← Book details Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 225

Sashe 58

Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ciki, tazo ta ganki, nan da kwana biyu hk se ki koma gida...." Cewar hajiya maryam da tayi mgnr cikin natsuwa. Hilwah dake sauraronta ta lumshe ido, a ranta tace nida bnda gidan iyaye me zance?'' Shiru tayi ba tare da tace komi ba. Hajiya maryam ta zuba mata ido tana nazartarta yayinda hannunta ke kan kafafuwanta. "Ko gidan naku da nisa ne?" Hajiya maryam ta kara tambaya idonta na kn hilwah. A wannan karom Hilwah karayin shiru tayi, salwah ta zuba ma hilwah ido, hk hajiya maryam ma idon ta zuba mata, mamaki ya rufeta ta fara tunanin ko de basu da gida ne, ko bata da iyaye ne, to in bata da iyaye a gun wa take zaune?'' Ta tambayi knta, ta bawa knta amsa da oho. "Iyayenki zasu damu da rashin ganinki , gashi ba waya a hannunki balle a kirasu a sanar dasu?" Cewar hajiya maryam data gaza hkri hk kawai ta tsinci knta dason tasan wacece yarinyar su waye iyayenta. "Wayana na motana..."_ cewar hilwah. Se ynzu hajiya maryam ta tuna data amshi car key da ATM card a hannunta sadda zasu sata a mota. Mikewa tayi tana fadin bari insa a dauko miki motar taki, ai riskine a barta a can..." Ta karashe mgnr tana ficewa a dakin, ta nufa compound nan ta samu dan ustaz a baranda a kan dadduma yanata nafilfili zuwa lokacin anyi sallarh isha'i shine daya dawo daga masallacin ya dasa da nafilfili, yayi sallama nema yana zaune se Aikin zubo addu'ur'i yakeyi, gidan fayau haske kamar rana. hajiya maryam ta karaso inda yake ta tsaya, yana ganinta ya shafa addu'arhsa ya mike tsaye yana fadin, "Hajjaju mutanen makka, wato nace Ainifin ya jikin ita me tarar aradu?'' Hajiya maryam ta hade rai ta kula shi besanma ba ason abu ba, kai kace ma zigashi akeyi. "Bana ce maka banason rashin kamun kai ba wai.." Cewar hajiya maryam da tayi mgnr babu alamar wasa a tattare da ita. Da hanzari dan ustaz ya kai hannayensa duka biyu ya dafe kansa wanda keta faman shining yace "latagadab!" Wato kada tayi fushi. Girgiza kai kawai hajiya maryam tayi, tace yaje cikin motar dasuka fita da ita dazu, zega atm card da key din motar. Dan ustaz yace toh ya juya a guje ya nufa packing space se waqar larabawa yakeyi.. hajiya maryam ta koma cikin gidan ba jimawa ta dawo hannunta riqe da yan dari biyar biyar sababbi guda goma, ta mikawa dan ustaz dake tsaye hannunshi riqe da Atm card din da mukullin motar, ya mikawa hajiya maryam ta amshi ATm din kawai, kana tace yaje ya dauko motar hilwah a sidi And song, ta bashi 5k din dake hannunta tace ya hau abin hawa, dan ustaz ya amshe yanata godia ya fice a gidan, se kara kirga 5k din yakeyi ya mnta yaushe rabonshi dayaga 5k a rayuwarshi. Juyowa hajiya maryam tayi ta dawo cikin gidan. Direct dakinta ta shigo nan ta samu salwah a zaune a gefen bed din, Hilwah kuma tana kan dadduma tanata jero sallarh la'asar da magrib da isha'i, seda ta watsa ruwan dumi salwah ta bata kaya ta canza kana tayi sallah. hajiya maryam ta zuba mata ido, kana ta juya ta fice a dakin ta nufa kicking dan kara sama mata abinda zata karaci kafin tasha mgninta na dare. Ita sam bata tunanin knta dukda kuwa tanajin yunwa. Jlp din Cuscus ta hada mata irin na larabawa wanda rabinshi duk ganyayyaki ne, a ranta se kokwanto takeyi anya ma hilwab zata iya cin cuscus din.... Dawowa dakin tayi hannunta riqe da trea a tsaye ta samu hilwah salwah ma na tsayen,... "Amihh wai hilwah zata tafi gida...." Salwah ta tareta da mgnr, hajiya maryam ta karaso cikin hanzari tana fadin "gida kuma? Wani irin gida!? Haba yatah.. Koma ki zauna plx..." Ta karashe mgnr kwayar idonta na kn hilwah, wadda ta tsaya ita wai so takeyi ta tafi gida, komawa tayi ta zauna gefen bed din har zuwa ynzu jiri take gani. Hajiya maryam ta ajiye trea din dake hannunta a kasan dakin, ta zauna gefen bed din kusa da ita cikin sanyin murya ta fara mgna "Yarinyata gida zakije,? Why plx? baki gama warkewa ba fa, ta yaya zakije gida, ki bani address din gidanku knji se inje in snr dasu halin da kk ciki ... amma ke bazan iya barinki ki tafi gida ba gaskia, se an kwana biyu naga yanayin jikin naki..." Hilwah tayi shiru kunnuwanta na sauraron daddad'an kalaman hajiya maryam. "Kin hakura zuwa gobe kou?'' Hajiya maryam tayi mgnr da sigar rarrashi, hilwah ta daga mata kai kawai. Murmushi hajiya maryam tayi, tana kokarin zuba Cuscus din a plt dan Ustaz ya hau doko sallahma a falon , hajiya maryam tace salwah taje, ba bata lokaci salwah ta mike ta fice a dakin... Hajiya maryam taci gaba da zuwa cuscus din a plt din, hilwah ta zubawa cuscus din ido, irin wanda mahaifiyarta ke dafa mata, tana sonshi sosai, dan haka duk ta kagu ta fara ci. Ba bata lokaci hajiya maryam ta fara feeding hilwah,..abinda ya bata mamaki shine ganin yadda hilwah Kecin cuscus din cike da kwarewa kai dagani kasan ba yau ta fara ciba, tabbas akwai tambayoyi cike da zuciar hajiya maryam amma ba damar yi sbda batason ta takura mata ganin halin da take ciki. Salwah ce ta dawo dakin ta bawa Amihh car key din Hilwah da dan ustaz ya bata tana fadin "gashi inji dan ustaz wai ya dauko motar ..'' Hajiya maryam tasa hannu ta amsa tace okay, ta ajiye drower din bedside. Ta ci gaba da bawa hilwah cuscus din. Salwah ta zauna gefen gadon itama, ta zubawa mahaifiyarta ido Mamaki fal ranta na yadda amihh keta tarairayar hilwah,... Amihh ta gama bata cuscus din ta bata magungunan dare ta sha, ta mike ta nufa bathroom ta hada mata ruwan dumi tace tayi wanka, ba musu hilwah ta shiga bathroom din tayi wankan ta fito kirjinta daure da bathrobe, Amihh da salwah suka zubo mata ido, tabbas ALLAH yayi halitta. Kallo daya biyu Hajiya maryam tama hilwah ta dauke kwayar idonta a knta tana me wani irin tunani a ranta, tabbas tanason wannan irin na hilwah. Hajiya maryam ta temaka mata ta shirya cikin kayan bacci sabbi kalar purple riga da wando ne, masu kyau da laushi. Hilwah taga tarairaya sosai se bin Hajiya maryam takeyi da ido, tana jinta a rnta kmr mahaifiyarta kwantawa hilwah tayi tanajin jikinta ya mata dadih sosai sbda wankan da tayi Amihh se sannu taketa jero mata....dan Ustaz ne ya kara sallahma da karfi a tsakiyar falon, salwah ta tashi ta fice a dakin ta nufa falon, Dan ustaz ta gani a tsakiyar falon hannunshi riqe da hand bag din Amihh da phone dinta. "Sannu hajiya karama,..wato ainifin hajiya karama kar de kiga kamar na dameki ne... Ga wannan jakar ta hajiya ce mutanen makka da wayarta se kira akeyi,..." Salwah tasa hannu ta amsa, haka kawai ta tsinci knta dason tambayar dan ustaz meya faru dazu. Tana tambayarsa kuwa kmr yana jira ya kwashe lbrin komi ya sanar da salwah shiru tayi, tayi jim tana me karajin soyayyar hilwah a rantan lallai dole Amihh tayita nan nan da ita ashe ta ceci rayuwarta ne. Salwah ta koma dakin zucia fal kaunar Hilwah. Ta samu Amihh na lullubeta da duvet tana mata adduarh, nanma seda kn salwah ya kara daurewa. Karasawa tayi ta mikawa Amihh bag din da phone dinta data kara daukar wani sabon ringing din. Seda ta gama ma hilwah adduarh kana ta dago ta amshi wayar da bag din zuciarta cike da mamaki, ita fa tama mnta dasu tadesan dasuka fadi da hilwah duka abubuwan dake hannunta seda suka zube, tashama tayi missn dinsu har abadan., kila shine dan ustaz ya gani ya dauko mata. Duba screen din wayar tayi yayinda kiran ma tini ya jima da katsewa nan ta budeta a luck taga number din hajiya Juwairriyya ne. Kallon salwah dake tsaye tayi tace "ki kwana da ita..." Salwah tace toh amihh ta juyo ta kalli hilwah kana ta fice a dakin, tana dealing number din hajiya juwairiyya. Hilwah tabi bayan Amihh da ido taso ace su kwana tare, salwah ta shige bathroom danyin wanka ta fito kirjinta daure da bathrobe Ta kai idanuwanta ga hilwah, wadda zuwa lokacin baccima ya dauketa cikin magungunan da Amihh ta bata akwai mesa baccu. Ficewa salwah tayi a dakin ta nufa bed room dinta ta shirya cikin kayan bacci kana ta fito ta nufa kiching dan samawa knta abinda zataci.
Chapter 58 · 0% Book details