← Book details Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 225

Sashe 48

Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Alhasan ya kira Alhaji samah, shine shugaba a asibitin da Amihh ke Aiki, ya mika masa bukatunsa na son yama Hajiya maryam trnsper ta dawo kd da aiki, alhaji samah yaso ya tubure sbda basu son rasa maryam a asibitin nasu, Amma alhasan ya cika shi da magiya beda yadda zeyi yace ba damuwa domin kuwa yana ganin mutumcin alhasan sosai shima yana darajasa ainun. A ranar Alhaji sama ya rubutowa hajiya maryam trnsper daga asibitin kd zuwa asibitin nosing home dake kaduna. Hajiya maryamna zaune a office dinta da system dinta a gabanta tana wasu yan tabe tabe, shugaban asibitin ya aiko kiranta, mikewa tayi ta je dan amsa kira. Ta nufa office dinsa, ta nemi izinin shigowa akayi mata ta shigo ta gaidasa ya amsa zucia cike da jin ddh, ba karamin kaunarta yakeyi ba, suna jin dadin aikinta sosai tanada karatu me zurfi wanda babu algush, sam beso yi mata trnsper ba dande beda yadda zeyi ne. Kujerar dake facing dinsa ya nuna mata ta zauna ya miko mata wata yar takadda tasa hannu ta amsa cikin ladabi , ta bude ta karantata ba bata lokaci, bayan ta gama karantar takaddar ta dago kwayar idonta ta zubawa alhaji samah ido, tana me neman karin bayani. Cikin harshen turanci ta fara magana ''sir naga knr trnsper ne ko? Zuwa kd? Kmr hkn ne" Alhaji samah shima ya mayar mata da harshen nasarah "Yeah trnsper ne kika samu zuwa kd tare da babban matsayin dayafi wannan da kk a wannan asibitin..." Hajiya maryam tayi jim kwayar idonta na kan Alhaji samah taci gaba da mgna da harshen turanci ''Sir babu ta yadda za a hanya wannan trnsper din plx...sbda bana da bukata...kuma ma Ai na kusa ajiye Aiki...." Alhaji samah ya amshe da "dukda hk dr...Ai su sunada bukatarki dr, aikin ceton rai kkeyi, Allah kadai yasan irin ladar dake takaddarki a lahira, kiyi hkri plx..." Ya karashe mgnr yana dawo da hnklinsa kn system din dake gabansa hajiya maryam ta masa godia badan rai yasoba ta fice a office din da takaddar trnsper din ga hannunta, direct office dinta ta nufa zucia babu dadih ta suri bag dinta da car key dinta ta fice a office din, farfajiyar kayataccen asibitin ta fito, ta shiga motarta ta fice zucia babu dadih, ta fara tunanin anya ba Alhaji Murtala bane yasa aka mata trnsper dinnan zuwa kd sbda taki amincewa da hkn, shine ya biyo mata ta bayan gida. "Amma ko dabe kyautaminba..." Ta fadi a bayyane yayin da take komarin Karya kan motarta zuwa gidan juwairiyya. Da takaddar a hannunta ta shigo falon Hajiya Juwairriyya zucia babu dadih. Hajiya dake zaune kan kujerar 2ct ta dago kwayar idonta ta zubawa hajiya maryam kallo daya ta mata ta gane bata cikin walwala. Ba tare da hajiya maryam tace komi ba ta ajiyewa hajiya Juwairriyya takaddar dake hannunta a kn jikinta ta nemi kujerar dake facing Juwairriyya ta zauna. Hajiya Juwairriyya ta shiga aikin warwarar takaddar ta budeta tas kana ta karantata trnsper tagani daga kano to kaduna. Ita knta tayi mamaki duk yadda asibitin kno ke ji ita amma suka turata kd lallai akwai laushe cikin nadi. "Trnsper nagani Hajiya?" Cewar hajiya Juwairriyya tyi mgnr fuskarta dauke da neman karin bayani. Hajiya maryam ta d'aga mata kai kana tace "yadda kk ganta haka nima na gnta kwatsam, yadda kksan saukar araduh ..." Hajiya Juwairriyya ta sauke ajiyar zucia hadi da rafka uban tagumi hannu biyu biyu kana tace ''to ynzu yaza ayi ne?'' Maryam ta watsa hannu hadi da cewa ''bnsani ba hajiya...amma ni ina tunanin na hakura da Aikinnan kawai danni gaskia bnda ra'ayin komawa kd..." Hajiya Juwairriyya dake cike da mamaki har lokacin tace "ikon Allah kenan, Hajiya daza kibi ta tawa dakin koma kd kawai , bata yuwwa fa ki ajiye aikinki nan asibitinki ai akwai doctors kwararru, meze hana kawai ki koma kd plx maybe Alheri ne ke kira ...." Hajiya maryam tayi kasak'e tana sauraron hajiya Juwairriyya tace "Alheri ta ina hajia? Nifa na fara tunanin alhaji babba ne yasa akamin trnsper dinnan...." Hajiya Juwairriyya tace "in kuma bashi bane knga kin dauki alhakinsa ,,kawai ki barwa Allah lamarin Allah ya zaba mna abnda yafi alheri in alherine Allah ya tabbatar mana...."hajiya maryam ta amsa da Ameen kawai, sam batajin zuciarta ta aminta da tafiyarta kd. Nan hajiya Juwairriyya tayita bata shawarwari tace taje taci gaba da adduarh itama zata tayata in alherine komawarta kd ALLAH ya tabbatar, inde zatayi ta adduarh to insha ALLAH zataji hnklinta ya kwanta. Sosai hajiya maryam kejin ddn shawarwarin hajiya Juwairriyya sbda tanada zurfin ilmin addini sam bata bata gurbatacciyar shawara suna tare da junansu ne da zucia daya. Da addu'ur'i a ranta ta bar gidan ta nufa gidanta , rnr kwana tayi kiyamun laili tana rokon Allah zabi na gari. A washe garin rnr data tashi taji zuciarta ta kwanta mata da zuwanta kd haka kawaima taji kaf hnklinta ya koma garin kaduna, kai kace asiri aka mata. 2:pm byn ta idar da sallar azahar ta lalubo wayarta ta kira Alhaji murtala ta sanar dashi zuwa next week zata dawo kd sbda an mata trnsper daga gun Aiki, ba karamin ddh Alhaji babba yaji ba, yace za a nema mata gidan zama, ta masa godiya Sosai kana ta katse wayar, ta kira Juwairriyya ta sanar da kta zata fara shirye shiryen komawa kd, Hajiya Juwairriyya tayi mamakin saukowar tata a lokaci kankani, lallai babu abnda yafi karfin Allah fatan alheri Juwairriyya ta mata dukda kuwa zuciarta na cike da kewar aminiyarta abokiyar shawararta ta tabbatr wata kewarma se in ta bar garin.
Chapter 48 · 0% Book details