← Book details Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 223 OF 225

Sashe 223

Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Shekaru suka shude king yana gwadawa rukayya care da love amma sede beson addini ta hkn data fahimta yasata yin addininta a boye ta kasance macece ne tsananin ibada da addini. Har suka shekara gama king besan rukayya nayin addininta ba shide sam beda addini akasin ni Abraham da nake addinin Christian, shekarunsu goma sha biyu da aure a ganin king rukayya ta samu ciki a nan ta kara ganin tattali da so ga King , a haka har ta haifo diyya mace king yasa mata suna princess Bata da suna se princess, ni ne ke kiranta da gift, mahaifiyyarta kuma na kiranta da HILWAH sbda tanada tsananin kyaunta na fitar hankalin me lissafi. Hilwah ta tashi cikin gata a hannun me renonta wadda take itama baturia ce. Mahaifiyyar hilwah ta ginata a kn addininta mahaifinta sam besan da hkn ba sbda shi ya ginata ne a kn nasa addinin sannan besan cewa bama rukayya tana addininta ba har yanzu. Hilwah ta daga cikin gata ta samu ilmi me zurfi a fannin boko, a boye kuma ta samu krtun alqur’ani me girma da litattafai a gun mahaifiyarta, tana 12yrs tayi sukar alqur’ani me girma a boye, tana 15yrs tasan komi dake gudana na addinin musulunci. Wasu Lokutan rukayya takanyi kuka sbda tasan zaman zina sukeyi ita da king ba zaman aure ba amma ita jarabawarta kenan ta gaza cire sonshi a rayuwarta komi yayi bata ganin lefinta. Hilwah nada 15yrs mahaifinta ya Kamu da sonta sede Allah ya cire masa sha’awarta shide kawai yana sonta ne ya aureta Koda ma ne kusanceta ba sbda bayajin sha’awarki mace in ba sha,awar rukayya ba wadda kanki nadamar kasancewar su tare amma sede bata da yadda zatayi a kn sonshi, king ya fiddo da maitarsa na son kasancewa da hilwah wato itama ya aureta hilwah ta bijire sbda a koyarwar mahaifiyarta bata nuna mata hkn ya halatta ga addininta ba, a ranar ta nuna masa ita musulma ce, ya cika da mamakin hkn shine zunubi mfi girma daya fara bata masa rai a rywarsa ya tilastawa hilwah barin addininta ta bijire, kuma taki aminta da aurenta dayace zeyi, king yace ta zaba ko dolar datake ciki ko kuma ta ajiye masa komi ta bar masa gidansa ya hkra da ita har abadan� cikin zafi yayi mgnr. Nan take hilwah ta yadda da barinta gidan da a kn ta bar addininta. Mahaifiyarta ta Nemi ya yafewa hilwah amma yaki koda sauraronta sema ya rufeta da fada sbda itace silar komi. Hilwah ta bar gidansa daga ita se kyn dake jikinta,, ni bana nan seda na dawo na samu lbrin komi daga bakin rukayya, wadda ta maidani kmr babban abikinta, na bata hkri na bata baki , amma Ina kullum cikin kunci yake da bakin cikin rywa sbda rashin yarta tilo daya a dunia shi knsa king yana cikin kuncin sede be bayyanar da nasa. Nayiwa rukayya alqawarin nemoki Amma ta ko ina na duba kuma nasa an bincika bamu sameki ba.

A bangaren hilwah tinda ta bar gidan iyayenta daga ita se kana nan kayn dake jikinta wadanda ta saba dasu, maza yan iska nata kawo mata hari amma ta tsare knta Allah ma ya tsareta, har a titi ta kwana amma bata su da mutumcinta ba,, kwanta uku a hnya tafia kawai takeyi daga ita se kyn jikinta, da picture din mahaifiyyarta wanda ke aljihun wandon dake jikinta. A hk har Allah ya hadata da wani kawalin mata Wanda yasan hjya magajia shine ya hada hilwah da magajiyar karuwaii, tasa yama hilwah visa ya kawota nigeria gidan karuwai nan ne matsugunninta na farko kuma na karshe ta hadu da amal da Khamilah da Kankana kawar amana. Zuwanta gidan krwai ya zamar ma magajia jari dukda bata taba bada knta ba ga d’ana miji, ta hadu da Alhaji sunusi ya dauki dawainiyarta ta komi dukda be taba saninta ba a matsayin diyya mace.

A bangaren mahaifiyyar hilwah kam ta rayu a kuncin rashin diyyarta a haka wata rana aka wayi gari gidansu ya Kama da wuta ba a tsira da kowa ba a gidan duksun kone kurmus ta mutu tana addininta na musulunci a boye amma ga zahiri tayiwa king alkawarin ta bar addininta tin baya daya gano taja yarsa ga musulunci ya mata horo me tsanani kana ya hanata ga addininta a zahiri amma harta mutu da addininta na musulunci, sede batasan makomarta ba ga ubangiji, na jimawar da tayi a aikata babban lefi na zina.
Chapter 223 · 0% Book details