← Book details Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 225

Sashe 67

Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba tare dana gama fayya ce muku girmansa ba, yafi dayan dakin girma sosai, tako ina dakin se shining yakeyi hatta da fentin dakin ma kyalkyali yakeyi irin kyalkyalinnan na gayu. "Nan naki ne...kama daga falon nan har zuwa dakunan nan duk naki ne, ki zauna kiyi abnda kkeso, dan Allah inaso ki cire wannan gidan karuwan a zuciarki plx..." Cewar Hajiya maryam dake mgnr cikin natsuwa kwayar idonta na kan hilwah wadda tinda ta fara mgnr tayi kasa da knta, tana tunanin meyasa duk hajiya maryam ke mata wadannan manyan karamcin har haka?" Jawota hajiya maryam tayi suka fice a falon suka dawo nan nata falon suka zauna a kn 3ct hajiya maryam se karawa hilwah natsiha takeyi, har zuwa lokacin sallar azahar hajiya maryam ta jawo hannun hilwah zuwa dakinta sukayi sallarh, suna idarwa hajiya maryam ta bata gado tace ta kwanta ta huta kafin ta hado mata binci, hilwah tabi umarnin Amihh wadda ta fice a dakin, ta nufa kicking. Amihh na fita a dakin hilwah ta tashi zaune zuciarta fal kewar su kankana dasu Amal, gaskia batajin zata iya zama a gidannan, sbda shaye shayen da takeyi, amm harga ALLAH tanason amihh da Salwah, jure rashin shaye shaye da rashin su kankana ne bazata iya ba gskya. Ba jimawa hajiya maryam da Salwah suka shigo dakin hannayensu riqe da manya manyan trea , salwah ta ajiye trea din dake hannunta a kasa, ta jawo canter table dake dakin gaban hilwah suka ajiye trea din a kai, hajiya maryam ta fice salwah ta koma gefen hilwah ta zauna se faman aika mata da fara'arh da murmushi takeyi. "You are beautiful..." Cewar hilwah da kwayar idonta ke kan salwah. "You are beautiful more than me sweetheart.." Cewar salwah. Hilwah tayi murmushi yynda dimple dinta na kasan gemu ya lotsa yan mitsil mitsil din haqoranta suka bayyana. Salwah ta bude baki zata kara mgna amihh ta shigo dakin, da wani trea din a hannunta ta ajiyeshi a bedside, ta dawo dayan gefen hilwah ta hannun dmnta ta zauna ya zamana Salwah na hannun hagu. Bubbude ma hilwah warmers din dake kn trea din hajiya maryan ta shigayi tana me tambayarta wanne takeso ta ci, abinci ne na alfarma se tiriri kawai yakeyi, hilwah tayi shiru kawai yynda kamshin abincin ke ratsata... Hajiya maryam data gaji da tambayrta dan knta Ta zuba mata abnda takeso ta shiga feeding dinta a baki, tana amsa tana ci tana lumshe ido,,salwah kam ta zuba musu ido farin ciki kmr zuciarta zata fito fili ko yunwah ma bataji sbda jin ddhn ganin hilwah yau a gidansu, duk ta kagu su kebance ta tambayi hilwah din ko ta dawo gidansu ne kou! Dan bataso ta tafi. Seda amihh ta tabbatr ta koshi kana ta batta haka, salwah ta kwashi kayayyakin ta nufa kiching dasu ta dawo ta kwashi sauran.... Rnr hk Amihh ta wuni tana tarairayar hilwah har dare ya tsala, after sunci abincin dare, sun dan taba hirah, yau salwah ce ke hira da Amihh cikin mutumci da mutumtawa, ba krmin ddh hkn ya ma salwah ba tasan duk dan sbda hilwah ne, dan hk ta kara kaunar hilwah a ranta. 11:pm bayan hilwah tayi wanka ta canza kaya zuwa na bacci sabbi dal dasu riga da wando masu laushn tsiya amihh tama hilwah adduarh ta lullubeta da duvet a dakin salwah dan ta kula tafi so ta kwana nan din, ta mata seda safe ta fice a dakin ta nufa nata dakin , domin samun dmr yin tunanin abinda ke ranta... Salwah dake toilet tayi wanka ta futo taga Hilwah kwance a kn bed amihh ta fita, hkn ya bata tabbacin ta tafi nata dakin ne seda safe kuma. Kure hilwah tayi da ido taga har zuwa lokacin idonta biyu ta kurewa gefe guda ido dagani tunanin wani abu takeyi, kuma hkn ne tana tunanin kayan mayen data saba sha ne, yau kuma babu, musammanma cocaine tafi sabawa da shanta. Shiryawa salwah tayi cikin kayan bacci ta feshe jikinta da Indians perfume nan ta hau aikin zuba kamshi. hilwah uwar yan son kamshi hadda lumshe ido ta rinkayi tana shaqar kamshin. Salwah ta hauro kn bed din ta zauna ta lankwashe kafa, hilwah ta waigo ta zubawa mata idanuwa suka sakarwa juna murmushi. "Kin dawo gidan mu kenan har abadan kou me rabin suna?'' Salwah ta jefowa hilwah tambayar. Murmushi kawai hilwah ta sakarwa salwah...salwah taci gaba da jan Hilwah da surutu har zuwa 12:30am , mikewa hilwah tayi ta fada bathroom idanuwanta a soye babu alamar bacci ta dauro alwala ta fito, Salwah nata binta da ido, ta nufa inda aka tanada dan gabatar da sallah, ta tayar da sallarh nafilah, salwah de nata binta da ido, duk raka'ah biyu inta kai seta dakata tayi karatun alqur'ani me girma. daga izifi goma ta fara zuwa kasa, cikin zazzakar muryarta me fidda fitinannan sauti. Salwah ta mike itama tayo alwala tazo tabi sahunta suka cigaba da nafilfilin.... Har zuwa wannan lokacin idanuwanta biyu bata samu ta rintsa ba se aikin zagaye takeyi tana safa da marwa a dakin nata, wasu irin tunani daban daban sunata bijiro mata a kn hilwah tabbas tanaso ta mata abnda bazata taba barin gidannan ba, ballan tana tayi tunanin komawa gidan ruwah. "Wani abu ne wannan?'' Wani bangare na zuciar hajiya maryam ta jefo mata wannan tambayar...dayan bngren zuciar na qoqarin bata amsa ta fara jiyo karatun alqur'ani me girma kasa kasa, fitowa tayi falo, tana me lumsar ido saboda dadin karatun al'qur'anin data rasa a ina take jiyosa....Tazo zata gifta dakin Salwah ta kara jiyo karatun na kusantarta, manna kunnanta tayi a jikin kofar dakin, tana jiyo daddadar muryar hilwah na karatu alqurani amma ta gaza gano ko wacece, tadesan ba muryar Salwah bace, bata tsammaci hilwah ta iya kira'arh sudais har haka ba,,sak kira'arta sak ta malam sudais. Turo handle din dakin tayi ta shigo idanuwanta suka sauka kn hilwah daketa karatun al'qur'anin se salwah daketa faman jero nafilfili. Hilwah ta dago kwayar idonta sanadiyar turo kofar dakin da akayi aka shifo tasata dago kwayar idon nata, Nan taga Amihh tayi shiru hadi da sauke kwayar idonta kasa sbda amihh daketa kallonta,,,juyawa hajiya maryam tayi ta fice a dakin ta nufa dakinta zuciarta ta kara yin full da soyayya da kaunar hilwah, tare da fatan kasancewa da ita har abadan da'iman. "To ta yaya?" Zuciarta ta tambayeta, bata tsaya bata lokacin bata amsa ba ta fada toilet ta dauro alwala ta fito ta zumbula hijjabi ta hau jero nafilfili tana me rokon Allah yasa tasamu mafita me salama a zuciarta a kn yadda hilwah zata kasance dasu har abadan...seda tayi sallarh asubahi gari yadan fara wayewa kana ta kwanta zuciarta wasai kmr ta sabon jariri yayin da tin tana nafilfili ta yankewa knta abinda ya dace da ita a kn hilwah. A bangaren su hilwah ma seda sukayi sallarh asubahi kana suka koma suka kwanta bacci, hilwah baccinta me cike da tsantsar mafarkan wannan guy din tayi, wai gata gashi suna kallon juna amma babu wanda ya tanka juna, se kallon tsana kawai guy din ke Aiko mata.... Yau ta kasance friday ce. 9:am Amihh ta tashi ta fada bathroom tayi wanka a daddafe ta fito ta shirya cikin abaya Cotton color ta yane knta da mayafin abayar ta karasa ta dauki kudi kimanin dubu dari hudu a drower din da take ajiye kudade. Ta saka 400k din a cikin bag dinta dmn already akwai 150k a ciki, ta xira plat shoe dinta na manyan mata ta dauki mukullin motarta ta fice a dakin, ta fito falo bataga kowa ba, sede ko ina tsaf tsaf yake, ta isa kofar dakin Salwah ta gnshi a rufe dagani basu tashi a bacci ba, sbda basu kwanta da wuri ba. Da fara'arh a kn fuskarta ta fice a falon, compound ta fito dai-dai watch din zallar gold dake hannunya ya nuna 10:13am. kukan tsintsaye iri daban daban se tashi yakeyi a compound din yayinda bishoyoyin dake gidan da flowers masu koren ganye se kadasu iska keyi a hnkli a hnkli. Dan ustaz dake zaune bakin get shida me gadi yaga fitowar hajiya maryam a guje ya taso se uban sheki yakeyi yayi wankan safe ya lafta uban mai kannan nashi tal-tal ya karaso inda hajiya maryam ke kokarin karasawa packing space yace "khaifak asbahtah yah hajjaju?'' Hajiya Maryam ta dago kwayar idonta ta zubawa dan ustaz tin daga kasan kafafuwanshi ta fara kallonshi inda yake sanye da green din slifas dan madina kafarnan tashi se sheki takeyi ya shafa mai sosai hatta da slifas dinma kullum in yy wanka seya shafa masa mai, kafarnan baki kirin, gashi an lafta mata mai seta kara bakikirin da ita. Hajiya maryam ta dawo ta kalli rigar jallabiyar dake jikinsa wadda da kadan ta wuce guiwa ta dawo da idonta kan fuskarshi se uban shinning takeyi, kusan mai kwalba daya yake shafewa a kwana biyu kuma me gurguwa yake shafawa, be murzawa sosai dukse fuskar tasa tayi yellow yellow gemunsa kuwa ya mayar dashi brown color, se murmushi yakewa hajiya Maryam, ita ko tasha kuka zeyi. "Meya faru zakayi kuka kuma? Mutuwa aka maka?'' Hajiya maryam ta tambayi dan Ustaz yynda dariya ke shirin subuce mata, Sbda shigar ta dan ustaz da ynyin siffarsa. Kara washe baki dan ustaz yayi yace "lah! Lah! Ana latagadab! Wato ainifin ni bana fushi hajiya, wato ainifin ma'aiki s.a.w ya mana natsiha da mu yawaita murmushi, to Murmushi nakeyi hajiya..." Ya karashe mgnr yana jawo gemun shi nan da nan kuwa hannunshi ya dauke da maikon dake gemun nasa. Hajiya maryam ta girgiza kai ashe Murmushi yakeyi ita wlhy tasha kuka ma yakeyi ko yake shirin yi. "ALLAH ya KYAUTAR..." Hajiyar maryam ta fadi hadi da juyawa ta nufa packing space dan ustaz ya biyota yana fadin "Wato ainifin Hajiya nace anguwa zakije ne? Ainifin ni zan jaki ko zaki tafi da kanki ne?" "Da kaina zanja kaina..." A takaice Hajiya maryam ta bawa dan ustaz amsa. Watsa hannu dan ustaz yayi ya dawo baya yana fadin "latagadab! Wato ainifin nace kada kiyi fishi hajjaju mutanen makka, ALLAH ya tsare hnya,...wato ainifin nace ko shagon saida kayan metahh yauma zaki je?" ya karashe mgnr Da tambayar Hajiya
Chapter 67 · 0% Book details