ce uwar kaf karuwan dunia shide yana santa a haka, ALLAH ne ya jarabcesa,,,rnr be dawo gida ba se 4:44am, amihh tayi tsumayensa hatta gaji tayi dubansa a side dinsa, har 12;am tana ziryar side dinsa, amma babushi babu dalilinsa gashi ta kira wayarsa yaki dagawa, abnda yafi ma Amihh ciwo kenan a gami da AB'ILAL in ta kirashi be daga ba, rnr zuciarta ji takeyi tafi ta uban kowa cunkushewa a dunia. Dole ta koma side dinta tana me tunani da tsammanin ko ya tafi garin kano ne, sbda in ze tafi baya sallama wasu lokutan shiyasa ta barshi a yana garin kanon, koda ta isa side dinta ta kwanta , gaza bacci tayi, ita ce har wuraren asubahin bata rintsaba, tana jikin window tana wasu tunani tunani, a hk har taga shigowar motarsa cikin gidan, da mamaki tabi motar tasa da ido, tin tini takeji a jinin jikinta ba lafia ba, shiyasa ta gaza rintsawa,. "Daga ina yake a wannan tsohon daren?'' Take tambayar knta da knta, hadi da dumbin mamaki a tattare da zuciarta da fuskarta. Tana nan tsaye jikin window din tana tunani har taga fitowarsa daga motar ya nufa side dinsa duk tana tsaye bakin window din, ba jimawa taga fitowarsa daga side din nasa daure da Alwala sbda yalwar hasken dake compound din gidan kmr rana, dan hk ta hango ruwan Alwala a kn fuskarsa, Tana kallonsa ya fice a gidan zuwa masallaci, dai-dai ana kokarin tayar da sallarh asubahin, jiki ba laka Amihh ta juya ta nufa toilet ta dauro alwala itama, ta fito ba jimawa, ta saka hijjabi ta nufa kn dadduma ta tayar da sallar asubahain, sam ko natsuwa bata dashi, sbda tunanin daga ina AB'ILAL yake a wannan lokacin, dan sam bata da full kwanciar hnkli hk ta idar da sallar, ko adduarh batayi ba ta tashi ta fice a dakin, ta fito falo, ta fice a side din gabaki daya, sanye da hijjabin data idar da sallar asubahin dashi, ta nufa side dinsa, ta isa har bedroom dinsa bata gnshi ba, hkn ya bata tabbacin be dawo daga masallacin ba, ta dawo falon ta shiga zirya a tsakar falon idanuwanta se lumshewa sukeyi jikinta duk tako ina a mace yake, burinta ya dawo daga masallacin taji daga ina yake, abnda yasa abin ya dameta, sam be taba fita ba ya shigo gida a wannan lokacin, ita kawai a yanayin jikinta takeji wani abu na damunsa,,duba da la'akari datayi da irin gagarumar ramar da yayi, itama ta kara firgitata, hnklinta sam be kwanta ba tako ina, zuciarta na rawa. "Allah ka jarabcemu da abnda zamu iya...." Abinda ya fito daga bakinta kenan, se kara zirya takeyi a falon, zuciarta sam ba natsuwa, da tayi wannan tunanin ta dawo tayi wancan tunanin, gabaki daya knta ya kwance, babbar adduarhta Allah yasa ba mummunar harka ab'ilal ya jefa knsa a ciki ba... Ta sauke ajiyar zucia me cike da zallar tashin hnklin da take ciki, ita de kawai hnklinta be kwanta ba, taji a jikinta yana cikin wani hali ne, sam ma bataga alamar natsuwa ba a tattare dashi... Tana nan tana zirya a falon ya shigo wuraren 7:am kasancewar ya tsaya yayi askar din safe hadi da zikiri da salatuttuka ga ma'aiki S.A.W. yana shigowa idanuwansa suka sauka a kn Amihh se zirya takeyi a falon tana ganinshi ta kureshi da ido nan take ta hango Ainihin matukar ramar da yayi se taji zuciarta ta amsa da tausayin d'anta, Ainihi Amihh tana jarabar son AB'ILAL kmr k'ashi da tsoka daya a miya. "Hubbul ruhh!" Amihh ta kirashi da sunan datake kiranshi dashi da yana karamin yaro, karasowa yayi ya fada jikinta daman kmr yana jira ya sakar mata nauyinsa ya fashe da kuka, amihh ta rungumeshi a jikinta sosai nan ta kara tabbatar da ramar da yayi ta shahara, duk jikinsa yabi ya canza. "Hubbul ruhh, meye na kuka? Waya tabamin kai? Ciwo kayi ne kayi wannan ramar?'' Amihh ta jero masa wadannan tambayoyin duk ta shiga d'imauta da dmwa, AB'ILAL be tankataba yaci gaba da kukansa yayin da hawayensa keta sauka a kafadarta inda yasa knsa, sam ko nauyinsa Amihh bataji hnklinta kaf ya riga ya gama tashi kawai de tana danne zuciarta ne, amma ji takeyi kmr ta fashe da matsanancin kuka. "Tell me plz, meya sameka Abii na? Daga ina ka dawo da Asubah?'' Amihh ta kara tambayarsa muryarta na kokarin bayyana tashin hnklinta amma tanata daurewa hadi da kokarin control. Cikin kuka ya fara mgna "Amihh san yarinyarnan wlhy kasheni zeyi!, na rasa sukuni a rayuwata, amihh pls kimin adduarh , Amma ba adduarh dazan rabu da santa ba,,amihh ina santa wlhy, ko a ina take ina santa, koda bata da kowa a dunia Amihh ina santa, Allah ne ya jarabceni, a knta ban iya bacci ban iya sukuni rayuwata ba dadih, pls amihh me nayi ALLAH ya jarabceni da Tsananin santa har haka!? Pls ki tayani neman gafara ga ubangijina, ya yafemin abnda nayi ya jarabceni da soyayyar yarinyarnan me kashe zucia da gangar jiki!'' Ya karashe yana me kara fashewa da kuka daman ya jima yana neman inda ze samu ya kwanta yayi kuka, ko ze samu sassauci a zuciarsa. Tabbas kukansa na tabata, bata taba ganin kukansa ba se a yn kwanakinnan kuma duk a kn yarinyar, Abin ya daurewa Amihh kai, bata taba ganin so irin wannan ba Ace mutum marabarshi d mahaukaci shine sitirar dake jikinsa,. "Pls kayi shiru ny boy..Kana cin abnci ma kuwa babana?" Amihh ta tambaya tana kara rungumosa jikinta, duk taji ma nauyin nasa babu wani na kirki ynzu. Kwace jikinsa yayi daga jikinta, fuskarsa shabe shabe da ruwan hawaye, ya tsugunna a kasan guiwowinsa idaniarsa na zubda kwallah, , ya dago ya zuba mata sexy yum-yums idaniarsa, wadanda suka koma kalar jajjawur sbda kuka a yn mintunan kukan da yayi yafi karfin a kirgashi a mintoci ko awanni, sbda da zuciarsa yake kukan, zucia kuwa tafi Second ko mintoci da awanni gudu, ko bature be isa ya kiyasta gudun zucia ba. Cikin hawayen ya fara mgna idaniarsa na kn Amihh itama idanuwanta na kn dannata da duk take ma masa kallon full mahaukaci. "Amihh bana ta Abinci a halin da nake ciki ynzu,, pls ki gayamin ina yarinyarnan take, dan Allah Amihh ki gayamin! Ki dawomin da ita tinda akwai Aure na a knta, Auren sunnah kikasa aka mana da ita, Amihh Wlhy yarinyar ba irin sauran mata bace Allah subhanahu shiya jarabceni da soyayyarta hadi da tsananin sha'awarta dan Allah Amihh ki temakeni!'' Ya karashe zuciarsa na beating da karfi ji yakeyi kmr zata fito daga kirjinsa ta fito fili, ya fashe da kuka me tsananta zuciarta me sauraro a zurfin tausansa. Lumshe ido Amihh tayi klmnsa na dukanta, ji takeyi kmr ta maidashi ciki, a lokaci knkani kamanninta suka sauya zuwa zallar damuwarta data fi ta da. "Tashi muje kayi wanka heart beat, kaci abnci, se in gaya maka inda take..." Amihh ta fadi da karyayyiyar zuciarta, dukda batajin zata iya gaya masa inda take, sbda zalincin da yayima yarinyar kmr sabo take jinsa a cikin zuciarta, amma tana tsananin tausansa, a jini da tsokarta tasan ya azabtu. Farin ciki ya rufe AB'ILAL jin tace zata gaya masa inda hilwah take, nan take farin ciki me bayyanar da annuri hadi da annashuwa me tsananin haske ya bayyana a kn kyakyawar fuskarsa, kmr bashi ke kuka ba, duk yabi ya shige halarar farin ciki. Amihh ta zuba masa ido, hadi da lumsar kyawawan idaniarta a knsa, ta kara budesu a kn nasa. AB'ILAL ya kamo hannayenta ya rike cikin nasa, still yana tsugunne bisa guiwowinsa ya fara mgna cikin zallar farin ciki "Auwal hubb da gaske xaki gayamin inda take?'' Amihh ta daga masa kai alamar Eh, kana ta fara mgna "Amma seka gayamin daga ina kake tin safe, ka dawo gidannan da asubahi?'' AB'ILAL ya lumshe idanunsa, komi Amihh tace masa ze iya yi sbda kawai tace zata gaya masa inda hilwah dinsa take. "Naje neman hilwah ne..." Ya bata amsa nan take. Amihh ta tsiresa da ido tace "Ina kaje nemanta?'' Ab'ilal ya bata amsa "Duk inda nasan akwai jama'arh a garin nan Amihh, inna ci gaba da zama ba tare da ita ba zan iya mutuwa Amihh...taba kiji zuciata kullum cewa takeyi zata fashe wlhy Amihh ni inaji a jikina inada ciwon zucia, mutuwa zanyi Amihh..." Ya karashe yana me dafe kirjinsa dake masa barazanar tarwatsewa. Amihh ta zuba masa ido tana sauraron kalamansa, wad'anda take jinsu har a kasan zuciarta. "Babana ka sassautawa knka pl..." AB'ILAL yayi hanzari katseta ta hanyar cewa "Amihh ai bani na daura wa kaina ba, balle in sassautawa kaina,,ki temakeni ki roki ALLAH subhanahu ya sassautamin plz!" Amihh ta sauke ajiar zucia sam zuciar tata bata cikin ddh tace "ALLAH ya sassauta maka hubbul ruhh..." AB'ILAL ya amsa da Ameen, still hannayensa na cikin nata. "Hubb ki gayamin inda take plz?'' Amihh tace "Seka tashi munje kayi wanka, kaci abnci sosai, ka saki sannan zan gaya maka..."" Jiki a sanyaye ya mike tsaye yana tangal tangal kmr ze fadi kasa,.. matsowa Amihh tayi ta rungumo abinta jikinta, a hk suka karasa har bakin toilet din bedroom dinsa, ya shige
Chapter 179 · 0% Book details